Saddam Husain...Karshen Alewa Kasa:
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Mutuwa kalma ce mai daga hankali da ba kasafai ake son jinta ba ballantana ma a yi farin ciki da zuwanta, to sai dai a wasu lokuta a kan yi farin ciki da zuwanta kai a yi ma fatan gaggauta zuwanta musamman idan za ta fada ne kan wani mutum irin Saddam Husain da rasuwarsa ke cike da zalunci da bala'i ga al’umma. A hakikanin gaskiya ranar 30 ga watan Disamban 2006 rana ce ta farin ciki ga mafiya yawan al’umma musamman al’ummomin kasashen Iraki, Iran da Kuwait, wadanda suka fi cutuwa daga bakin mulkin wulakatancen dan mulkin kama-karyan, wanda ya fara rayuwarsa a wulakance ya kare ta a wulakance.

Saddam Husain dai azzalumin shugaba ne wanda ya janyo bala'i ga al’ummar Iraki. Tun yana karami ya ke cutar da wadanda ke tare da shi, lokacin da ya dare karagar mulki kuwa, ya yi amfani da karfi da kudi wajen tilasta musu mika wuya, wadanda suka ki kuwa ko dai gudu daga kasar ko kuma su saurari kisa ko azabtarwa mai tsanani.

Farin cikin da al’umma suka nuna kan rataye Saddam ko da wasa bai zama abin mamaki ba, babban abin mamaki kuma abin takaicin shi ne yadda wasu suka dinga kokarin rage armashin wannan babbar nasara kai kace akwai wata boyayyiyar aniya da suke da ita, kai a gaskiya ma akwai ta. Saboda rataye Saddam ke da wuya sai ga wasu maganganu suna yawo irinsu ‘rataye Saddam daukan fansar ‘yan Shi'a ne kan ‘yan Sunna’ ‘Farisawa ne suka dau fansa kan Larabawa’ ‘kashe Saddam ranar salla keta hurumin musulmi ne’ da dai sauran maganganu marasa tushe da wasu suka dinga yadawa don wata manufa ta siyasa.

Wadannan maganganu dai ba su da wata kima a idanuwan al’ummar Iraki, (da ma na Iran da Kuwait da sauran al’ummomin da son zuciyarsu ba ta rufe musu ido ba) saboda sun san wane ne Saddam, saboda har yanzu ba su mance da jinin mutanen Dujail 148 da Saddam ya zubar ba, ba su mance da Kurdawa sama da dubu dari da tamanin da ya watsa musu iskar gas mai guba harin ‘Anfal’ ba, ba su mance da jinin Shahid Bakir al-Sadr da ‘yar’uwarsa Bintul Huda da ya zubar ba, ba su mance da jinin masu boren 1991 da ya zubar ba, ba su mance da jinin Iraniyawa da Irakawa sama da miliyan guda da ya zubar a lokacin kallafaffen yakin shekaru takwas ba, ba su mance da dubban ‘yan kasar Kuwait da suka rasa rayukansu da dukiyarsu lokacin da ya mamaye kasar, ba su mance da….ba su mance da….ba su mance da….don haka ne suke la’antar duk wanda ma ya tausayawa Saddam din da kiran da a yanke alaka da duk wata kasa da ta nuna tausayawa gare shi.

A hakikanin gaskiya wasu daga cikin abubuwan da aka tayar da su, bayan rataye Saddam, ba sa bukatar bata lokaci kansu, magana irinsu daukan fansa ‘yan Shi'a a kan Saddam, saboda ba ‘yan Shi'a ne kawai ya cutar ba, kai a takaice ma ba ruwansa da wani Sunna ko Shi'a, wajensa duk wanda ya ki mika kai makiyi ne, Shi'a ne ko Sunna. Haka nan batun Farisanci da Larabci, a wajen Saddam, babu bambanci tsakanin Balarabe da Bafarishe, mamaye Kuwait wacce kasa ce ta Larabawa, kuma mafiya yawan al’ummarta ma Sunna ne, kai ta ma taimaka masa lokacin da yake yakan Iran, ya isa zama hujja. Kai ko harin da ya kai Iran, da mafiya yawan al’ummarta Farisawa ne, yayi hakan ne don biyan bukatar tsoffin iyayengijinsa, wadanda suka daga  tauraruwarsa sama daga baya kuma suka tsakuloshi daga cikin rami tamkar bera.

Babban abin da ya fi daukan hankula daga cikin wadannan maganganu shi ne batun rataye Saddam ‘ranar salla’. A hakikanin gaskiya hakan kokari ne kawai na kawar da hankula daga ayyukan Allah wadai da Saddam ya aikata da wasu ke kokarin yi da kuma biyan bukatar sabuwar siyasar Amurka a yankin Gabas ta tsakiya ta rarraba kan al’ummar musulmi. Abin tambayar ma a nan shi ne mene ne laifin rataye Saddam ranar salla, shin laifi ne yin hakan. A shari’ar Musulunci dai babu inda aka haramta zartar da haddi a ranar salla, ballantana har rataye Saddam (ranar salla a wajen wadansu kasashe) ya zamanto abin tada jijiyoyin wuya ko kuma a ce cin mutumcin musulmi ne. (Duk da cewa ba Saddam ba abin koyi ba ne) amma shi kansa Saddam mutane nawa ya rataye ranar sallar, me ya sa bai zamanto abin magana ba. Kasar Saudiyya tana daga cikin kasashen da suka nuna damuwarsu kan wannan batu, to amma abin tambaya a nan shi ne me za ta ce kan kashe alhazan Iraniyawa (da ma na sauran kasashe) da ta yi a dakin Allah ranar Arafa a shekarar 1987 alhali suna yin Allah wadai ne da ma’abuta girman kan duniya. Shin hakan shi ne yafi zama cin mutumcin musulmi ko kuma rataye Saddam da ke kashe musulmin?

Ashe kashe Saddam ranar salla ba ma zai kara wa sallar armashi ba ne saboda zai zamanto murna kan murna? Shin masu wannan ra’ayi ba sa ganin kashe Saddam zai sanya karin farin ciki cikin zukatan iyalan Kurdawa alal akalla kusan dubu dari biyu da Saddam ya kashe da iskar gas, ashe kashe Saddam ba zai kara armashin sallar al’ummar Kuwait ba? Ashe rataye Saddam ranar salla ba zai kara murna kan murna ga miliyoyin al’ummar Iran da ya cutar ba? Ashe rataye Saddam ranar salla ba zai kara faranta ran al’ummar Iraki da ya yi sama da shekaru talatin yana cutar da su ba? Ashe kashe Saddam ranar salla ba zai kara murna kan murna ga…..? Ashe kashe Saddam ranar salla ba zai kara murna kan murna ga…..? kai abin dai da yawa wai mutuwa ta shiga kasuwa. A takaice na yi amanna da cewa rataye Saddam ‘ranar salla’ zai kara armashin sallar mafiya yawa daga cikin al’ummomin musulmi na yankin Gabas ta tsakiya wadanda suka fi cutuwa da mulkin zalunci na Saddam, kai hatta ma wadanda suka nuna bakin ciki daga cikinsu, imma dai wadanda aka ruda ne ko kuma wadanda kabilanci ya rufe musu ido (wadanda su abin tausayi ne) ko kuma wadanda suka ci daga ‘babban masakin’ Saddam  din ne, wadanda su ma sun cancanci a hukumta su, idan ma ba rataye su ranar sallar ba.

Ni ina ganin maimako a dinga tayar da irin wadannan tambayoyi kamata ya yi a bijiro da wasu batutuwa irin su me ya sa aka gaggauta rataye Saddam din ba tare da an jira an gama masa shari’a kan sauran muggan ayyukan da ya aikata ba. Da dama dai suna ganin rataye Saddam da aka yi a daidai wannan lokaci (ba wai ina nufin ranar salla ba fa saboda ni ban ga laifin yin hakan ranar sallar ba) da kasar take cikin mawuyacin halin rashin tsaro sannan kuma ake kokarin hado kan al’ummar kasar waje guda lamari ne da bai dace ba, da kamata ya yi a jinkirta har zuwa wani lokaci, lokacin da lamurra suka dan lafa sai a aiwatar ko da kuwa ranar salla ce, babu wani bambanci. A ganina kashe Saddam a irin wannan yanayi na daga cikin kura-kuran gwamnatin Maliki, duk da cewa sun fadi dalilansu na yin hakan, da cewa sun yi hakan ne saboda wasu bayanai da suka zo musu na kokarin da wasu suke yi na sace Saddam din da fitar da shi daga kasar don ya zamanto wani gwarzo. To wannan dai ra’ayinta kenan, shin haka lamarin yake ko ba haka ba, allahu a’alam, amma dai abin da babu kokwanto cikinsa shi ne akwai hannun Amurkawa wajen gaggauta rataye shi saboda ci gaba da yi masa shari’a kan sauran batutuwan da za su zo nan gaba ba zai haifar da da mai ido ga Amurkan ba saboda hannun da take da shi dumu-dumu cikin ayyukan Allah wadan da Saddam ya aikata.

