Fatima bint Hazam - Ummul Banin - Uwar Abul Fadhl al-Abbas (a.s):
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ita Fatima bint Hazam bn Khalid bn Rabi' ibn Amir al-Kalbi, ta fito daga cikin gidan ma'abuta daukaka da kyawawan dabi'u, don kuwa iyayenta suna daga cikin shugabannin larabawa madaukaka. Mahaifinta shi ne Hazam bn Khalid bn Rubai'. Ana mata lakabi da Ummul Banin (Uwar 'ya'ya), wanda shi ne ma aka fi kiranta da shi. Akwai maganganu biyu kan dalilin da ya sa ake kiranta da wannan suna. Na farko dai an ce ana kiranta da wannan suna ne don kwatanta ta da kakarta Laili bint Amr wacce take da 'ya'yaye biyar maza don haka ake kiranta da uwar 'ya'yaye. Na biyu kuma cewa aka yi ita ce ta bukaci Amirul Muminina Ali (wato mijinta kenan) da ya dinga kiranta da wannan suna saboda ba ta so ya kira ta da asalin sunanta wato Fatima, don kada hakan ya tayar wa su Hasan da Husain (a.s) hankali da kuma tunatar da su mahaifiyarsu Fatima al-Zahra 'yar Manzon Allah (a.s), don haka yake kiranta da wannan suna (Ummul Banin).

Fatima Ummul Banin ta tashi ne karkashin kulawar madaukakan mahaifanta da aka sansu da kyawawan dabi'u, don haka Allah Ya arzurta ta da kyawawan dabi'u, hangen nesa da sauran siffofi kyawawa.

Haka nan lokacin da ta girma ta kasance abin misali tsakanin mata a bangaren dabi'u na kwarai da ya sa ta kasance abin yabo da son barkan kowa.

Bayan rasuwar Fatima al-Zahra (a.s), Amirul Muminin Ali (a.s) ya bukaci ya sake yin aure don ci gaba da rayuwa, kamar yadda daman matarsa abin kaunarsa Fatima al-Zahra (a.s) ta yi masa wasicci da hakan. To sai lokacin da ya so yin auren ya so ya samu macen da ta fito daga gidan ma'abuta jaruntaka da kyawawan dabi'u, don ya samu 'ya'ya ma'abuta jaruntaka da sadaukarwa saboda aikin da ya so za su aikata nan gaba a madadinsa, don haka sai ya bukaci dan'uwansa Akil - wanda yake masani ne kan hali da yanayin larabawa - da ya zaba masa mace, ma'abuciya jarunta da dai wadannan siffofi da muka ambata a baya. Sai Akil ya ce masa:

"Ya dan'uwana! Me ya sa ba za ka nemi hannun auren Fatima bint Hazm ba, babu wadanda suka fi iyayenta jaruntaka cikin larabawa".

Don haka sai Akil, ya tafi gidansu Fatima (Ummul Banin) don shaida musu ya zo neman auren Fatima ne ga dan'uwansa Ali.

Wannan labari dai ya faranta ran iyayen Ummul Banin, saboda sun san irin matsayin Ali (a.s) da irin falalar da ya ke da ita, kuma za su sami falalar zama surukan dan'uwan Manzon Allah (s) don haka suka amince da wannan bukata ita ma kanta Fatima ta yi na'am da wannan bukata.

Bayan gudanar da dukkan abubuwan da ake bukata na aure, sai aka daura auren, amarya kuma ta tare a gidan mijinta (a.s)