|
|
|
|
| |||
|
Daga: Muhammad Awwal Bauchi IRIB-Tehran - I.R.of Iran awwalubauchi@yahoo.com ________________________ Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Wasu ruwayoyi na tarihi sun bayyana cewar an haifi Salman al-Farisi ne a shekara ta 568 miladiyya ko kuma kusa da haka a wani gari na kasar Farisa da ake kira Jiyye da a halin yanzu yake kusa da garin Isfahan (a Iran). Asalin sunan da mahaifinsa ya sanya masa shi ne Rozeba, sai dai daga baya, bayan musuluntarsa Manzon Allah (s.a.w.a) ya sauya masa suna zuwa Salman, an ce a wasu lokuta a kan kira shi da Abu Abdullah. Mahaifinsa attajiri ne kuma mai fadi a ji a wannan gari da kewayensa, yana da mutumci sosai a idanuwan mutanen garin, sannan ga shi da gidaje, bayi da dabbabobi. Salman shi ne dansa kawai, don haka yake tsananin kaunarsa. A wancan lokacin mafi yawan al’ummar Farisa suna bin addinin bautan wuta ne, don haka cikin wannan addini ne Salman ma ya taso, inda mahaifinsa ya ware wasu malamai don koyar da shi akidu da koyarwar wannan addini, ta amma sakamakon irin hazakar da yake da ita ya zamanto ya sami ilmi mai yawan gaske sama da malaman da suke koyar da shi a daya daga cikin dakunan bautan da suke da su. A wancan lokacin babban abin alfahari ne ace mutum ya zamanto daya daga cikin fada-fada (malaman addini) kuma mai hidima wa daya daga cikin dakunan bautan wutan a kasar Farisan, hakan na kawo wa mutum daukaka da girmamawa. Don haka ne mahaifin Salman yayi kokarin ganin dansa ya zamanto daya daga cikin irin wadannan mutane tun yana dan shekara sha shida a duniya. Salman yayi shekaru uku yana aiki a dakin bautan wuta na Jiyye, to sai dai ba a jima ba sai ya fara kosawa da wannan aiki da malaman dake karantar da shi saboda kasantuwansu mutane masu karancin tunani da ilimi. A mafi yawan lokuta ba sa iya amsa tambayoyin da yake musu ko kuma su ba shi amsa maras gamsarwa. Don haka tun daga lokacin ya fara tunanin yadda zai sami wata mafita. Kwatsam sai ga wata dama ta zo masa, lokacin da mahaifinsa ya tura shi wani gari don ya wakilce shi a wani aiki mai muhimmanci da ya taso masa saboda ba zai iya tafiya da kansa ba sakamakon bakin da ya yi wadanda dole ne ya tsaya don ganawa da su. Da gari ya waye sai Salman ya kama hanya, bayan fitarsa wajen gari sai ya ci karo da wata hanya da ta rarrabu, bai san wacce zai dauka ba, don haka sai ya tsaya yana tunani mene ne abin yi. Yana cikin wannan tunani ne sai ya hango alamar wani haske, sai ya nufi wajen don ganin mene ne a wajen kuma su waye suke rayuwa a wajen. Ko da ya iso sai ya ga wasu mutane ne suke cikin wani daki suna ibada da wakoki. Bayan da suka gama sai wani daga cikinsu ya matso kusa da shi ya tambaye shi kan shi wane ne sannan kuma me yake nema. Nan take Salman ya gaya masa ko shi wane ne sannan kuma ya bukaci ya san me suke yi kuma wani addini suke bi. Sai ya kai shi wajen babban malaminsu wanda ya shaida masa cewa su mabiya addinin Kirista ne da suka fito daga kasar Siriya, inda yayi masa bayanin akidun addininsu, daga karshe dai ya samu nasarar janyo hankalin Salman da mai she shi Kirista. A can gida kuma mahaifinsa yana cikin damuwa sakamakon rashin dawowarsa, ko da mahaifinsa ya ganshi ya dawo sai ya rungume shi don farin ciki yana mai tambayarsa dalilin jinkirin da yayi wajen dawowa gida. Salman ya shaida masa cewa yana tare ne da wasu Kiristoci da ya gamu da su. Hankalin baban nasa ya tashi kwarai da gaske yana tambayarsa cewa yana fata dai ba su batar da shi ba. Nan take Salman ya shaida masa cewa lalle ya gamsu da abin da suke fadi kuma ma yana ganin addinin Kirista yafi addinin bautan wuta da suke bi. Hankalin mahaifin Salman ya kara tashi kwarai inda ya bukace