|
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Abin da za mu yi batu a kai anan shi ne fahimtar Musulunci. Fahimta shi ne abin da wani yake nufi. Rashin fahimta yana nufin ba wa fahimtar wani ko ayyukansa mummunar ma'ana. Ba shakka, abin da ya kamata shi ne dukkan mutane su fahimci junansu, sannan kuma rashin fahimta yana faruwa ne daga rashin ilmin kishiya ko ajiye wasu ka'idoji a wurin da bai kamace su ba. A wasu lokuta, kwatanci fadi ko tsammani yana iya kawo shakku. Rashin fahimta, a kowane lokaci kuma ga kowane mutum ya kan haifar da hasara da takaici. Misali idan muka dauki mutane biyu suna hamayya da juna, wannan mai bautar Allah ne, dayan kuma mai son abin duniya, duk da haka zai zame musu mafi alheri idan suka samu wata irin fahimta a tsakaninsu wacce zata dimke su wuri guda. Saboda kar su kasance suna shakkar juna game da manufofinsu; wato saboda a samu zama lafiya a tsakani. To amma abin takaici game da Musulmi shi ne, bayan da cewa sun rarrabu zuwa kungiyoyi daban-daban a kan abubuwa da suka shafi imaninsu, suna fama har ila yau da rashin fahimta saboda abin da suke tsammani 'yan'uwansu na yi ko sun yi imani da shi. A da, da kuma yanzu, an samu, ana kuma ci gaba da samun masu makirci wadanda nufinsu da kokarinsu duk suna amfani da shi ne wajen yada masifu a tsakanin musulmi. Barazanar da irin wannan rashin fahimta mara hujja ke yi, ya fi ainihin banbancin akida hatsari. Ta fuskar imani, musulmi suna iya samun hadin kai, da zama 'yan'uwa saboda da Allah da suke bautawa daya ne - dukkan musulmi suna fadin, La ilaha illa Allah, (babu abin bautawa da gaskiya sai Allah). Kuma sun yi imani da Annabcin, Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa. Sun san cewar Alkur'ani Littafi ne mai tsarki sun kuma dauka cewa shi ne tsarin mulkin musulmi. Dukkansu suna azumi a watan Ramalana su kuma yi bukin salla (bayan watan)cikin annashuwa da girmama juna. Sannan kuma suna soyayya da biyayya ga dangin Annabi (s). Wadannan abubuwan da suka dace a kai, ya isa ya hada zukatansu wuri guda da haifar da 'yan'uwantaka irin ta musulunci a tsakaninsu. Amma, abin bakin ciki, har yanzu akwai wannan rashin fahimtar a tsakaninsu. Har yanzu akwai mummunar fahimta ga mazhabobi. Kuma wadannan abubuwa ba sa komai in banda ruguza dangantakar da ke tsakanin musulmi.
Ba muna so ne mu rushe duk mazhabobi saboda komawa ga ginshikan Musulunci ba. Saboda da farko dai wannan aiki ne da ya fi karfinmu, na biyu kuma ba ta hanyar rushe mazhabobi ne kawai za a iya samun hadin kan musulmi ba. Fannoni daban-daban na Musulunci ba za su hana 'yan'uwantakar musulunci ba, kuma fannonin da aka dace suna da yawa kuma karfafa ne wadanda kuma za su hada musulmi wuri guda. Ba kuma muna son mu ce duk banbancin da ke tsakanin musulmi saboda rashin fahimta ba ne, a'a, ba kowane banbanci ne rashin fahimta ke haifar da shi ba, saboda haka idan ana son a warwaresu ana iya yin hakan ta wasu hanyoyi. Nufinmu shi ne magance banbance-banbancen da ke tsakaninmu saboda rashin fahimtar juna. Muna son mazhabobi daban-daban na musulunci su fahimci junansu ainihin yadda suke, sannan su yi watsi da mugayen zace-zace game da 'yan'uwansu na sauran mazhabobi. Ayoyin Alkur'ani mai girma da kuma hadisan Ma'aiki (s) da kuma na Imamai (a.s) duk sun tafi akan kiran