Kafa Sabuwar Helkwatar Rundunar Sojin Amurka A Afirka (AFRICOM):
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Masana dai suna ganin hukumcin kafa sabon helkwatar rundunar sojin Amurka mai cin gashin kansa a nahiyar Afirka a matsayin daya daga cikin tsarin ma'aikatar tsaron Amurka da kuma muhimmancin da gwamnatin Bush take bai wa nahiyar Afirka wajen cimma manufofinta na tsaro tun bayan harin 11 ga watan Satumban da aka kai wa kasar. Wannan ba da muhimmanci ya ci gaba da fadaduwa sakamakon tunanin da ake da shi na cewa akwai yiyuwar kafuwar kungiyoyi masu amfani da makamai a wasu yankuna na nahiyar wanda hakan ya haifar da karuwar tsoma bakin Amurka a wadannan yankuna da kuma barkewar yaki a kasar Somaliya da kutsawar da sojojin kasar Ethiopia – bisa goyon bayan Amurka kai tsaye – cikin kasar Somaliyan don taimakon gwamnatin rikon kwaryar kasar wajen gamawa da dakarun kotunan Musulunci da suke rike da madafan mulki a kasar a watan Disamban da ta gabata. Ko shakka babu barkewar yaki a kasar Somaliya ya taimaka wajen sake ta da wannan batu na kafa sabon helkwatar rundunar sojin Amurka a Afirka da kuma kokarin gaggauta shi.

Batun ba da muhimmanci ga nahiyar Afirka da gwamnatin Amurkan musamman ma'aikatar tsaron kasar, bayan shekara da shekaru na yin watsi da batun sakamakon rashin nasarar da sojojin Amurkan suka fuskanta a Somaliya tsakanin shekarar 1992-1994 ya sake tasowa ne a shekara ta 2002 lokacin da Amurkan ta kafa sansanin soji a kasar Djibouti don sanya ido kan abubuwan da ke gudana a yankuna da ake kira 'Kuryar Afirka' (wato kasashen Somaliya, Ethiopia, Eritrea, Kenya, Djibouti da Sudan) da kuma na Gabashin nahiyar, kamar yadda kuma a wannan shekara ne dai ma'aikatar tsaron Amurka ta fitar da wani shiri da ta kira 'Pan-Sahel Initiative' don ba da horon aikin soji ga sojojin kasashen Mali, Mauritaniya, Chadi da Jamhuriyar Nijar, sannan daga baya kuma a shekara ta 2005 aka fadada shirin don ya hada da wasu kasashe goma na daban na yankin. Shi dai wannan shiri ya hada har da wani da suke kira Trans-Sahara Counter Terrorism Initiative (wato shirin fada da ta'addanci a yankin Sahara) inda suka ware kimanin dala miliyan 500 don abin da suka kira 'kawo karshen masu tsaurin ra'ayin addinin Musulunci da suke yankin da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda ta hanyar ba da makamai da horon soji ga dakarun kasashen yankin.

Baya ga aikin horon, dakarun Amurkan sun kasance cikin wasu hare-hare da aka kai kan abin da suke kira fada da ta'addanci a nahiyar da suka hada da shiga cikin tsare-tsare da kai hare-haren da kasashe hudu dake yankunan da ke kewaye da Hamada (wato kasashen Mali, Chad, Nijar da Aljeriya) suka kai kan 'yan kungiyar 'Jama'at al-Salafiyya lil da'awa wa al-Jihad' a watan Maris na 2004 da kuma harin da jiragen yakin Amurka suka kai kudancin Somaliya a watan Janairun 2007 ga yankunan da suka ce wai wasu 'yan kungiyar Al-Ka'ida suna boye a wajen.

To sai dai matsalar da Amurkan take fuskanta a Afirkan tun bayan kaddamar da shirin da ta kira 'fada da ta'addanci' a Afirka shi ne rashin helkwatar rundunar sojinta ta musamman kan Afirka cikin helkwatocin rundunonin soji da ma'aikatar tsaron Amurkan take da su a fadin duniya. Saboda an an raba nahiyar ne tsakanin helkwatocin sojin Amurkan guda uku. A matsayin misali kasar Masar da Gabashin Afirka suna karkashin kulawar helkwatar sojin ta tsakiya ne (Centcom), sauran kasashen nahiyar kuma suna bin helkwatar (kasashen) Turai (Eucom) ne in banda Madagascar da Mauritius wadanda suke bin helkwatar Pacific (Pacom), wannan rarraba da aka samu yana haifar da matsala wajen gudanar da ayyukan sojin Amurkan a Afirka.

Duk da cewa batun kafa helkwatar Afirka mai cin gashin kanta ya samo asali ne tun lokacin mulkin shugaban Amurka Bill Clinton, to sai dai ba a fara wani aiki wajen cimma hakan ba sai tsakiyar shekara ta 2006 a kokarin da Amurkawan suke yi na sake tsarin ma'aikatar tsaron kasar da aka fara lokacin tsohon sakataren tsaron Amurkan Donald Rumsfeld. A lokacin ne aka kafa kwamitin da zai yi dubi cikin yiyuwar kafa helkwatar, inda bayan binciken shugaba Bush ya ba da umurnin kafa ta a watan Disambar bara. Helkwatar dai za ta hada dukkanin kasashen nahiyar Afirkan ne in banda kasar Masar wacce za ta ci gaba da zaman karkashin kulawar helkwatar tsakiya.