shi da yayi watsi da wannan sabon addini da ya karba, yayin da ya ki yin hakan, sai ya sa aka ta dukansa kana aka tsare shi kwana da kwanaki ba tare da abinci ko ruwan sha ba. Daga cikin bayin baban Salman akwai wani guda da ake kira Mehran wanda yake tsananin kaunar Salman saboda shi yake kula da shi tun yana yaro. Irin wannan alaka da take tsakaninsu ne ta sanya Salman ya bukace shi da ya taimaka masa ya gudu daga inda ake tsare da shi da kuma hada shi da wadannan kiristoci na Siriya. Mehran ya amince da wannan bukata inda ya shirya masa hanyar da zai gudu da tafiya wajen Kiristocin. Lokacin da ya isa wajensu, su ma a nasu bangaren sun hada shi da wani ayari mai zuwa kasar Siriya da yi musu wasiccin da su ba wa Salman kulawa ta musamman. Bayan wasu kwanaki, Salman da ‘yan tawagarsa sun iso birnin Damaskus (babban birnin kasar Siriya), a wannan gari ma da sauran garuruwan da ya zauna ya ci gaba da karance-karance da neman ilimi lamarin da ya bashi damar tara dimbin ilimi da masaniya. Baya ga ilimin da yake da shi, Salman ya kasance mutum ne mai kyakkyawar siffa ga karfin jiki, ga shi kuma a daidai lokacin yana jin karfin samartaka. To sai dai a wannan karon ma ya sake shiga wata damuwar yana jin cewa lalle abin da yake kai ba shi ne hakikanin gaskiya ba, akwai gaskiya ta hakika da har yanzu bai isa gare ta ba. Lokacin da wannan tunani ya dame shi sosai sai ya mika komai ga Allah Madaukakin Sarki Yana mai addu’ar cewa Allah Ya nuna masa hakikanin gaskiya. Allah Mai karban, Salman bai san cewa ya kusa kai wa ga gaskiyar da yake bukata ba. Bayan da ya bar garinsu Salman ya zauna a kimanin garuruwa guda hudu ne, gari na karshe da ya zauna shi ne Ammuriya dake karkashin daular Rumawa. A nan ne a karon farko ya sami labarin bayyanar wani Annabi a garin Makka da yazo da sakon bautan Allah Shi kadai da yin watsi da bautan gumaka. Nan take Salman ya fara tunanin cewa watakila wannan haske da ya bayyana a Makka shi ne shiriyar da yake bukata. Don haka ya fara shirye-shiryen tafiya Makka don ganawa da wannan sabon Annabi don yayi masa wasu tambayoyi. A irin yawace-yawacen da yake yi sai ya samu labarin isowar wani ayari na matafiya garin Ammuriyan, sannan kuma ya fahimci cewa wadannan mutane ‘yan kasuwa ne da suke zuwa garin daga Yathrib (Madina) don kasuwancin dawaki. Bayan da ya nemi karin bayani daga wajensu sai suka bayyana masa cewar bayan sun sayar da dawakinsu su kan tafi garin Damaskus ne don su hadu da wani ayari su koma inda suka fito (Yathrib). Jin haka sai Salman ya bukaci shugaban ayarin ko zai amince masa ya shiga cikinsu su tafi zuwa Damaskus daga nan zuwa Yathrib, shi kuma ya saka musu da dan wani abin da yake da shi. Bayan wasu kwanaki na tafiya cikin wahalhalu, ayarin ya iso wani waje da ake kira Wadi –ul- Kura a yankin Hijaz, a nan sai jagoransu ya sanar da cewa za su yi zango na kwanaki uku. A wannan waje ne Salman ya yanke shawarar zai wuce garin Makka daga Yathrib, sai dai abin da bai sani ba shi ne wadannan abokan tafiyarsa suna shirin kulla masa makirci da ha'intarsa. Kamar yadda muka fadi a baya cewa Salman mutum ne mai kyakkyawar kira ga kuma karfi na jiki hakan ne ya sanya abokan tafiyar tasa kama shi da sayar da shi ga wasu yahudawa a matsayin bawa, duk kokarin da yayi na nuna musu cewa shi ba bawa ba ne ya ci tura saboda ba shi da wani dalili da zai tabbatar da hakan. Haka suka tafi suka barshi ya ci gaba da zama a matsayin bawa. Salman dai yayi kasuwa sosai a wannan waje sakamakon irin jikin da yake da shi don haka su ma wadanda suka saye shi suka sayar da shi ga wasu har dai ya fada hannun wani mutumin Yathrib wanda yake zuwa Wadi –ul-Kura don harkar kasuwanci. Ko da ya tafi da