Tun farko kafa kotun da za ta yi wa Saddam da jami’an tsohuwar gwamnatinsa shari’a  jama’a suke da alamun tambayoyi kan yadda za a gudanar da shari’ar. Da dama dai sun so ne a kai Saddam din kotun duniya inda watakila a can lamurra za su fi fitowa fili, amma Amurka ta ki amincewa da hakan, alamar tambaya ta farko kenan. Sannan abu na biyu shi ne yadda aka fara da batun Dujail wanda batu ne karami idan aka kwatanta shi da sauran batutuwan da suke kas. Tun a lokacin da dama suke ganin akwai abin da Amurkawan suke son cimmawa, na farko dai shi ne cewa da wuya a iya tabbatar da hannunsu cikin kisan gillan da aka yi wa mutanen Dujail, don haka cikin sauki za a iya samun Saddam da laifi a rataye shi ba tare da an kai ga sauran batutuwan ba. Abu na biyu kuwa shi ne shafa kashin kaji ga ‘yan Shi’an kasar wadanda su ne ke rike da madafan mulkin kasar cewa sun nuna son kai saboda mutanen Dujail din ‘yan Shi'a ne. Abu na biyu kuma shi ne yadda aka ta datse da dama daga cikin bayanan da Saddam da mataimakansa suke yi a kotun don kada jama’a su ji (ana fakewa da batun tsaro). An tsara kotun ne ta yadda aka shirya wa alkalin kotun wasu maballai guda biyu, na farko zai iya katse abin da Saddam yake fadi idan ya matsa shi na biyun kuma zai iya rufe inda wadanda ake tuhuma suke da labule a duk lokacin da suka yi ‘wani abin da bai dace ba’. Don haka ‘yan jaridu da sauran mutanen da suke kotun za su iya ji da ganin abin da aka yarda su gani ne kawai. Sannan kuma akan nuna wa mutane abin da ke gudana a kotun ne da jinkiri na mintoci ashirin zuwa talatin don a samu damar cire abin da ba a so jama’a su ji. Wadannan abubuwa ne da suke sa shakku cikin yadda kotun take gudanar da ayyukanta. A nan yana da kyau a fahimce ni da kyau ba wai ina kokarin kare Saddam ba ne, face dai ina kokarin nuna yadda aka yi kokarin hana duniya sanin wasu boyayyun hannaye cikin ayyukan Allah wadan da Saddam ya aikata.