Man Fetur Da Fada da Ta'addanci:

Abin tambaya a nan shi ne mece ce manufar kafa wannan helkwata?

Hukumcin kafa helkwatar sojin Amurka na Afirka yazo ne sakamakon wasu abubuwa da suke da alaka da manufa ta siyasar Amurka kan nahiyarmu ta Afirkan, wacce ta ginu bisa wasu abubuwa muhimmai guda biyu, su ne: lamunce samun man fetur da kuma abin da suka kira fada da ta'addanci, wanda da dama suke ganin za su shafi kungiyoyi ne da suka adawa da siyasar Amurka ko da kuwa a hakikanin gaskiya ba kungiyoyi ne na ta'addanci ba. Dukkan wadannan lamurra guda biyu suna da muhimmancin gaske ga mahukuntan Amurkan.

Dangane da batun ta'addanci kuwa, mahukuntan Amurkan suna ci gaba da sanya ido kan nahiyar Afirkan saboda suna ganin nahiyar ta zamanto wata tunga ta yaduwar ayyukan kungiyoyin da ake ganinsu a matsayin masu tsaurin ra'ayin addini da kuma masu adawa da bakar siyasar Amurkan da sauran kungiyoyi saboda dalilai irinsu talauci, ci gaba da raunin da gwamnatocin kasashen nahiyar suke fama da shi musamman a yankunan 'Kuryar Afirka' da kasashen da ke makwabtaka da Hamada. Hakan ne ya sanya sabbin mahukuntan Amurkan daukan matakin abin da suka kira 'kare kai' ta hanyar daukan matakan riga malam masallaci a bangarori daban-daban ciki kuwa har da matakin soji. Yana da kyau a san cewa irin farkawar Musulunci da al'ummar Afirka suke samu lamari ne da baya wa sabbin 'yan mazan jiyan Amurka dadi, duk kuwa da cewa a hakikanin gaskiya ba za a iya rufe ido kan kokarin da wasu kungiyoyi masu mummunar ra'ayi na addini da kafirta juna da suke kokarin samun gindin zama a nahiyar. Don haka akwai bukatar a dinga rarrabe su da sauran kungiyoyin Musulunci.

Ita dai wannan sabuwar helkwata ta Africa ana sa ran za ta gudanar da muhimman ayyuka guda uku ne. Na farko shi ne yin aiki wajen samun yardar jama'a ta hanyar ba da taimako jin kai ga al'umma saboda tunanin da suke da shi na cewa hakan zai ba su damar sauya tunanin al'umma da adawar da suke yi da su. Na biyu kuma shi ne horar da sojojin kasashen Afirkan don samun damar kasancewa tare da sojojin Amurka, sai kuma na uku shi ne zaman cikin shirin kai hare-haren soji kan kungiyoyin masu makamai da ke adawa kasantuwar Amurka a yankin.

Masana al'amurran yau da kullum dai suna ganin gwamnatin Amurkan tana so ne ta fadada abin da ake kira da 'samfurin Ethiopia na fada da ta'addanci' wato kutsawar sojin kasar Ethiopia kasar Somaliya, ya rage wa Amurkan kutsawa kai tsaye wajen yakar mabiya kotunan Musulunci na kasar inda ta takaita kawai da bai wa sojojin Ethiopian bayanai na sirri kan kungiyar. Don haka yaki a madadi shi ne shi ne abin da Amurkan take son yi a shirinta na abin da ta kira fada da ta'addanci a nahiyar Afirkan.

Amma dangane da abin da ya shafi man fetur kuwa, muhimmancin man fetur din Afirka ga Amurkan a fili yake musamman idan aka yi la'akari da karin bukatar man fetur da iskar gas da Amurkan take yi daga nahiyar Afirka. Idan dai ana iya tunawa tun shekaru biyar da suka wuce bukatar Amurkan ya kai kashi 15 cikin dari a halin yanzu kuma ya kai kashi 20 cikin dari sannan kuma ana hasashen cewa zuwa shekara ta 2015 adadin zai kai kashin 25-30 cikin dari.

