AYYUKAN KASASHEN YAMMACI....UMMUL ABA'ISIN DIN AYYUKAN TA'ADDANCI:

Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran-Iran

awwalubauchi@yahoo.com


Ya zuwa yanzu dai ta'addanci da kuma ayyukan ta'addanci suna daga cikin muhimman al'amurran da suka dauki hankula al'ummomi da kasashen duniya da nufin ganin bayansu, hakan kuwa tum bayan harin 11 ga watan Satumban 2001 da aka kai wa Amurka ne da kuma sauran ayyukan ta'addancin da suka dinga biyowa baya. Ko shakka babu kawo karshen ayyukan ta'addancin da suke yin sanadiyyar mutuwar mutanen da ba su ci ba su sha ba, abu ne da da dama daga cikin mutanen duniya suke son ganin bayansu don al'umma su sami daman zama lafiya da kwanciyar hankali. To sai dai kuma kokarin ganin bayan ayyukan ta'addanci ba tare da la'akari da dalilan da suke kawo su da kuma magance su ba lamari da da wuya zai iya haifar da najita, wato kawo karshen wannan babbar anoba. Ta'addanci dai, kamar sauran lamurran siyasa da zamantakewa, yana da asalin abin da ke kawo shi, sai dai babban abin bakin cikin shi ne cewa 'yan siyasa da gwamnatocin kasashen yammaci musamman ma Amurka ba sa ba da wani muhimmanci na azo a gani kan wadannan dalilai don magance su.

Cikin 'yan shekarun nan dai masana daban-daban sun ta fadin albarkacin bakunansu kan wannan anoba da kuma dalilan da suke kawo ta. Da dama dai suna ganin ayyukan kasashen yammaci da kuma yadda suke gudanar da siyasarsu a kasashe masu tasowa musamman ma dai a kasashen musulmi na daga cikin dalilan da suke haifar da kai hare-haren 'ta'addanci' akan manufofi da kuma al'ummomin kasashen yammancin. Masu wannan ra'ayi dai suna cewa ne idan aka duba za a cewa mutanen da a halin yanzu ake kiransu da " 'yan ta'adda" mafi yawansu sun fito ne daga kasashen da suka kasance karkashin mulkin mallakan kasashen yammaci ko kuma wadanda a halin yanzu suke fuskantar wahalhalu saboda siyasar kasashen yammacin. Cikin karnonin da suka wuce, 'yan mulkin mallakan kasashen yammaci sun maida al'ummomin wadannan kasashe masu tasowa tamkar bayinsu da kuma wulakantasu, baya ga sace dukiyoyinsu da suka yi da sanya su cikin mawuyacin hali da kunci, sannan kuma har ya zuwa yanzu suna ci gaba da hakan ta wasu sabbin hanyoyi na daban da suka kirkiro, ciki kuwa har da tsoma baki cikin al'amurransu na cikin gida da kuma kafa musu hukumomin da za su ci gaba da lamunce musu (kasashen yammaci) manufofinsu da dai sauransu. Irin wadannan abubuwa ne suke sanya su kuma wadannan mutane, don hushe haushinsu, suke daukan wannan mataki na kai hare-hare akan manufofin yammacin da kuma kashe al'ummomi, duk da cewa hakan shi ma dai kuskure ne mai girman gaske. A takaice dai wadannan ayyukan zalunci na kasashen yammaci su ne abin da ke haifar da wadannan ayyuka.

Wani abu kuma na daban, wanda shi ne ma yake da muhimmancin gaske, da ke haifar da irin wadannan hare-hare akan manufofin yammacin shi ne kokarin da kasashen yammacin suke yi na fada da Musulunci da kuma tilasta wa al'umman musulmi irin akidunsa da kuma bakaken siyasunsu da nufin mallake kasashen musulmin da al'ummominsu yadda suke so. Sanannen abu ne dai cewa al'umman musulmi da suke da kyawawan al'adu, akidu da kuma koyarwa irin ta Musulunci ko da wasa ba za su taba amincewa da irin al'adu da koyarwa ta yammaci ba da suka ginu akan watsi da addini, yada lalacewa da fasadi tsakanin al'umma musamman ma matasa da dai sauran nau'oi na muggan dabi'u da hatta da dama daga cikin al'ummomin yammacin hakan ya fara isansu. Cikin 'yan shekarun nan musamman ma bayan darewa karagar mulkin Amurka da 'yan mazan jiya masu ra'ayin akidar 'kiristancin sahyoniya' karkashin jagorancin George W. Bush suka yi, kasashen yammacin suka fitar da maitansu a fili wajen kokarin ganin bayan koyarwar Musulunci na hakika da kuma tilasta wa musulmi amincewa da akidunsu ta hanyar amfanin da kafafun watsa labaransu da kuma barazana ta siyasa, tattalin arziki da kuma soji. Tun dai daga darewar mulkin 'yan mazan jiyan, duniya ta ga yadda suka fada wa kasar Afghanistan, da sunan kawar da gwamnatin Taliban da kuma kawo karshen kungiyar Alka'ida (wadanda su da kansu suka kafa su da kuma daure musu gindi), sannan kuma a baya-bayan nan suka mamaye kasar Iraki duk dai da nufin baza sojojinsu a wannan yankin na Gabas ta Tsakiya da kuma tsakankanin kasashen musulmi. Irin wadannan abubuwa ne suka sanya wasu daga cikin musulmin, don mayar da martani da wannan danyen aiki na yammaci, suka dau makamai da kuma aikata ayyuka daban-daban na ta'addanci akan al'ummomin da ba su ci ba su sha ba na wadannan kasashe na yammaci. Duk da cewa dai yin hakan ba wai abu ne da ya dace ba, to amma wa ya janyo hakan? Masu iya magana dai sukan ce wai in an bi ta barawo a bi ta mabi sawu, wai idan bera da sata, to ai daddawa ma da wari. A bugunta na lokacin da ake bukukuwan tunawa da shekara biyu da faruwar harin 11 ga watan Satumba, jaridar Guardian da ake bugawa a birnin London, ta bayyana kasashen yammaci a matsayin ummul aba'isin din yaduwar ayyukan ta'addanci.

A kokarin da suke yi na cika barazanarsu ta siyasa, soji da kuma al'adun yammaci akan kasashen musulmi, ya sa a shekarun karshe-karshe na karni na ashirin aka gabatar da mahangar nan ta 'Fada Tsakanin Al'adu' ko kuma abin da ake kira a turance da 'Clash of Civilizations'. Tun a wancan lokacin da dama daga cikin masanan yammacin suke ganin lalle wannan mahanga za ta haifar da rikici tsakanin al'adu. Daga cikin irin wadannan masana kuwa har da sanannen masanin nan dan kasar Amurka Samuel Huntington wanda yake ganin lalle a bisa wannan mahanga za a samu rikici da sabanin tsakanin al'adun yammaci da sauran al'adu musamman ma dai al'adun Musulunci, don kuwa hakan kamar fada ne da musulmi. Har ila yau kuma da dama sun yi amanna da cewa Bush, shugaban Amurka na yanzu, shi ne wanda ya ke son gudanar da wannan dadaddiyar mahanga. Don haka ne masanan suke ganin cewa bisa la'akari da irin wannan yanayi na fada da al'adun Musulunci, samun irin wadannan kungiyoyi masu wuce gona da iri abu ne da ba za a iya nesanta faruwarsa ba.

Wani abin da kuma yake da kyau a fahimta shi ne cewa wasu daga cikin irin wadannan kungiyoyi na ta'addanci ko kuma 'yan ta'addan, kafin wannan lokaci, sun kasance ne karkashin kulawar irin wadannan kasashe ko kuma ma su suka kirkiro su. A matsayin misali, Usama bn Ladin da kungiyarsa ta Alka'ida (wanda shi ne a yau ake ganinsa a matsayin babban dan ta'addan duniya) sun kasance karkashin kulawa da goyon bayan Amurka lokacin da tsohuwar tarayyar Sobiyeti take mamaye da kasar Afghanistan. Sannan kungiyar Taliban (wacce ita ma tana daga cikin kungiyoyin da ake ganinsu a halin yanzu a matsayin ta ta'addanci) a shekarun baya (farko-farkon shekarun 1990) ta kasance ne tana samun goyon baya da daurin gindin Amurka, Saudiyya da kuma Pakistan, abin da ya sa ta samu kame mafi yawa daga cikin kasar Afghanistan. Hakan dai yana tabbatar mana da cewa ne jami'an fadar White House ta Amurka a shirye suke su yi aiki (ko kuma ma su kirkiro) da duk wata kungiya komai munin irin ayyukan da take yi matukar dai za ta kare musu manufofinsu. Don hakan ne ma jaridar The Guardian da ake bugawa a birnin London ta rubuta cewa: "Kasashen yammaci su da kansu suka karfafa abokan gabansu ta hanyar karfafa Bn Ladin da sauran mujahidan larabawa a lokacin yakin cacan baki bugu da kari kuma kan taimakawa kungiyar Taliban wanda hakan kuma yana nuni ne da irin siyasar son kai na kasashen yammaci".

Saboda da haka, muna iya cewa tushen ta'addanci da kuma yaduwarsa na cikin siyasar wariya da danniya ta kasashen yammaci ne, duk da cewa sun ki su fito fili su bayyana hakan da kuma daukan matakan da suka dace wajen ganin bayan hakan. Babban abin da ke nuni da hakan kuwa shi ne irin ayyukan kasar Amurka tun bayan harin 11 ga watan Satumban da aka kai wa kasar, inda ta zama kamar mahaukaciyar kare tana da kai hare-hare na siyasa, tattalin arziki da ma na soji akan kungiyoyi da kasashen da ta kira na ta'addanci alhali kuwa ita ta share musu fagen munanan ayyukan da suka kasance suna yi, sai dai kuma har ya zuwa yanzu ta gagara cimma wannan manufa da ta ce tana son cimmawa, wato kawar da tushen ta'addanci, duk kuwa da cewa dai ta samu nasarar kawar da kungiyar Taliban daga mulki da kuma tarwatsa 'yan kungiyar Alka'ida. Maimakon ma dai irin hare-haren da suka kai wa kasar Afghanistan ( da nufin kawar da Taliban da Alka'ida) da kuma wanda suka kai Iraki (da nufin kawar da Saddam Husseini) bugu da kari kan barazanar da suke yi wa sauran kasashe ya zamanto ya rage karuwar kiyayayya da kuma kai hare-hare ga manufofin Amurka a duk inda suke face ma dai hakan sai dada karuwa yake yi a kullum.

