Sahabin Manzo, Ammar bn Yasir (R.A):
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

An haifi Ammar bn Yasir ne tsakanin shekara ta 53 da ta 57 kafin hijirar Ma'aiki, tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi. Mahaifinsa shi ne Yasir sannan mahaifiyarsa kuwa ita ce Summaya wadanda suka yi shahada tun farko-farkon Musulunci sakamakon azabar da kafirai suka yi musu saboda karbar kalman Shahada.

Ana kirga Ammar bn Yasir daga cikin musulman farko-farko da suka fuskanci takurawa da azabtarwa daga mushirikan Makka, sannan kuma daga cikin musuluman da suka yi hijira zuwa Madina. Ammar bn Yasir ya halacci yakukuwan da Manzon Allah (s) ya yi irinsu Badar da Khandaq, inda ya kashe wani adadi mai yawa na kafirai.

Bayan rasuwar Ma'aiki, ya kasance daga cikin Sahabban da suka yi kira zuwa ga mubaya'a wa Amirul Muminina Ali bn Abi Talib (a.s) a matsayin halifan Ma'aiki, don haka yana daga cikin wadanda suka taru a gidan Fatima al-Zahra (a.s) don nuna rashin amincewarsu da halifan da aka zaba a Sakifa.

Ammar na daga cikin na kurkusan da suka yi salla wa al-Zahra (a.s) bayan rasuwarta da kuma bisne ta a boye. Kamar yadda yana daga cikin mabiya Ali (a.s) na kurkusa wadanda suka mika masa dukkan rayuwarsu wajen kare shi da kuma tafarkin da yake kai.

Ammar bn Yasir yana daga cikin 'yan kalilan din da Allah da Manzonsa (s) da kuma Ahlulbaiti (a.s) suka yi musu kyakkyawar shaida kan irin matsayin daraja da imani mai girma da suke da shi.

A cikin Alkur'ani mai girma Allah Ya yi masa shaida da cewa zuciyarsa cike take da imani, wato lokacin da kafiran Makka suka tilasta masa fadin wasu kalmomi na batanci ga Ma'aikin Allah (s) da Musulunci bayan sun kashe mahaifansa (Yasir da Sumayyah), inda Allah Madaukaki Ya ke cewa: Sai dai wanda aka tilasta alhali zuciyarsa na cike da imani. (Suratun Nahl 16:106).

A wannan lokacin ma an ruwaito Manzon Allah (s) yana cewa: Ya Ammar! Idan sun dawo (idan sun sake tilasta maka) to ka fadi (abin da ka fadi a baya) don kuwa Allah Ya karbi uzurinka, kuma Yana umartanka da ka sake fadi (abin da ka fadi) idan suka sake dawo maka".

Akwai maganganu daban-daban na Ma'aikin Allah (s) kan Ammar bn Yasir da suke nuni da daukakan matsayinsa duniya da lahira.

Ga kadan daga cikinsu: