|
|
|
|
| |||
|
Daga: Muhammad Awwal Bauchi IRIB-Tehran - I.R.of Iran awwalubauchi@yahoo.com ________________________
A ranar 30 ga watan
Disambar da ta wuce ne mahukunta a kasar Iraki suka rataye tsohon dan mulkin
kama-karya na kasar, Saddam Husain (ko kuma Saddam al-Tikriti kamar yadda aka
sanshi a da kafin ya canza sunansa) bayan da kotun manyan laifuffuka ta kasar ta
yanke masa hukumcin kisa sakamakon samunsa da laifin kashe mutanen kauyen Dujail
su 148. Ita dai wannan shari’a an fara ta ne a ranar 19 ga watan Oktoban 2005
sannan bayan zama 55 na kotun aka yanke masa hukumcin kisa a ranar 5 ga watan
Nuwamban bara (2006). Duk da cewa bisa ga tsarin mulkin kasar Iraki dole ne a
zartar da hukumcin da aka yanke cikin kwanaki talatin daga lokacin da aka yanke
hukumcin, to sai dai kotun ta ba shi damar daukaka kara idan har bai yarda da
hukumcin da aka zartar din ba, hakkin da ya hana da dama daga cikin wadanda ya
zalunta lokacin mulkinsa. Lauyoyi masu kare shi sun daukaka karar to sai dai
bayan wani lokaci kotun daukakan karar ta same shi da laifin da ake tuhumarsa da
shi inda ta tabbatar da hukumcin da aka yanke masa na farko. To sai dai da dama
daga cikin masana suna ganin bai kamata a ce kotun da za ta yi shari’ar dan
ta’adda irin Saddam ta takaita kawai da shari’a da yanke hukumci kan daya daga
cikin ayyukan ta’addancin da ya aikata ba tare da an yi dubi cikin sauran
ayyukan ba, wadanda ma watakila sun fi na farko girma da daga hankali ba. Saboda
a hakikanin gaskiya Saddam ya aikata muggan laifuffukan da binciken kowani guda
daga cikinsu zai fitar wa da duniya muhimman bayanan da suka shiga mata duhu.
An rataye Saddam ne alhali
shari’ar da ake masa kan batun Anfal, wato kisan kiyashin da gwamnatinsa ta yi
wa dubun-dubatan Kurdawan kasar a 1988, ba a riga da an gama ta ba. Baya ga
hakan, akwai kuma wasu batutuwan wuce gona da irin Saddam din da ba a ma yi
maganarsu ba irin su kisan kiyashin da ya yi wa al’ummar kasar a 1991, ga kuma
batun azabtarwa da kisan gillan da aka yi a gidajen yarinsa irin su Abu Ghuraib
da sauransu. Baya ga hakan kuma ga batun harin da ya kai wa kasashen Iran da
Kuwaiti, shi ma dai ba a yi maganarsa ba duk kuwa da kiran da kasashen biyu suka
yi na a yi nazarin batun, alhali da a ce an yi magana kansu, musamman yakin
shekaru takwas da ya kallafa wa Iran da abubuwa da dama da suka shiga duhu sun
fito fili.
Tambayar da take tasowa
dai ita ce, wai shin me ya sa aka gaggauta rataye Saddam ne duk kuwa da cewa ba
a tabo ko da kashi guda cikin dari na munanan ayyukan da ya aikata ba? Da dama
daga cikin masana sun yi amanna da cewa daya daga cikin dalilan gaggauta rataye
Saddam shi ne hana bayyanar da irin alaka da taimakon da gwamnatocin kasashen
yammaci musamman Amurka suka ba wa Saddam a lokacin mulkinsa musamman kan yakin
da ya kallafa wa Jamhuriyar Musulunci ta
Iran.
Masana da marubuta sun yi rubuce-rubuce masu yawan gaske kan wannan batu, daga
cikin har da fitaccen marubucin nan dan kasar Ingila Robert Fisk. A cikin wata
makala da ya rubuta a jaridar Independent ta kasar ya yi ishara da
ganawar da manyan jami’an Amurka suka ta yi da Saddam kafin fara wannan yaki a
shekarar 1980 inda Amurkawan suka ba shi taimakon makamai masu guba sannan kuma
sun san zai yi amfani da su a kan al'ummar Iran. Marubucin ya ci gaba da cewa:
“Rataye Saddam ya zamanto kariya ga sirrukan Amurka. Irin taimako da goyon baya
na boye da ya saba wa tunani da Amurka da Ingila suka jima suna ba wa Saddam
lamari ne da shugaban Amurka da prime ministan Birtaniyya ba sa so ya fito
fili”.
Don haka, sabanin abin da
jami’an Amurkan suke nunawa, babu kokwanto suna da hannu cikin gaggauta rataye
Saddam da aka yi. A hirar da tashar talabijin din CNN ta yi da mai ba da shawara
wa tsohon shugaban Amurkan Jimmy Carter kan harkokin tsaro Zbigniew Brzezinski
ya bayyana cewar: “Har zuwa ‘yan awoyi kafin rataye shi, Saddam ya kasance a
hannun Amurkawa ne, hakan yana nuni da cewa Amurka ita ce ummul aba’isin din
rataye Saddam. Ita ma jaridar Humanity ta kasar Faransa ta yi ishara da
cewa: “A hakikanin gaskiya tsoron da Amurka da kawayenta suke da shi kan
bayyanar da irin hannun da suke da shi cikin danyen aikin Saddam, shi ne dalilin
gaggauta rataye Saddam don kada asirinsu ya tonu”. Jaridar tana ganin Amurka da
gwamnatocin kasashen Turai suna da alhakin kera makamai masu guba da amfani da
su da Saddam ya yi. Shi ya sa ma jaridar ta ci gaba da cewa: “Saddam ya tafi
tare da batutuwa masu yawan gaske tare da shi”. Hakan dai shi ne gaskiyar
lamarin, saboda ci gaba da shari’a wa Saddam tamkar shari’a ce ga wadannan
kasashe sakamakon irin hannun da suke da shi wajen ayyukan da ya aikata.
Baya ga ‘yan koke-koken da
aka dinga yi kan yadda aka gudanar da shari’ar musamman yadda ba a tsaya an
gabatar da dukkanin koke-koke da ta’addancin da Saddam din ya aikata a gaban
kotun ba, rataye Saddam har ila yau ya fuskanci mayar da martani daban-daban.
Wadannan mayar da martani sun hada da masu nuna farin cikinsu kan zartar da
hukumcin, wato al’ummomin da Saddam ya cutar a kasashen Iraki, Iran da Kuwait da
sauransu da kuma wasu ‘yan tsiraru da suka nuna fushinsu da suka hada da ‘yan
jam’iyyar Ba’ath ta Iraki da sauran larabawa da suka rufe ido kan gaskiya. Sai
dai a hakikanin gaskiya babu wani mutum mai hankali da zai rufe ido
kan irin zaluncin da Saddam ya aikata a lokacin
mulkinsa. Wasu kuma gani suke rataye Saddam din a irin wannan yanayi da kasar ke
ciki na rashin tsaro da rikice-rikice lamari ne da bai dace ba, suna ganin
dacewa ya yi a hakura har lokacin da al’amurra suka daidaita.
Ala kulli hal, dukkan
hakan ra’ayi ne da kowa ke da hakkin rike nasa, to amma abin bakin cikin shi ne
yadda wasu daga cikin kasashen Larabawa da kafafen watsa labaransu, bugu da kari
kan wasu daga cikin masana da malaman addini suke kokarin amfani da batun
rataye Saddam din wajen haifar da rikici da sabani tsakanin musulmi, wato mabiya
tafarkin Shi'a da Sunna. Wadannan mutane suna kokarin nuna Saddam a matsayin
mabiyin tafarkin Sunna wanda ‘yan Shi'a suka kashe shi don daukan fansa kansa
kai ka ce kamar ‘yan Shi'a kawai Saddam ya kashe a lokacin mulkinsa, alhali sun
san ba haka ba ne kai sun ma san cewa Saddam mutum ne da babu ruwansa da addini
ballantana ma Sunna ko Shi'a, a wurinsa kowa ma nama ne. Babban misalin irin
wadannan kafafen watsa labarai ita ce tashar talabijin ta Al-Jazeera ta kasar
Katar wacce ta ba da dukkan karfinta wajenta wajen nuna Saddam a matsayin wani
gwarzo wanda aka zalunce shi sakamakon rataye shi da aka yi. A daidai wannan
lokacin tashar Al-Jazeeran ta yi ta gabatar da rahotanni da hirarraki da wasu
mutane da suka nuna rashin adalcinsu a fili duk dai da nufin nuna cewa rataye
Saddam daukan fansa ne da ‘yan Shi'a suka yi kan Saddam da ma ‘yan Sunnar Iraki
kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce ummul aba’isin din hakan.
Haka nan wasu kasashen
larabawan ma a fili sun nuna rashin jin dadinsu da rataye Saddam din da aka yi.
Babban abin bakin cikin ma shi ne cewa da dama daga cikin wadannan kasashe sun
fuskanci barazana da cutarwa daga Saddam din lokacin mulkinsa, wasu daga cikinsu
ma sun koma ga Amurka ne don ta kare su daga barazanar Saddam, amma a yau kuma
su ne suke nuna rashin jin dadi da rataye shi da aka yi. Mai yiyuwa ne wasu su
yi mamakin wannan matsaya ta su, kamar yadda kuma mai yiyuwa ne wasu su rudu da
hakan, to amma ga wanda ya san abin da ke gudana a yankin nan (Gabas ta tsakiya)
ko da wasa ba zai rudu da wannan matsaya ta su ko kuma mamaki ba.
Da farko dai kowa ya san
yadda wadannan kasashe na larabawa suke bin Amurka sau da kafa da kokarin biya
mata bukatarta kowani iri ne kuwa. Abu na biyu kuma shi ne cewa kowa ya san
babbar siyasar Amurka a yankin Gabas ta tsakiya a wannan lokaci shi ne haifar da
rikici tsakanin mabiya tafarkin Shi'a da Sunna. A matsayin misali babban kokarin
da Amurkan take yi a halin yanzu shi ne nunawa mabiya tafarkin Sunna cewa irin
karfin da ‘yan Shi'a suke samu a wasu kasashe kamar su Iraki, Labanon da Bahrain
(bayan shekara da shekaru na danne su da ake yi) a matsayin babbar barazana da
hatsari ga ‘yan Sunna, suna masu tuhumar Iran da cewa duk ita ce take tsara
hakan. To amma lamarin a fili yake cewa duk wata kasar da aka gudanar da tsarin
demokradiyya kamar yadda ya dace babu makawa wadanda suka fi yawa su ne za su yi
nasara, kamar yadda hakan ya ke faruwa a kasashen da mabiya tafarkin Sunna suka
fi yawa, don haka mene ne ya kawo hannun Iran cikin hakan. Don haka ba abin
mamaki ba ne idan aka ce wadannan kasashe suna kokarin biyan bukatar Amurkan ne
a yankin ta hanyar irin wannan matsaya tasu ta kokarin nuna goyon baya ga
bangare guda da rufe ido kan ayyukan ashshan da gwamnatin Saddam din ta aikata.
Ala kulli hal,
Saddam dai ya tafi tambayar da take yawo ita ce ya ya kasar Irakin za ta kasance
bayan rataye dan mulkin kama-karyan. A daidai lokacin da wasu suke ganin rataye
Saddam mafari ne na ci gaba da karuwar rikice-rikice da rashin tsaro a kasar,
wasu kuma suna ganin cewa za a samu rikice-rikice nan da can amma na wani lokaci
ne kawai, daga baya komai zai dawo daidai saboda kowa ya san Saddam azzalumi ne.
Wannan dai ra’ayi ne to sai dai abin da babu kokwanto cikinsa shi ne cewa babban
abin da zai magance matsalar da Irakin take ciki shi ne ficewar ‘yan mamaya daga
kasar da kuma kawo karshen tsoma bakin da kasashen waje suke yi ga harkokin
cikin gidan kasar da barin Irakawan su zaba wa kansu abin da ya dace da su.
Hakan ne kawai zai magance matsalar da Irakin take fuskanta. Hakan nan kuma wani
abin da zai tabbatar da zaman lafiya a kasar shi ne al’ummar musulmin kasar,
Shi'a da Sunnarsu, su fahimci cewa Saddam dai ya tafi ba zai kuma dawo ba har
abada, don haka su yi watsi da duk wani kokarin raba kansu don biyan bukatun
wasu na daban. |
||||