Akwai dalilai da dama da suka sanya Amurka ba da gagarumin muhimmanci ga man fetur din Afirkan daya daga ciki shi ne barazanar da ke fuskantar man fetur din saboda dalilai na cikin gida da waje. A matsayin misali aikin tace man fetur a kasashen yammacin Afirka yana fuskantar barazanar rashin tsaro da tashin tashina na cikin gida a wadannan kasashe, babban misalin hakan shi ne abin da ke faruwa a yankin Niger-Delta na kasar Nigeria na irin hare-haren da 'yan tawaye suke kai wa matatun man da hakan yake barazanar da ayyukan tace mai a kasar. To sai babbar barazanar da ta fi wannan ga Amurkan ita ce irin gasa mai tsanani dake gudana tsakanin manyan kasashen duniya kan albarkatun man fetur na nahiyar Afirka, don kuwa a halin yanzu gasar ba wai ta takaita ne kawai tsakanin manyan kamfanonin man fetur na kasashen yammaci ba ne, a'a ga kuma kasar China ma wacce ta shigo da dukkan karfinta. A halin da ake ciki kasar ta zamanto kasa ta biyu a duniya bayan Amurka da tafi amfani da makamashi saboda irin gagarumin ci gaba cikin dan lokaci da ta yi a bangaren masana'antu da sauran bangarori na tattalin arziki, da hakan ya sanya ta kashe makudan kudade wajen fitar da man fetur a nahiyar Afirkan.

Wani abu kuma da ya sanya Amurka kara sanya ido kan man fetur din Afirkan, kamar yadda wasu suke gani, shi ne matsalar da take fuskanta a yankin Gabas ta tsakiya da irin kashin da manufofinta suke sha a yankin, wanda hakan barazana ce gare ta da kuma burin da take da shi na ci gaba da diban man fetur na bello badin a yankin, don haka take neman wajen fakewa ido rufe.

To sai dai tambayar da masu tambaya suke yi ita ce: Shin kafa helkwatar sojinta na Afirka mai cin gashin kai zai taimake ta a wannan gasa ta man fetur da ake yi?

A hakikanin gaskiya gasar albarkatun man fetur dake tsakanin Amurka da China da wuya ya koma rikici na soji alal akalla dai a halin yanzu, sai dai duk da hakan ba za a iya kore yiyuwar samuwar wata rawa da karfin soji zai iya takawa a wannan bangare ba saboda ko ba komai kafa helkwatar sojin a Afirka zai iya zama yakin farfaganda kuma wani lamari dake nuni da amfani da karfin tuwo wajen fuskantar China da sauran kasashe da kuma tabbatar musu cewa Amurkan ba za ta ci gaba da zuba ido kan kokarin da kasar Chinan take yi na mamaye lamurra a nahiyar ba.

Sai dai mafi muhimmanci cikin hakan, kamar yadda masana suke gani, shi ne samar da helkwatar sojin a kan kansa wani riga malam masallaci ne dangane da gasar da ake tsammani za tayi karfi kan nahiyar Afirkan tsakanin kasashen duniya wanda Amurkan tana ganin hakan a matsayin babbar barazana da manufofinta dake bukatar ta karfafa karfinta na soji don magance wannan barazana.

Ko shakka babu kafa helkwatar Afirka ta sojin Amurka  a halin yanzu tana ta alaka ta kut da kut da irin siyasar gwamnatin Amurka mai ci yanzu na amfani da siyasar 'bakin bindiga' wajen cimma manufarta musamman idan aka yi la'akari da cewa gwamnatocin da suka gabata ba su yi tunani aiwatar da wannan shiri ba hatta a lokacin yakin ruwan sanyi lokacin da nahiyar Afirkan ta zamanto daya daga cikin yankunan da kasashen yammaci da gabashi suke rikici da cin kafan juna a cikinta musamman yankunan 'Kuryar Afirka' da kudancin nahiyar, amma gwamnatocin lokacin ba su yi wani kokari wajen samar da helkwatar ba.

Matsalar da gwamnatin Amurkan take fuskanta a wannan shiri nata shi ne kasar da za ta zamanto mazaunin helkwatar. A daidai lokacin da wasu kasashe suka nuna aniyarsu ta amince da karban bakuntar sojojin Amurkan a kasarsu, kamar yadda jami'an ma'aikatar tsaron Amurkan suka bayyana, wasu kuma suna nuna damuwa da dar-dar dinsu kan hakan. Masu nuna dar-dar din suna ganin ita kanta nahiyar tana da nata matsalolin da suka yi mata katutu don haka ba a shirye suke su sake janyo wasu matsaloli ga kansu ba sakamakon yarda da kafa sabuwar helkwatar sojin Amurkan. Wadannan shugabanni suna kafa misali ne da wajajen da Amurkan ta tura sojojinta don abin da ta kira fada da ta'addanci inda ake samun karuwar ayyukan ta'addancin maimakon magance su, babban misalin hakan su ne kasashen Afghanistan da Iraki inda ayyukan ta'addanci suka zamanto ruwan dare gama duniya, da shigowar kungiyoyin ta'addanci wasu da sunan fada da kasantuwar Amurka a wajen wasu kuma su kansu Amurkawan suke zuwa da su don halalta ci gaba da zamansu. Don haka ne masu wannan ra'ayi suke ganin zuwan Amurkawan musamman da nufin fada da wadanda suke kira 'yan ta'adda zai iya haifar da wannan yanayi da ake fama da shi a Afghanistan da Iraki, wanda ko ba a fadi ba zai kallafawa kasashen yankin nauyin da ba za su iya dauka ba.