shi Yathrib, a can ma yayi farin jini inda ya dinga yawo daga wannan hannu zuwa wancan har lokacin da ya fada hannun wani bayahude mai kudin tsiya mai suna Uthman bn Ashhel. Uthman bn Ashhel ya fahimci cewa Salman ba mutum ne mai yawan magana ba amma a duk lokacin da ya yi magana sai ka ganta cike da hikima, don haka ya amfana da shi ba kawai ta wajen aikin karfi ba har ma ta wajen shawarwari, amma duk da irin wannan amfana da yake yi da shi mai gidan nasa bai barshi haka ba sai da ya dinga sanya shi ayyuka ba dare ba rana. Duk da irin wannan tsanani da Salman yake ciki amma hakan bai hana shi ci gaba da tunani da fatan saduwa da Ma’aiki (s.a.w.a) ba da kuma yin dukkan kokari wajen ganin ya cimma wannan manufa tasa. Wata rana Salman yana cikin aiki sai ya ji mai gidansa yana tattaunawa da wani mutum wanda yake bayyana masa cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi hijira zuwa garin Yathrib, nan take Salman ya fara tunanin yadda zai sami damar ganawa da wannan Annabi. Wata rana mai gidansa ya tafi wata harka wajen gari, don haka sai Salman yayi amfani da wannan dama wajen cimma burinsa, inda ya dauki dabinon da ya samu ya sanya shi cikin buhu ya nufi cikin gari don neman Annabi Muhammad (s.a.w.a) da ganawa da shi. A wancan lokacin Manzon Allah (s.a.w.a) yana zaune ne a gidan Abu Ayyub al-Ansari (r.a) a matsayin bakonsa. Ko da Salman ya iso sai ya bukaci a yi masa iso wajen Manzon Allah (s.a.w.a), inda aka kai shi wajensa a daidai lokacin kuwa yana tare da wasu daga cikin sahabbansa. Ko da suka yi ido biyu da Manzon Allah (s.a.w.a) nan take sai yaji zuciyarsa ta cika da kaunar wannan Annabi yana gaya wa kansa cewa lalle wannan mutumi ba makaryaci ba ne. Bayan sun gaisa sai ya bayyana wa Ma’aiki (s.a.w.a) manufar zuwansa. Shi kuwa Ma’aiki (s.a.w.a) ya bayyana masa sakon da yazo da shi wato Musulunci da kuma abin da ya kumsa. Bayan wani lokaci na tattaunawa nan take Salman ya karbi Musulunci, yayi imani da cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu bawansa ne kuma ManzonSa. Daga nan Manzon Allah (s.a.w.a) ya sake masa sunansa zuwa Salman, shi kuwa yayi na’am da wannan suna da nuna tsananin kaunarsa gare shi, kuma da hakan ne aka sanshi tsawon tarihi. Tun daga wannan lokaci Salman ya ci gaba da zuwa wajen Ma’aiki (s.a.w.a) a kai a kai. Da haka ne wannan doguwar tafiya ta Salman ta kawo karshe. Ya isa ga tafkin ruwan da yake son sha, ga fitilar da yake fatan za ta haskaka masa hanyarsa, ga tafarkin da zai amsa masa tambayoyin da yake da su da magance masa matsalolin da yake fama da su, baya ga samun darajar kasancewa daya daga cikin sahabban Ma’aikin Allah (s.a.w.a). Bisa la’akari da halin da Salman yake ciki na bauta, Manzon Allah (s.a.w.a) ya bukaci ya ‘yantar da shi daga wajen mai gidansa ta hanyar sayen Salman, sai dai mai gidan nasa ya ki amincewa da hakan yana mai cewa akwai yiyuwar wata rana Salman ya zamanto daga cikin sojojin Musulunci da za su yaki yahudawa, saboda tuni ya riga da ya san cewa Salman ya musulunta. To sai dai bayan wani lokaci, wato lokacin da musulmi suka yi karfi da korar manyan kabilun yahudawa daga Madina bayan karya yarjejeniyar da aka kulla da su a lokacin yakin Badar da Uhudu, mai gidan Salman ya amince da bukatar inda ya sanya kudin fansa ran Salman shi ne cewa dole ne ya shuka masa bishiyar dabino guda dari uku sannan kuma ya biya oza arba’in na zinare. Lokacin da Salman ya gabatar wa Manzon Allah (s.a.w.a) da wannan bukata ta mai gidansa, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya juya ga sahabbansa ya ce musu: “ku taimaki dan’uwanku”. Nan take Sahabbai suka mike suka hada wadannan bishiyoyi da bayahuden yake bukata, sannan Annabi (s.a.w.a) ya bukace su da su tona ramukan da za a shuka su, bayan da aka gama tona ramin sai Manzo (s) ya zo da kansa ya shuka bishiyar farko sannan sauran sahabbai suka biyo sahu. To an gama shuka bishiyoyi amma abu guda ya rage shi ne zinare, don haka har ya zuwa yanzu Salman yana a matsayin bawa. Bayan wasu ‘yan makonni sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya aike a kira masa Salman, ko da yazo sai ya sami Manzon Allah (s.a.w.a) yana zaune a kasa tare da sahabbansa, a gabansa kuwa ga wani kwano dauke da zinare, ya bukace shi da ya dauka ya kai wa mai gidansa a matsayin abin da ya rage na fansar ransa. Ta haka ne Musulunci ya ‘yantar da Salman daga bauta wa wanin Allah zuwa ga bautan Allah Shi kadai da kaunar Ma’aikinSa (s.a.w.a). Salman ya ci gaba da mika rayuwarsa gaba daya wajen hidima ga Ma’aikin Allah (s.a.w.a) da ba da kariya ga sabon sakon da ya zo da shi. Daya daga cikin gagarumar hidimar da Salman yayi wa Musulunci shi ne lokacin da kafiran Makka suka shirya makircin kawo hari birnin Madina da mamaye shi gaba daya. A wannan lokaci ne Salman ya ba wa Ma’aiki (s.a.w.a) shawarar a tona rami mai zurfin gaske a kewaye garin Madina da shi don hana makiyan shigowa. Bayan gama tonun ramin sahabbai sun yi farin ciki da jinjina wa Salman kowani bangare naso ya janyo shi zuwa ga bangarensa, hakan ne ma ya sanya wani daga cikin Muhajirai (mutanen Makka da suka yi hijira zuwa Madina) ya ce: “Salman daya ne daga cikinmu mu Muhajirai”, nan take sai wani Ba’ansare (mutumin Madina) ya yi caraf yace: ‘A’a Salmanu daya ne daga cikinmu, mu Ansarawa”. Haka dai aka ci gaba da kace nace tsakanin bangarorin biyu. Bayan wani lokaci sai ga Manzon Allah (s.a.w.a) ya iso, yayin da yaji su suna wannan musu, sai yayi murmushi ya kawo karshen musun da cewa: “Salmanu ba Muhajiri ba ne ba kuma Ba’ansare ba ne, Salman yana daga cikin(mu) Ahlulbaiti”. Wannan babban matsayi ne da Manzon Allah (s.a.w.a) bai taba ba wa wani mutum in ba Salman ba, wato Salmanu ya zamanto daga cikin Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a), zababbiyar zuriya daga wajen Allah Madaukakin Sarki. A tarihin Musulunci babu wani mutum da ya taba samun irin wannan gagarumin matsayi in ba Salman al-Farisi ba. Ko da kafiran Makka suka zo suka ga wannan rami sai hankalinsu ya tashi ba su san yadda za su yi ba. Suka tsaya suka yi cirko-cirko. To sai dai daya daga cikinsu wanda yake da jaruntaka sannan kuma da tsananin adawa da musulmi wato Amr bn Abdu Wudd ya lashi takobin sai ya tsallake ya je ya sami musulmi. Shi da wasu daga cikin mabiyansu su uku sun kusato wajen rami suna dubawa sai suka ga wani dutse a cikin wani bangare na rami da musulmi suka gagara fasa shi, don haka suka yi amfani da shi wajen tsallake ramin da shigowa inda musulmi suke. Salman al-Farisi ya kasance tare da Manzon Allah (s.a.w.a) har lokacin da Allah Ya yi masa (Annabi) rasuwa a lokacin (Salman) yana da shekaru 65 a duniya. Bayan rasuwar Ma’aiki (s.a.w.a), Salman ya koma wajen magajinsa na hakika Imam Ali (a.s) inda ya ci gaba da yi masa da’a da biyayya. Lokacin da Imam Ali (a.s) ya zama halifan musulmi, ya nada Salman a matsayin gwamnansa a garin Mada’in na kasar Iraki duk da cewa a lokacin tsufa ta kama shi, amma duk da haka ya kama hanyar Mada’in. A hanyarsa ta zuwa garin Mada’in din Salman ya rabar da kusan dukkan abin da ya mallaka don biyan bukatar marasa shi. To sai dai abin bakin cikin shi ne cewa bai jima a wannan gari ba, Allah Ya karbi ransa alhali yana da shekaru 88 a duniya kuma an bisne shi ne a wannan gari na Mada’in. Allah Ya karbi irin wannan hidima da Salman yayi wa Musulunci da Manzon Allah (s.a.w.a) da Ahlulbatinsa (a.s). |
||||