Da dama daga cikin masana dai sun yi amanna da cewa ayyukan kasashen yammaci musamman ma dai na jami'an fadar White House ya yi kama da ayyukan ta'addanci, kuma kamar yadda wadannan 'yan ta'adda suke zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba, haka su ma wadannan jami'ai suke zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba. Ko ba a fadi ba kuwa irin hakan shi ma ya jawo karuwar ayyukan ta'addanci a duk fadin duniya.

Har ila yau wani abin da ke kara kiyayyar yammaci cikin zukatan musulmi shi ne irin amfani da kalmomin batanci ga Musulunci, Manzon Allah (s.a.w.a) da sauran abubuwan girmamawa na addinin da wasu manyan jami'an kasashen yammacin suke yi ta hanyoyin kafafen watsa labaransu. Daga cikin mutanen da suka kaurin suna wajen irin wannan danyen aiki sun hada har da prime ministan kasar Italiya Berlusconi, Jerry Falwell, babban malamin kirista a fadar White House, Pat Robertson, mai ba wa shugaban kasar Amurka Bush shawara, Frankhin Graham, shi ma dai wani jami'i a Amurkan da dai sauransu wadanda suke maganganu na batanci akan addinin Musulunci. Ko ba a fadi ba irin wadannan abubuwa sukan tunzura al'umman musulmi da sanya su dauka hukumcin a hannayensu.

Baya ga hakan, wani babban abin da kuma ke janyo karuwar kai hare-hare kan manufofin yammaci din shi ne goyon baya ido rufe da kasashen yammacin suke bai wa haramtacciyar kasar Isra'ila da 'yan ta'addan jami'anta wadanda a kullum ba abin da suka sa a gaba in banda zubar da jinin musulmi da takura musu rayuwa. Irin wadannan goyon baya kuwa sun hada har da na tattalin arziki, siyasa, soji da dai sauransu, na baya-bayan nan kuwa shi ne hawa kujeran nakin da kasar Amurka ta yi wa kudurin yin Allah dai da haramtacciyar kasar Isra'ila a kwamitin tsaro kan kisan gillan da suka yi wa Shaikh Ahmad Yasin shugaban kungiyar gwagwarmayar Palastinawa ta Hamas. Babu shakka irin wannan mummunan aiki na Amurka ya kasance abin da ke kona ran al'umman musulmi a kowace rana don haka ko ba a fadi ba hakan zai iya sanya musulmi su nemi daukan fansa a kan duk wata manufa ta Amurka a duk lokacin da suka sami daman yin hakan.

Wadannan abubuwa da muka ambata a sama dai suna daga cikin abubuwan da ake ganin su a matsayin ummul aba'isin din yaduwar ayyukan ta'addanci a duniya.

To sai dai kuma duk da haka, wani abin da ke da muhimmanci shi ne cewa duk da irin wadannan abubuwa da suke faruwa akan musulmi, to amma fa addinin Musulunci ko da wasa bai yarda da ayyukan ta'addanci da zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba. A bisa madaukakiyar koyarwa ta Musulunci, zubar da jinin mutumin da bai ci bai sha ba abu ne da ba za a amince da shi ba, duk da cewa hakan yakan halalta idan an kai shi ne akan masu wuce gona da iri ko kuma 'yan mamaya, to fa a wannan yanayi ba wai ma kawai halal ba ne face ma dai aikata hakan wajibi ne. Wannan halalci ba wai kawai a dokokin na Musulunci ba ne, face ma dokokin kasa da kasa, suna ganin fada da mamaya da tabbatar da hakkoki abu ne da yake halal kana kuma abin so. Don haka ko da wasa malaman Musulunci da kuma ma'abuta gaskiya da adalci na duniya ba sa ganin tsayin daka da gwagwarmayar da kungiyoyin kwatar 'yanci da korar 'yan mamaya a matsayin aikin ta'addanci, face dai aikin da ya kamata a jinjina masa.

Ala kulli halin dai, ci gaba da yaduwar kai hare-haren 'ta'addanci' yana nuni ne da cewa amfani da karfi ba hanya ce da ta dace wajen kawo karshen ta'addanci ba, face dai hakan ba abin da zai haifar in banda karuwar wannan annoba. Hanya guda kawai ta kawo karshen 'ta'addanci' shi ne kawo karshen abubuwan da suke kawo shi, wadanda mafi yawa daga cikinsu sun samo asali ne daga ayyukan kasashen yammaci wadanda suka kururuta duniya da cewa suna son ganin bayan ayyukan 'ta'addanci'. Matukar kuwa ba hakan aka yi ba to kawar da ta'addanci fa abu ne mai wahala. Allah Ya saukaka.