musulmi da su hada kansu waje guda da kuma kara tabbatar da hakan a tsakaninsu. (1). A cikin surar Ali Imrana, Allah na cewa: (2). Aya ta 105, a cikin wannan surar ta ci gaba da bayyana abin da ake nufi da hadin kan musulmi: Wato, kar ku kasance kamar sauran (mabiya wasu addinai) wadanda suka rarrabu zuwa kungiyoyi daban-daban bayan Allah Ya yi musu wahayi. Saboda wadannan mutane za su sadu da fushin Allah. Wannan aya ta nuna a fili cewa rarrabuwa game da addini zai kirkiro da wasu addinai. Saboda wadannan gardamomi sun fi sauran hatsari. Yana da muhimmancin gaske a san cewar a tsakanin wadannan ayoyi guda biyu (aya ta 103 da ta 105) akwai wata aya mai muhimmanci wacce take da alaka
da umarnin da ke cikinsu, ayar kuwa ita ce: Wata jama'a daga cikinku ta kasance tana kira ga ayyukan alheri, kuma suna hani ga mummuna ayyuka. Wadanda suke aikata wannan a tsakaninku, su ne wadanda za su kai ga nasara. Wannan ya kasance haka ne saboda Alkur'ani ya bayyana cewa ana samun hadin kai ne ta hanyar umurni ga ayyukan alheri da hani ga munana. Idan aka mance ko aka yi watsi da wannan fanni na musulunci, ba za a taba samun hadin kan Musulunci da hadin kai a tsakanin musulmi ba. Mu musulmi mu ne muke da wannan kira ta shiriya, kuma dole mu yi umurni da alheri da kuma hani ga mummunan ayyuka, amma saboda rashin sanin Musulunci da manufofinsa, sai ya kasance mun san 'yan kadan ne kawai daga zahiran dokokinsa wadanda ba su shafi ainihin tushen musuluncin ba. Duk lokacin da muka yi kira da shiryarwa, ba ma wuce 'yan abubuwan da suka shafi kwawawan halaye da ibada; alhali kuwa daga daga cikin manyan manufofin Musulunci na zahiri shi ne hadin kan musulumi. Farko, kuma babban nauyin da ke kan masu kira ga ayyukan alheri da hani ga munana shi ne, shiryar da jama'a da hada kan musulmi. Hakika kamar yadda muka ambata, addinin Musulunci ya mai da hankali ya kuma ba da muhimmanci kwarai da gaske game da hadin kai a tsakanin musulmi, kuma hadin kai a Musulunci shi ne mafi girma daga cikin manufofin Musulunci. Wadanda suke kira ga alheri kuma suna hani da mumanan ayyuka, aikinsu ne su ga cewa sun cimma wannan manufa ta duk hanyar da za su iya. Wata hanyar da za a bi saboda samun hadin kai shi ne ta rashin jayayya. Alkur'ani mai girma yana cewa: Wato ku daukaka addininku, ku rabu da jayayya. Duk wani aiki na Musulunci da kuke kiran mutane gare shi, zai kasance mai wuyar yi ne ga mushirikai. Wannan aya tana nuna mana cewa abokanen gabar Musulunci, abokanen gaba ne ga manufofinsa. Ko da yaushe suna so ne su kawo rashin jituwa a tsakanin musulmi, suna jin tsoron hadin kansu, ko da yaushe suna kara iza wutar sabani da rarrabuwa wadda yake kara hana hadin kan musulmi. Alkur'ani na cewa: Babu shakka rarrabuwa na kawo rauni, wannan aya tana gabatar da hadin kan musulmi da cewa shi ne asasin karfinsu da izzarsu da farin cikinsu.
Tana cewa idan kuka samu rashin jituwa a tsakaninku za ku rasa duk karfinku. Wasu rashin jituwar ana samunsu ne saboda rashin son abu, wasu kuwa suna da tushe ne a akida.
Wannan yana da hatsarin gaske, idan aka mika shi daga wannan zamani zuwa wani, zai kawo wasu tatttaunawa, jayayya, littattafai da rubuce-rubuce wadanda za su haifar
da banbancin akida. Lokaci na wucewa, ana kara samun baraka, kamar yadda Alkur'ani ke cewa: |