|
|
|
|
| |||
|
Daga: Muhammad Awwal Bauchi IRIB-Tehran - I.R.of Iran awwalubauchi@yahoo.com ________________________
A safiyar ranar 30 ga watan Disambar da ta wuce ne
hukumar Iraki ta zartar da hukumcin kisan da aka yanke wa tsohon shugaban kasar
Irakin Saddam Husaini inda aka rataye shi har lahira, bayan watanni na shari'a
da yanke masa hukumcin kisa saboda samunsa da hannu dumu-dumu wajen kashe
al'ummar garin Dujail.
An haifi Saddam Husain ne a shekarar 1937, wadanda
suka sanshi sun ce tun yana karami an san shi da hatsabibanci. A shekarar 1957
ne ya shiga jam'iyyar Ba'ath ta kasar Iraki, bayan shekara biyu kacal da shiga
jam'iyyar ya shirya wani shiri na kashe shugaban jam'iyyar na lokacin Abdul
Karim Kasim a shekarar 1959 sai dai bai yi nasara ba. Har ila yau bayan nasarar
da 'yan jam'iyyar Ba'ath din suka samu a juyin mulkin da suka shirya a shekarar
1968, an nada Saddam a matsayin mataimakin shugaban kasar Irakin na lokacin
Ahmad Hasan Bakr. A cikin wannan lokaci da yake matsayin mataimakin shugaban
Iraki, Saddam ya nuna kwazonsa na gamawa da duk masu adawa da shi da zubar da
jinin mutane ba tare da tsoro ko shakkan kowa ba. Kai daga karshe ma a shekarar
1979, Saddam ya tilasta wa Ahmad Hasan Bakr yin murabus inda shi kuma ya dare
karagar mulkin kasar.
Darewar Saddam mulki ke da wuya sai ya ci gaba da
dirkan mikiya ga duk wanda ke adawa da siyasarsa na daga 'yan jam'iyyar Ba'ath
din da ma wasunsu. Cikin wannan lokaci Saddam ya kashe wani adadi mai yawan
gaske na 'yan jam'iyyar Ba'ath din wadanda bai yarda da su ba ko kuma wadanda ke
adawa da siyasarsa ta mamaye dukkanin madafan mulki. Haka nan kuma don tabbatar
da wannan manufa tasa ta zama bakin fadi kawai a Iraki, Saddam ya rike kusan
dukkanin mukamai masu muhimmanci na kasar da suka hada da shugabancin kasa,
shugabancin jam'iyyar Ba'ath, babban kwamandan sojojin kasar, babban kwamandan
kungiyoyin leken asirin kasar da dai sauran mukamai masu muhimmanci. A takaice
dai Saddam ya zamanto babban dan mulkin kama-karya da dukkan ma'anar
kalmar.
Masu iya magana dai sukan ce wai nagari na kowa
mugu sai mai shi, bisa la'akari da wannan dabi'a ta mulkin karya da Saddam yake
da ita ya sanya shi bai yarda da kowa ba face wasu 'yan kadan daga cikin mabiyan
nasa kamar yadda su ma jama'a din ba su yarda da shi ba. Kai wasu bayanai ma sun
tabbatar da cewa an kai wani matsayin da hatta na kurkusa da shi ma Saddam ba
wai ya amince da su ne dari bisa dari ba. Wasu rahotanni ma sun bayyana cewar
Saddam mutum ne da ba ya yarda da duk wani nuna rashin amincewa da ra'ayinsa
daga kowani irin mutum ne kuwa, hakan ne ma ya sanya shi harbe wani daga cikin
'yan majalisar ministocinsa har lahira saboda ya bayyana ra'ayinsa
kan wata mas'ala da ta
saba wa tasa a wani taro da suke yi. Wani abin da ke tabbatar da hakan kuma shi
ne kisan gillan da ya yi wa Mahir Abdurrashid daya daga cikin manyan
kwamandojinsa kuma na kurkusa da shi a lokacin yakin da ya kallafa wa Iran,
bayan gama yakin saboda tsoron da yake da shi cewa kada ya yi kokarin kawar da
shi saboda irin suna da daukakan da ya samu.