Duk da cewa mutanen da Saddam ya cutar suna farin cikin yadda karshen dan mulkin kama karya ya kasance, sai dai su da sauran al’ummomin duniya ba su ji dadin yadda aka bar wasu tambayoyi ba tare da ya amsa su da kansa ba. A gaskiya al’ummar Iraki da sauran al’ummomin da Saddam ya cutar, kafin a kashe shi, sun so su san ya ya aka yi Saddam ya dare kan mulki? Sun so su san gudummawar da kungiyar leken asirin Amurka CIA ta bayar a wannan bangare? Sun so su san hakikanin dalilinsa na kawo wa Iran hari? Wani irin taimako suka ba shi yayin yakin? Wasu gwamnatoci ne suka ba shi makamai masu guban da ya yi amfani da su akan al’ummar Halabja na kasar Iraki, da al’ummar Sardasht na kasar Iran da kuma sauran dakarun Iran a lokacin kallafaffen yaki? Sun so su san irin goyon baya da lamunin da suka ba shi wajen hana gurfanar da shi a gaban kuliya? Sun so su san me tsohon sakataren tsaron Amurka (ko kuma ministan yaki kamar yadda ‘yan Al-Manar suke kiransa) Donald Rumsfeld ya zo yi a Iraki a ranar 19 ga watan Disamban 1983 da ranar 24 ga Maris 1984? Wani irin gudummawa ce gwamnatocin Jamus, Ingila, Holland, Belgium da Tsohuwar tarayyar Sobiyeti suka bayar wajen mallakan makamai masu guba da Saddam ya yi? Wata gudummawa kamfanin Bechtel, da ke da alaka da kamfanin Halliburton na Amurka da kamfanonin Faransa da Jamus suka bayar a wannan bangare? Wa ya ba wa Saddam jiragen sama masu saukan ungulu (Bell helicopters) da suka watsa iskar gas mai guba ga Kurdawa? Me ya sa Amurka ta rufe ido da kuma ba wa Saddam karfin gwuiwan diran mikiya kan al’ummar kasar da suka yi bore lokacin yakin Tekun Fasha na farko inda ya kashe dubban al’ummar kasar? Wata gudummawa kasar Faransa ta bayar a wannan bangare? Wasu kasashe ne suka dinga hana fitar da kudurin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya don Allah wadai da ayyukan Saddam musamman lokacin yakin shekaru takwas da Iran? Su kuma kasashen larabawa na Tekun Fasha fa, wata gudummawa suka ba wa Saddam a wannan lokaci? Wata gudummawa ‘mai martaba’ Sarki Fahd bn Abdul’Aziz na ‘Saudi-America’ (ai Saudi Arabiya) da ‘mai martaba’ Sheikh Jabir bn Ahmad al-Sabah sarkin Kuwait suka bayar? Shin dala biliyan 85 din da aka sanar cewa kasashen Saudiyya, Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa sun ba wa Saddam a matsayin gudummawarsu wajen yakan Iran su kenan ko kuma ma akwai sauran da ba a fadi ba? Shin wadannan kasashen (larabawa) ne kawai suka ba wa Saddam taimako ko kuma akwai wasu na daban irin su Masar da Jordan? Kai tambayoyin dai suna da yawan gaske, wadanda babu wanda zai amsa su in ba Saddam ba. Don haka ne masana suke ganin Amurkawa da kawayensu sun amince da gaggauta rataye Saddam ne don rufe amsoshin wadannan tambayoyi da ma wasunsu. Abin bakin ciki ne yadda Saddam ya tafi wajen da aka tanadar wa irinsa alhali yana dauke da irin wadannan bayanai.

Saddam dai shi ne ummul aba’isin din mummunan halin da al’ummar Iraki da ma na yankin Gabas ta tsakiya suke ciki, sannan kuma sunansa ya dasu cikin zukatan al’ummar duniya a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan ta’addan da tarihin duniya ya shaida. Saboda baya ga laifuffukan da ya aikata da ake gani da jinsu a jika, akwai kuma wasu laifuffukan da ya aikata wadanda ake ganin mummunan tasirinsu ga yankin Gabas ta tsakiya. Daga cikinsu akwai:

1- Shi ne sanadin asarar rayuka da dukiyan kasashen Iran da Iraki sakamakon yakin shekaru takwas da ya kirkiro tsakanin kasashen biyu.

2- Shi ne ummul aba’isin din jibge sojojin Amurka a yankin Tekun Fasha sakamakon yakin da ya kallafa wa Iran (bisa taimakon wasu kasashen Larabawa irin su Saudiyya da Kuwait da sauransu) da kuma sakamakon mamaye Kuwaiti da ya yi, wanda hakan ya janyo matsaloli ga yankin Gabas ta tsakiya da ba wa Amurka daman mamaye kasashen Afghanistan da Iraki.

3- Shi ne ummul aba’isin din gasar sayen makamai a yankin Gabas ta tsakiya wanda hakan ya ba kasashen Amurka, tsohuwar tarayyar Sobiyeti da sauran kasashen Turai samun damar sayar da makamansu daga kudaden kasashen musulmi da ya kamata a yi amfani da su a wasu bangarori na ci gaban kasa. Makaman da ba sa wani amfani wajen fuskantar makiya face al’ummomin da aka yi amfani da kudadensu wajen sayensu.

