“To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a
bayan abin da ya zo kama daga ilmi, to ka ce: “Ku zo mu kirayi
‘ya’yanmu da ‘ya’yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa’an nan kuma
mu kankantar da kai, sa’an nan kuma mu sanya la’anar Allah a kan makaryata”. (Suratu Al-Imrana 3:61)
Kusan karshe-karshen rayuwar Ma’aiki
(s.a.w.a), sakamakon irin nasarar da Musulunci ya samu kuma yake ci gaba da
samu, da dama daga dauloli da kasashen da suke kewaye da daular Musulunci sun
nufo Madina don mika wuya da amsa kiran Manzo (Musulunci), sai dai duk da haka
wasu daga cikin kasashe da kabilun ba su musulunta ba don haka Ma’aiki
(s.a.w.a) ya aike musu da wasikun gayyata zuwa Musulunci. Daga cikin al’ummar
da Ma’aikin (s.a.w.a) ya aike musu da irin wannan goron gayyata har da
kiristocin Najran (da ke kasar Yemen). A cikin wannan wasika da Manzon Allah
(s.a.w.a) ya aike wa babban fadan Najran wato Abu Haris bn Alkama yana cewa:
"…..bayan haka, ina kiranku zuwa ga
bautan Allah maimakon bautan bayinSa, ina kiranku zuwa ga mika kai ga Allah
maimakon mika kai ga bayi, idan ba ku karbi wannan kira nawa ba, to ku amince
da bayar da jizyah ga gwamnatin Musulunci in kuwa ba haka ba to ku shirya wa yaki.
Wassalam.”.
Lokacin da wasikar Ma’aiki (s.a.w.a) ta
shiga hannun mutanen Najran din sai manyansu suka taru don tattaunawa kan wasikar da kuma aiwatar da abin da ya
dace. Bayan tattaunawa, da kuma bayanin da wasu suka yi na cewa lalle Allah Ya
yi alkawari wa Annabi Ibrahim cewa zai tayar da wani annabi cikin zuriyar dansa
Isma’il, don haka yana da kyau a tura tawaga wacce za ta tafi wajen Ma’aiki
(s.a.w.a) don tattaunawa da shi da kuma dubi cikin lamurransa da kuma
yanayinsa. Don haka aka shirya tawaga karkashin jagorancin babban malamin
kiristan garin da sauran manyan malamai da za su tafi Madina don ganawa da
Ma’aiki (s.a.w.a).
Lokacin da wannan tawaga ta iso Madina,
sai suka canza tufafin da ke jikinsu suka sanya tufafi na alfahari na hariri da
zobbunan zinare da giciye a wuyayensu suka nufi masallacin Ma’aiki don ganawa
da shi. Ko da suka iso wajen Ma’aiki sai ya juya musu baya, ya ki saurarensu.
Ganin haka sai suka fita suka nufi wajen wasu sahabbai suna neman shawararsu
kan me ya kamata su yi ganin Manzo ya ki
saurarensu. Wadannan sahabbai dai ba su san me ye abin yi ba, sai da suka zo
wajen Imam Ali (a.s) (wata ruwayar kuma ta ce su kansu wadannan sahabbai ne
suka tambayi Ali kan mene ne ya kamata su yi) inda shi ne ya ce musu su cire wadannan
tufafi da suka sa su sanya tufafinsu na malamai su tafi wajen Ma’aikin zai
saurare su. Bayan da suka yi hakan kuwa, sai Ma’aiki (s.a.w.a) ya tarbe su da
yin maraba da su yana mai cewa: “Na rantse da Sarkin da Ya aiko ni a
matsayin ManzonSa, lokacin da suka zo na farko, na gansu ne tare da Shaidan”.
Bayan gabatar musu da addinin Musulunci,
kiristocin sun tambaye cewa: ‘Me za ka ce kan Isa dan Maryam?’ sai ya ce musu:
“Shi bawan Allah ne kuma ManzonSa”.
Su kuma kiristocin suka ce a'a shi kaza
da kaza ne (wato suka fadi akidarsu kan Annabi Isa (a.s) shi kuma Ma'aiki (s.a.w.a) yana amsa
musu da mahanga ta Musulunci, har aka saukar masa da ayar: "Lalle ne
misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adamu ne, (Allah) Ya halitta shi daga
turbaya, sa'an nan kuma Ya ce masa: "Ka kasance", sai ya
kasance". (Suratu Al-Imrana 3:59)
Bayan wasu tambayoyi da amsoshin da Manzo
(s.a.w.a) ya ba su, wadannan kiristoci sun ki amincewa su karbi Musulunci, duk
kuwa da tabbatattun hujjoji da Ma’aiki ya kafa musu.