A fili yake cewa idan har haka Saddam yake mu'amala
da na kurkusa da shi da wadanda suka taimaka masa wajen ci gaba da mulki, to ya
ya kuma ga sauran jama'a wadanda babu wata alaka da ta hada su da shi? Wadanda
suka san Saddam sun tabbatar da cewa mahangarsa
kan jama'a ita ce ko dai
su mika masa kai ko kuma su fuskanci kisa. Duk da cewa mafi yawa daga cikin
al'ummar kasar sun mika masa kan (suna so ko ba sa so) amma kuma a koda yaushe
suna jiran samun wata dama da za su kawar da shi wato su yarda kwallon mangoro a
huta da kuda. Abin da ke tabbatar da hakan kuwa shi ne kokarin da al'ummar kasar
suka yi na kawar da shi bayan yakin kame kasar Kuwaiti da ya yi da fitar da shi
da karfin tsiya da sojojin hadin gwuiwa karkashin jagorancin Amurka a shekarar
1991. Rahotanni sun tabbatar da cewa a yayin wannan bore na al'umma, sun sami
nasarar kame yankuna daban-daban na kasar da 'yantar da su daga mulkin zalunci
na Saddam da ba don daukin da Amurka ta kawo masa ba da babu makawa da sun kawar
da dan mulkin kama-karyan. Sai kuma a shekara ta 2003 lokacin da Amurka ta kai
hari kasar da kawar da gwamnatin kama karyan. A lokacin mulkinsa dai Saddam ya
kashe dubun-dubatan al'ummar kasar, kamar yadda wasu dubun dubatan kuma aka
sanya su a gidajen yari da azabtar da su a wasu lokuta ma wasu sukan rasa
rayukansu sakamakon azabtarwar baya ga wadanda aka kore su daga kasar da dai
sauran nau'oi na mulkin kama karya. A lokacin mulkin nasa Saddam ya watsa 'yan
leken asirinsa zuwa dukkanin yankuna da lungunan kasa don tattaro labarai, inda
komai kashin zargi kan rashin biyayya ga gwamnatin zai iya kai mutum ga mutuwa
ko kuma zama gidan yari na tsawon lokaci da azabtarwa kala-kala.
A wasu lokuta 'yan mulkin kama-karya sukan yi
kokarin fakewa da wani abin da suka san al'umma sun yi imani da shi don su dan
sami goyon bayansu alhali su kuwa ba su imani da wannan abu ba. Daga cikin irin
wadannan abubuwa da 'yan mulkin kama-karyan suke fakewa da shi har da addini
wato su nuna cewa suna da alaka da addini saboda irin matsayin da addini yake da
shi a idon mutane, alhali kuwa ba su da wata alaka da addini. Saddam ma bai
tsira daga wannan abu ba. A lokacin mulkinsa, musamman lokacin yakin tekun fasha
na farko da aka yi don fitar da shi daga kasar Kuwaiti, ya yi amfani da addini
da nuna cewa yana da alaka da shi don neman goyon bayan al'ummar musulmi. Amma a
hakikanin gaskiya Saddam mutum ne da ba shi da wata alaka da addini kai yana ma
adawa da shi. Daya daga cikin abin da ke tabbatar da hakan shi ne cewa shi ne
shugaban jam'iyyar Ba'ath wacce jam'iyya ce da take adawa da addini. Saboda haka
ne ma malaman Musulunci suka zamanto makiyan farko gare shi. Tsawon mulki Saddam
ya tsare da kashe malaman Musulunci masu yawan gaske bayan ya azabtar da su
azabtarwa, daga cikinsu akwai Ayatullah Shahid Sayyid Muhammad Bakir Sadr,
Ayatullah Azzawi, Ayatullah Burujerdi, Ayatullah Sadik al-Sadr da dai sauransu,
kai shi Ayatullah Bakir Sadr kan ma an ce shi da kansa ya kashe shi. Wani abin
da ke nuni da adawar Saddam ga addini shi ne matsin lambar da yake yi wa
makarantun addini (hawza) na birnin Najaf ta yadda ya mayar da ita tamkar ma ba
ta nan. To amma saboda yana son jan hankulan jama'a zuwa gare shi da goyon
bayansu musamman a lokutan da yake cikin matsala, sai ya nuna tamkar yana da
alaka da addini don ya yaudari al'umma, kamar yadda ya aikata lokacin yakin
Tekun Fasha na farko da kuma lokacin da ake masa shari'a yayin da yake zuwa kotu
da Alkur'ani da janyo ayoyin Alkur'anin a duk lokacin da zai fara magana kai
hatta ma lokacin da za a rataye shi.
