Taron Bincike Kan 'Holocaust' A Tehran (1):

________________________

A ranakun 11 zuwa 12 ga watan Disambar nan ne (2006) aka gudanar da wani taron kara wa juna sani na kasa da kasa kan batun kisan kiyashin da aka yi wa yahudawa (abin da ake ce ma holocaust) da ya janyo kace-nace a birnin Tehran da taken “Review of the Holocaust: Global Vision”. Taron dai ya samu halartar kimanin masana da masu bincike 300 daga kasashe 30 na duniya da nufin tattaunawa da musanyen ra’ayi kan kisan gillan da aka ce an yi wa yahudawa a yayin yakin duniya na biyu. Sakamakon irin kutsawa da tasirin da yahudawa (sahyoniya) suke da shi a kasashen yammaci, tattaunawa da musanyan ra’ayi kan wannan batu na ‘holocaust’ ya zamanto babban laifi da ba za a taba gafarta wa wanda ya aikata shi ba, don haka ne ma taron ya janyo hankulan duniya, wasu na Allah wadai, wasu kuma na maraba da hakan wasu kuma suna nuna ban mamakinsu kan irin jaruntakar da gwamnatin Ahmadinejad take da shi na shirya irin wannan taro kamar yadda wani daga cikin mahalarta taron ya bayyana wa shugaba Ahmadinejad din.

Batun shirya taron dai ya taso ne shekara guda da wani abu da ta wuce sakamakon tsananta kamu da hukumta masana da dama a Turai saboda dankara alamun tambaya da suka yi ga batun ‘holocaust’ din, inda shugaban Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewar wannan matsaya ta Turai ta saba wa ‘yancin fadin albarkacin baki da suke ikirari. Shugaban na Iran ya bayyana cewar masanan Turan suna da ‘yancin bincike kan batun ‘holocaust’ musamman ma saboda akwai alamun tambayoyi da dama kansa. Don haka ne ma ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar cewar za ta shirya taro kan ‘holocaust’ din don jin ra’ayin wadanda suka yarda da shi da ma wadanda ba su yar da shi, don a fahimci hakikanin lamarin.

Bayan yakin duniya na biyu, yahudawa sun yi da’awar cewar ‘yan Nazi bisa umurnin Hitler sun kashe yahudawa miliyan shida ta hanyar kona su da kuma amfani da iskar gas mai cutarwa. Tun daga wancan lokacin ya zuwa yanzu an rubuta makaloli, littafa da shirya fina-finai da nufin  tabbatar da ikirarin. Yahudawa sun yi amanna da cewa yada labarin ‘kashe yahuwa miliyan shida’ shi ma a irin wannan mawuyacin hali, zai daga hankulan al’umma da sanya tausayi yahudawa cikin zukatansu, su kuwa yahudawan sahyoniyan sai su yi amfani da wannan dama wajen cimma manufarsu ta mamaya da samun matsuguni, hakan kuwa shi ne ya haifar da haramtacciyar kasar Isra’ila a kasar Palastinu a 1948. A takaice dai babbar manufa ita ce samar da wata dama ga yahudawan sahyoniya wajen cimma manufarsu ta mamaya. Don haka yahudawan sahyoniya sun yi amfani da wannan batu na ‘holocaust’ da ‘akidar gaba da yahudawa’ (anti-semitism) a lokuta daban-daban don cimma manufarsu.

Rayar da batun ‘holocaust’ da tunasar da mutane irin ‘zaluncin da aka yi wa yahudawa’ lamari ne da ke da muhimmancin gaske ga yahudawan sahyoniya, don haka sanya alamun tambaya kan 'holocaust' ko da kuwa da nufin fitar da hakika ne, lamari ne da yahudawan da ‘yan koransu ba za su taba amincewa da shi ba. A kasashen yammaci, yahudawan sahyoniya sun sanya ‘yan siyasa da ‘yan jaridu, har ma da wasu daga cikin masana ko kuma ma mafiya yawansu cikin wani irin yanayi na tsoro da ba za su iya magana kan ‘holocaust’ ba. A kasashe irin su Jamus, Austria da Faransa, sanya alamar tambaya kan batun ‘holocaust’ ko da kuma da nufin bincike ne da gabatar da hujja, hukumcin hakan shi ne gidan yari. Alhali a irin wadannan kasashe, ba wai ma shakka ba hatta ma cin mutumcin tsarkaka abubuwan addini ba komai ba ne, face dai “ ‘yancin fadin albarkacin baki”. A takaice dai ana iya cin mutumcin Annabawan Allah da saukakkun littafa, babu wani laifin cikin hakan. A yayin ganawar da muka yi da shi a yayin wannan taro, shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya yi ishara da wannan batu inda yake cewa: “A halin yanzu ‘holocaust’ ya zamanto wani babban gunki ga manyan kasashen yammaci, a irin wadannan kasashe mutum yana iya sanya alamun tambaya kan Allah (Madaukakin Sarki) da Annabawan Allah, amma magana kan ‘holocaust’ kan lamari ne ba za a iya gafarta wa mutum kansa ba”.

A halin yanzu ‘holocaust’ ya zamanto wani mizani ko sikeli na auna kula da kiyaye ‘yancin fadin albarkacin baki da hakkokin bil’adama na kasashen yammaci. A matsayin misali wadannan kasashe na yammaci, a koda yaushe, sun kasance masu takurawa wa wadansu kasashe da sanya musu takunkumi saboda rashin kula da hakkokin bil’adama da ‘yancin fadin albarkacin baki. To amma su dai wadannan kasashe, wadanda a zahiri su ke ikirarin demokradiyya, ba su yarda a yi bincike da neman karin bayani kan wani lamari na tarihi (kisan gillan da aka ce an yi wa yahudawa) ba, da yana iya zama gaskiya ko kuma akasin haka. Hatta wannan taro na Tehran gwamnatocin Amurka da wasu na Turai sun yi Allah wadai da shi, sannan kuma sun ci gaba da takurawa wadanda suka halarci taron, takurawa ta shari’a da siyasa. Daga cikinsu har da Farfesa Robert Faurisson dan kasar Faransa, wanda a hakikanin gaskiya ya burge kowa a wajen wannan taro saboda irin karfin hujjojin da yake da su kan rashin ingancin ikirarin kisan kiyashin da aka yi wa yahudawan, akwai kuma John Bernhoff dan kasar Sweden da aka dakatar da shi daga aikinsa sakamakon halartar wannan taro da dai sauransu.

Ni dai a ganina jaruntar da mahalarta taron, musamman wadanda suka zo daga Turai, suka nuna wajen halartar taron ba ta gaza na wadanda suka shirya shi ba, saboda irin hatsarin da suka sa kansu ciki sakamakon halartar taron, duk da cewa su ma wadanda suka shirya taron ko kuma in ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran hakika ta nuna jaruntaka da ba ko wace kasa ce za ta iya yin haka ba in ba irin su Iran ba wacce ta ginu wajen kare wadanda ake zalunta. Ina iya tunawa shi kansa Farfesa Faurisson ya fadi wani abu mai ban mamaki a gidan shugaba Ahmadinejad (lokacin da muka je ganawa da shi) inda ya ce lokacin da shugaba Ahmadinejad ya bayyana ‘holocaust’ da cewa ‘soki burutsu’ ne ko kuma dai tatsuniyar gizo da koki ne, su kansu sun yi mamaki ashe akwai wani shugaban kasa da zai iya fadin haka, har ma yake cewa wani abokinsa (ya fadi sunansa amma na mance) ya aiko masa da sako yana tambayarsa shin ya ji abin da shugaban Iran kuwa ya fadi, har ma ya ci gaba da cewa ai shi kenan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kawo karshe, saboda girman da wannan magana take da shi a idanun kasashen Turai. Amma ina har ya zuwa yanzu dai tana nan daram dinta. Shi kansa Farfesa Faurisson din ma yana cewa wannan kalami na shugaba Ahmadinejad yana daga cikin manyan mu’ujizozin juyin juya halin Musulunci na Iran.

Ala kulli hal, ‘holocaust’ dai lamari ne da ke da tasirin gaske wajen makomar da dama daga cikin al’ummomin duniya musamman al’ummar Palastinu, ba don komai ba saboda sun kasance manyan wadanda batun ‘holocaust’ din ya fi cutarwa. Don haka ne tun da jimawa, wasu suke da ra’ayin lokaci ya yi da ya kamata a zauna a binciki hakikanin wannan batu, idan ya tabbata a tabbatar da shi, a kuma tausayawa wadanda aka cutar, in kuwa bai tabbata ba to a yi watsi da shi don a dainar cutar da wadanda ba su ci ba su sha ba, to amma an rasa daga ina za a fara, don haka ne Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki nauyin gudanar da wannan taro don binciko gaskiya. Sai dai abin da ke da kyau a fahimta shi ne cewa tun kafin taron da ma lokacin da ake yinsa jami’an Iran sun bayyana cewar manufar taron ba ita ce tabbatarwa ko kore faruwar ‘holocaust’ din ba kamar yadda ministan harkokin wajen Iran din Manuchehr Mottaki, a jawabin bude taron, ya bayyana cewar: “Manufar gudanar da taron ita ce share fage wajen bayyanar da ra’ayuyyuka daban-daban kan wani lamari na tarihi, mu ba muna son tabbatar da batun ‘holocaust’ ko kore shi ba ne”. A hakikanin gaskiya wannan taro, wata dama ce ga wadanda suka yarda da aikata ‘holocaust’ da wanda ba su yarda ba da su yi musanyan ra’ayi da hujjoji, cikin ‘yanci da walwala don duniya ta saurara. Kai ina ma iya tunawa a a lokacin ganawa da shi a ofishinsa, shugaba Ahmadinejad ya bayyana cewar idan ma da turawan sun gane ai wannan wata dama ce gare su na su yi kokari tabbatar da batun ‘holocaust’ din ka ga shi kenan duk duniya sai ta goya musu baya cewa an zalunci yahudawa, don zalunci ai zalunci ne ga kowa kuwa aka aikata shi, idan kuwa aka gagara tabbatar da shi to shi kenan sai a rufe wannan shafi kowa ma ya huta, kuma a daina cutar da jama’a don ba su yarda da shi ba.

A yayin wannan taro dai an gayyaci masana masu ra’ayi daban-daban kan ‘holocaust’ din wato masu cewa lalle an yi ‘holocaust’ da kuma wadanda suke ganin tatsuniya ce kawai aka shirya kuma kowa ya kawo hujjojinsa, don haka ne ma aka kafa kwamitin kwararru tsakanin masana, don su ci gaba da bincike kan hujjojin da aka gabatar. To sai dai abin da ke da muhimmanci a fahimta shi ne cewa abin da ya fi janyo hankulan kusan dukkanin masanan wanda kuma suka yi ‘ta’akidi’ kansa shi ne zaluntar al’ummar Palastinu da aka yi kuma ake ci gaba da yi ta hanyar fakewa da batun ‘holocaust’. Da dama daga cikin masana suna tambayar cewa ne, idan ma abin a yarda da abin da yahudawan suke fadi ne cewa an zalunce su, shin wani dalili ne ya sanya cewa Palastinawa ne za su biya bashin wannan ‘zalunci da aka yi wa yahudawan’, me ya sa za a mamaye musu kasa da ci gaba da zaluntarsu don an zalunci yahudawa alhali ba su ne suka zalunce sun ba? Shi ma shugaban kasar Iran, a yayin ganawa da shi da ma a wasu lokuta ya yi tambayar cewa me ya sa al’ummar Palastinu ne za su biya bashin danyen aikin da Hitler ya aikata?

A fili yake cewa yahudawan sahyoniya, suna so kuma ma sun yi amfani da batun ‘holocaust’ wajen zalunta al’ummar Palastinu kamar yadda daya daga cikin malaman yahudawan da suka zo wanda taro, wanda shi ya yi ma amanna da cewa an aikata ‘holocaust’ din mai suna Ahron Cohen ya bayyana cewar: “A gaskiya an aikata ‘holocaust’ amma bai kamata ayi amfani da shi ba wajen halalta danyen aikin da yahudawan sahyoniya suke aikatawa a Palastinu ba. Yahudawan sahyoniya so suke su fake da batun ‘holocaust’ don cutar da Palastinawa. Suna cewa suna fada da zaluncin Jamusawa, alhali kuwa suna aikata irin wannan danyen aiki a Palastinu”.

 

A biyo mu a kashi na biyu don ganin bangarorin da aka tabo a yayin wannan taro kan wannan da’awa ta yahudawa (holocaust).



Wanda Ya Rubuta: Muhammad Awwal Bauchi