Don haka sai Allah Madaukakin Sarki Ya
saukar da ayar mubahala da muka kawo a sama, wato:
“To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a
bayan abin da ya zo kama daga ilmi, to ka ce: “Ku zo mu kirayi
‘ya’yanmu da ‘ya’yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa’an nan kuma
mu kankantar da kai, sa’an nan kuma mu sanya la’anar Allah a kan makaryata”
Bayan saukar wannan aya Manzon Allah
(s.a.w.a) ya gabatar wa kiristocin da tayin yin mubahala (wato tsinuwa tsakanin
da neman Allah Ya la’anci makaryaci). Bayan tattaunawa tsakaninsu, kiristocin
sun amince da wannan tayi na Manzo, inda suka tsayar cewa a taru a rana ta gaba
don mubahalar. To amma sai babbansu Abu Haris ya ce musu ku sanya ido sosai
idan har Muhammadu ya fito mubahalar tare da 'ya'yayensa da Ahlulbaitinsa kada
ku yarda ku yi mubahalar, amma idan ya zo ne da sahabbansa da mabiyansa to ku
yarda ku yi mubahalar da shi.
Tun da sanyi safiyar ranar 24 ga watan
Zul Hajji, Manzon Allah (s.a.w.a) ya bukaci sahabbansa da su shirya wajen da za
a yi mubahalar a wajen gari inda shi da mutanen gidansa za a su zauna. Ko da
lokaci ya yi sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya fito tare da iyalan gidansa, wato
yana dauke da Imam Husain (a.s), yana rike
da hannun Imam Hasan (a.s) Nana Fatima
da Imam Ali (a.s) suna biye da shi,
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce musu: "Idan kun ji na yi addu'a ku ce min
amin". Koda ganin Ma'aiki da iyalan gidansa, sai babban kiristocin ya
tambaya cewa: su wane ne wadannan? Sai aka ce masa: wancan na bayan Muhamamdu dan
baffansa ne kuma mijin 'yarsa, wadancan yaran kuma 'ya'yan 'yarsa ne ita kuma
wancan 'yarsa ce, wacce tafi soyuwa a gare shi sama da kowa kuma abin kaunarsa.
Don haka sai wannan babban malamin kirista ya ce wa mabiyansa:
"Ya ku nasara (kiristoci)! Lalle ni
na ga wasu fuskoki da idan suka roki Allah da Ya kawar da wani dutse daga inda
ya ke, lalle zai kawar da shi da su, don haka kada ku yi mubahala da su sai ku
halaka, kuma babu wani kirista da zai saura a bayan kasa har zuwa tashin kiyama".
Don haka sai suka ce wa Manzon Allah
(s.a.w.a): "Ya Abal Kasim, lalle mu ba za mu yi mubahala da kai ba, mu
barka a kan addininka kai ma ka bar mu a
kan namu".
Sai ya ce musu: "To idan ba za ku
yi mubahala ba, to ku musulunta, sai ku sami duk abin da musulmi suke samu, da
kuma wani abin da ya hau kan musulmi"
Amma sai suka ki amincewa don haka sai
Ma'aiki (s.a.w.a) ya ce musu: "To ku shirya wa yaki". Sai suka
ce: Lalle ba mu da karfin yaki da larabawa, sai dai kawai mu yi sulhu
tsakaninmu cewa ba za ka yake mu ba, kuma ba za ka kawar da mu daga addininmu
ba, mu kuma kowace shekara za mu dinga ba ka kayayyakin ado dubu biyu: dubu
guda a Safar, dubu gudan kuma a Rajab da kuma garkuwa guda talatin na bakin karfe".
Don haka sai Ma'aiki (s.a.w.a) ya amince
ya yi sulhu da su yana mai cewa:
"Na rantse da wanda rai na ke
hannunSa, da mutanen Najran sun yi mubahala da mu, da an mayar da su birrai da
aladu, da an musu ruwan wuta, da kuma an halaka mutanen Najran da dukkan abin
da ke ciki hattta tsuntsayen da ke kan bishiyoyi".
Wannan dai shi ne labarin mubahala da
abin da ya faru wanda mabiya Ahlulbaiti
(a.s) suke nuna farin cikinsu da yin bukukuwa a duk lokacin da wannan
rana ta zagayo saboda abin da ta kumsa na nuna falalar Ahlulbaiti (Ashab
al-Kisa) a kan sauran sahabbai, kamar yadda Zamakshari cikin Tafsirinsa na
Al-Kashshaf yayin da yake magana kan wannan aya ta mubahala ya ke cewa: "Wannan
aya dalili ne mai karfin da ya wuce kowanne kan falala da fifikon As'hab
al-Kisa" (wato Muhammad, Ali, Fatima, Hasan da Husain - a.s-).
Wannan magana babu kokwanto cikinta don
kuwa hatta sahabban Ma'aikin sun fahimci haka shi ya sa ma wasu daga cikinsu
suka yi fatan da da su ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya fita don yin mubahalar.
A takaice dai wannan aya ta mubahala da
shi kansa abin da ya faru a wajen mubahala yana nuni da wasu muhimman al'amurra
da suka hada da: nuna irin matsayin da Imam Ali
(a.s) mai dakinsa Fatima al-Zahra da 'ya'yansa Hasan da Husain
wajen kare addinin Musulunci da tabbatar da gaskiyarsa da kuma rashin ingancin
sauran addinai. Kamar yadda ayar tana nuni da matsayin Amirul Muminina (a.s) da kuma halifancinsa bayan Ma'aiki da
kuma cewa babu wani da zai aiwatar da aikin Ma'aiki (s.a.w.a) a bayansa in ba
shi ba. Saboda idan aka duba ayar za a ga cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya zo ne
da Ali (a.s) a matsayin