WATAN RABI'UL AWWAL

 

"Daga cikin abubuwan mamakin rayuwar Manzon Allah (s) shi ne cewa duk tsawon wadannan shekaru goma (da yayi a Madina) babu wani lokaci da ya tafi haka kawai a banza, ba a taba gani ba cewa Annabi (s) ya yi kasa a guiwa wajen bayyanar da haske, shiryar da mutane, koyarwa da kuma tarbiyya ba. A hakikanin gaskiya, farkawarsa, barcinsa, zama a masallacinsa, a gidansa, a fili daga, mu'amala da iyalansa, da dai sauranus, duk akwai darussa a cikinsu".

(Ayatullah al-Uzma Khamene'i)
Yayin da yake bayani kan rayuwar
Annabi (s) a birnin Madina
Adadi
Kwana Wata
Abin Da Ya Faru a Ranar
Shekara
1
1
Hijirar Manzon Allah (s) daga Makka zuwa Madina (farkon kirgen kalandar Musulunci.
---
2
3
Harin da Hussain bn Numair ya kai garin Makka don kame Abdullahi bn Zubair, a bisa umurnin Yazid bn Mu'awiyyah, da kuma sanya wa dakin Ka'aba wuta.
64 B.H
3
4
Fitar Manzon Allah (s) daga kogon Thawru bayan kwanaki uku zuwa birnin Madina.
---
3
5
Wafatin Sukaina, 'yar Imam Husaini (a.s).
117 B.H
4
8

Shahadar Imam Hasan al-Askari (a.s), Imamin Shi'a na goma sha daya.
260 B.H
5
8
Farkon Imamancin Imamul Mahdi (a.s), Imamin Shi'a na sha biyu.
260 B.H
6
10
Wafatin Abdulmutallib, kakan Annabi (s).
---
7
10
Auren Manzon Allah (s) da Nana Khadija (a.s).
15 K.H
8
12
Isowar Manzon Allah (s) birnin Madina.
1 B.H
9
14
Mutuwar Yazid dan Mu'awiyya (la'anar Allah ta tabbata a gare shi).
64 B.H
10
17
Ranar Maulidin Manzon Allah (s.a.w.s).
53 K.H
11
17
Haihuwar Imam Sadik (a.s), Imamin Shi'a na shida.
83 B.H
12
22
Ranar da Manzon Allah (s) ya ba wa 'yarsa Nana Fatima (a.s) kyautar Fadak.
4 B.H
13
26
Sulhun Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) da Muawiyya dan Abu Sufyan.
41 B.H