Saddam dai ya tafi (ilal jahim – kamar yadda Irakawa suke fadi) to sai dai babban abin bakin cikin shi ne yadda wasu suke ci gaba da ruduwa da wasu abubuwa na zahiri da ya nuna lokacin da ake masa shari’a da kuma lokacin da za a rataye shi, abubuwa irinsu rike Alkur'ani mai girma, karanto ayoyin Alkur'ani da kalmar shahada da sauransu.

Saddam ya jima yana rudan mutane ta hanyar fakewa da addini don cimma manufarsa musamman lokacin yakin tekun Fasha na farko lokacin da ya ke neman goyon bayan al’umma alhali tarihin rayuwarsa ya nuna cewa ba shi da wata alaka da addini musamman idan aka yi la’akari da alakar da yake da ita da jam’iyyar Ba’ath da ke gaba da duk wani abi da ke da alaka da addini.

Wannan sai ya tuna min da abin da ya rubuta na karshe-karshen rayuwarsa inda ya ce wai zai yi shahada don al’umma da kuma kalmar shahadar da ya yi kafin a rataye shi. Abin dai akwai ban dariya cikinsa, saboda da dai da gaske yake yi yana son shahada don ‘al’umma’ da ya yi tsayin daka wajen yakan Amurkawan lokacin da suka shigo kasarsa har ya yi shahadar ba wai ya shiga wasan ‘yar buya da Amurkawan ba kafin su zakuloshi cikin rami. Kai hatta ma lokacin da suka gano maboyar tasa, da ya fuskance su har ya yi shahadar, ba ya tsaya yana ce musu ‘ni ne Saddam Husain, shugaban kasar Iraki, ina son tattaunawa da ku’, kai Allah wadaran naka ya lalace. Da bai bari ‘ya’yansa Uday da Kusay sun wuce gabansa da nuna ‘jaruntaka’ sama da shi ba a wannan bangaren, saboda alal akalla su sun ‘kwama’ da Amurkawan kafin suka ci karfinsu.

Abin da ya fi zama wargi da wasa da hankulan mutane ma shi ne batun ‘kalmar shahada’ da Saddam ya yi lokacin da ya ga tabbas tasa ta kare. Abin da ya fara zuwa min tunanina lokacin da na ga wannan ‘dramar’ a tashar Al-Jazeera ita ce tsohuwar haddar da nake da ita, wato fadin Allah Madaukakin Sarki lokacin da ya ke magana kan masu ‘tuban kurege’ inda Yake cewa: “Tuba kuwa ba ta zama karbabbiya ba ga wadanda suke aikata munanan ayyuka har idan mutuwa ta zo wa dayansu, sannan ya ce: ‘Lalle ni na tuba yanzu. Haka kuma ba (za a karbi tubar) wadanda suke mutuwa alhali kuwa suna kafirai. Wadannan Mun yi musu tattalin wuta azaba mai radadi”. (Suratun Nisa’ 4:18) da na kara lalubo haddar kuma sai wannan ayar da Allah Madaukakin Sarki ke magana kan tubar Fir’auna lokacin da ya ga tabbas zai halaka, wato fadinSa cewa: “Kuma muka ketarar da Bani Isra’ila teku, sai Fir’auna da rundunarsa suka bisu bisa ga zalunci da ketare haddi, har a lokacin da nutsewa ta riske shi ya ce: ‘Na yi imani cewa, hakika babu abin bauta face Wannan da Bani Isra’ila suka yi imani da shi, kuma ni ina daga cikin musulmi”, daga nan sai Allah Ya ce masa: “Ashe! A yanzu! Alhali da can ka ki ka kuma kasance cikin masu barna? To a yau kam za mu tserar da jikinka domin ka zamanto aya ga wadanda za su biyo bayanka. Kuma lalle ne masu yawa daga mutane, hakika, gafalallu ne ga ayoyinMu” (Suratu Yunus 10:90-92).

Ni dai a ganina wannan aya ta dace da wasan kwaikwayon da Saddam ya yi kokarin shiryawa, kuma lalle bayyanar da gawarsa da aka yi (musamman lokacin da aka dauko ta cikin motar ‘a kori kura’ aka mika ta ga danginsa) za ta kasance aya ga kowa da kowa musamman wadanda duniya take kokarin ruda da kuma wadanda suka dauki Amurka uwargijiya koma bayan Allah da ManzonSa da muminai.