Zalunci da ayyukan Allah wadan Saddam Husaini ba su
takaita kawai kan
al'ummar Iraki ba, hatta ma ga sauran al'ummomin kasashen da ke makwabtaka da
shi. Misalin hakan shi ne harin da ya kai wa al'ummomin kasashen Kuwait da Iran.
A yakin da ya kallafawa Iran na shekaru takwas dubun-dubatan al'ummomin kasashen
biyu ne suka rasa rayukansu. Babu irin ta'addancin da Saddam bai yi wa al'ummar
Iran a lokacin yakin ba da suka hada da kai hare-hare kan gidajen fararen hula
da gangan, kai hatta jiragen sama da na kasa na fasinja ba su tsira daga
hare-haren Saddam din ba, mafi munin abin ma shi ne amfani da ya yi da makamai
masu guban da ya samo su daga kasashen yammaci a kan al'ummar Iran. Kamar yadda
ya yi amfani da irin wadannan makamai a kan al'ummar Kurdawan Halabja na kasar
Iraki inda kimanin mutane dubu biyar suka rasa rayukansu. Har ya zuwa yanzu
al'ummomin Iran da Irakin da ya yi amfani da makamai masu guba a kansu suna ci
gaba da fuskantar matsaloli da cututtuka daban-daban.
A takaice dai Saddam mutum ne ma'abucin girman kai
mai son tabbatar da mulkinsa ko ta wata hanya. Haka ya ci gaba da zaluntar
al'ummarsa da zubar da jininsu har lokacin da aka kawar da shi ya shiga cikin
yanayin wulakanci da kaskanci. Bayan kawar da gwamnatinsa da kamun kazar kukun
da aka yi masa, gwamnatin Irakin ta ba shi damar kare kansa a gaban kotu,
sabanin yadda shi ya kasance yana yi wa al'ummar Irakin. Duk da cewa ayyukan
Allah wadai din da ya aikata a fili suke amma dai an ba shi damar kare kansa, to
amma sakamakon gazawar da yayi wajen kare
kan nasa, kotu ta yanke masa hukumcin kisa da aka
zartar da shi a ranar 30 ga Disambar baran. Bakar siyasar Saddam ita ce ta kai
al'ummar Iraki cikin halin da suke ciki yanzu. Ita ce ta yi sanadiyyar mamaye
kasar da Amurkawa suka yi, ita ce ta sanya kasar cikin halin tsaka mai wuya na
tsaro da tattalin arziki da take ciki.
Ala kulli halin, rayuwar
Saddam da yadda karshensa ya kasance babban darasi ne ga kowa musamman masu
mulkin kama-karya na duniya wadanda suke ganin cewa mulkin nasu ne kawai, na su
san cewa Allah Madaukakin Sarki Ya yi alkawarin mummunan karshe ga duk wani
azzalumi, lokaci ne kawai ake jira. |
||||