Uwar Muminai Ummu Salamah (r.a):
Daga:
Muhammad Awwal Bauchi
IRIB-Tehran - I.R.of Iran
awwalubauchi@yahoo.com

________________________

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Uwar Muminai Ummu Salama, tana daga cikin matayen Manzon Allah (s) bayan Nana Khadijah (r.a) wacce kuma take da kyawawan dabi'u da daukaka masu yawa. Tun da jimawa an san iyayenta da karimci da kyawawan dabi'u hakan ne ma ya sanya ake kiran mahaifinta Abu Umayyah ibn al-Mughirah al-Makhzumi da sunan ma'abucin karimci ga abokan zamansa. To ita ma ta gaji irin wadannan halaye na mahaifinta na karimci, tausayi da biyayya ga na gaba.

Uwar Muminai Umm Salama tana daga cikin mutanen farko-farko da suka karbi Musulunci sannan suka yi hijira zuwa kasar Habasha da kuma Madina don kare imaninsu. A gidanta ne aka saukar wa Manzon Allah (s) Ayar Tsarkakewa (33:33) ga Ahlulbaiti (a.s).

Mijinta na farko shi ne Abu Salama ibn Abdul Asad wanda ya kasance abokin wasanta ne kuma yana daga cikin wadanda suka yi hijira zuwa Habashan don kare imaninsa sakamakon tsananin zalunci da azabtarwar da suke fuskanta. A can ne suka haifi 'yarsu da ake kira Salamah da dansu Umar wanda daga baya ya zamanto gwamnan Bahrain lokacin halifancin Imam Ali (a.s). Abu Salamah yayi shahada ne sakamakon rauni mai tsananin da ya samu a lokacin yakin Uhudu. An ce wata rana Umm Salama ta bukace shi da su yi alkawari wa junansu cewa idan daya daga cikinsu ya riga dayan rasuwa to wanda ya sauran ba zai sake aure ba. Mijin nata dai ya ki amincewa da hakan, maimakon hakan sai yayi mata addu'ar cewa: Ya Allah! Ka ba wa Umm Salama wani mijin da yafi ni bayan rasuwa ta".

Hakan kuwa ya faru, don bayan rasuwar tasa, Manzon Allah (s) ya tafi gidansu don yi mata ta'aziyya da kwantar mata da hankali, shi ma sai yayi mata addu'ar cewa: "Ya Allah! Ka fitar mata da damuwar da take ciki, ka saka mata sannan Ka zaba mata miji na gari da yafi tsohon mijinta".

Umm Salama mace ce ma'abuciya kyawawan dabi'u (kamar yadda muka ce a sama) ga ta da kyaun halitta don haka ne ma da dama daga cikin manyan mutane suka bukaci aurenta amma ta kiya. Har sai lokacin da Manzon Allah (s) ya nemi hakan nan take ta amince, kuma ta sami matsayi mai girman gaske cikin zuciyar Ma'aiki (s) bayan Nana Khadijah matarsa ta farko. A hakikanin gaskiya Umm Salama ta mika kanta gaba daya ga Ma'aiki (s) ta yadda a shirye take ta aikata duk wani abu don dai ta faranta masa rai, sannan a kuma a koda yaushe ta kasance mai tausaya masa a duk lokacin da ya shiga wani hali da ban tausayi. Hakan ne ma ya sanya ta kasancewa tare da shi a yakukuwa da tafiye-tafiyen da yayi irinsu Yakin Khandak, Bude birnin Makka, Yakin Hawazen da kuma hajjin ban kwana.

Uwar Muminai Umm Salama mace ce mai ilimi da hangen nesa, don haka Manzon Allah (s) ya kan saurare ta a duk lokacin da take ba shi shawara kan wani abu da ya taso. A matsayin misali a lokacin Sulhun Hudaibiyya lokacin da Ma'aiki (s) ya bukaci sahabbai da su aske gashinsu da yanka dabbobin da suka zo da su (hadaya) sannan kuma su koma Madina (kamar yadda dai aka cimma yarjejeniya tsakaninsa da kafiran Makka), da dama daga cikin sahabbai ba su aikata hakan ba. Lokacin da Umm Salama ta ga alamun bacin rai tattare da Ma'aiki (s) sai ta ba shi shawarar cewa ya tashi ya fara aikata hakan shi da kansa za su biyo bayansa. Hakan kuwa ya faru.

Har ila yau Uwar Muminai Umm Salama ta kasance mace ma'abuciya son sadaukarwa ga Musulunci, wato a shirye take ta aikata komai wajen kare Musulunci ko da kuwa ranta ne. An ruwaito cewa wata rana ta tafi wajen Ma'aiki (s) ta ce masa: Ya Manzon Allah! Maza sun sami falalar yin jihadi da tafiya fagen daga alhali mata kuwa ba su da wannan dama, don haka ba za su sami damar yin shahada ba. Lalle mun yi babban rashi".

Sai Manzon Allah (s) ya bayyana mata wasu daman kuma da mata suke da shi yana mai cewa: "Jihadin mace yana ga halayenta ga mijinta".

Bayan haka sai Mala'ika Jibril (a.s) ya sauko da wahayi daga Ubangiji da ke cewa:

﴿وَلاَ تَتَمَنَّوْاْ مَا فَضَّلَ اللّهُ بِهِ بَعْضَكُمْ عَلَى بَعْضٍ لِّلرِّجَالِ نَصِيبٌ مِّمَّا اكْتَسَبُواْ وَلِلنِّسَاء نَصِيبٌ مِّمَّا اكْتَسَبْنَ وَاسْأَلُواْ اللّهَ مِن فَضْلِهِ إِنَّ اللّهَ كَانَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمًا

"Kuma kada ku yi burin abin da Allah Ya fifita sashenku da shi a kan sashe; maza suna da rabo a kan abin da suka aikata, kuma mata suna da rabo daga abin da suka aikata. Ku roki Allah daga falalarSa. Lalle ne, Allah Ya kasance ga dukkan komai masani". (Suratun Nisa' 4:32)

Daga nan kuma sai aka saukar da ayar:

﴿إِنَّ الْمُسْلِمِينَ وَالْمُسْلِمَاتِ وَالْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ وَالْقَانِتِينَ وَالْقَانِتَاتِ وَالصَّادِقِينَ وَالصَّادِقَاتِ وَالصَّابِرِينَ وَالصَّابِرَاتِ وَالْخَاشِعِينَ وَالْخَاشِعَاتِ وَالْمُتَصَدِّقِينَ وَالْمُتَصَدِّقَاتِ وَالصَّائِمِينَ وَالصَّائِمَاتِ وَالْحَافِظِينَ فُرُوجَهُمْ وَالْحَافِظَاتِ وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيراً وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا

"Lalle, musulmi maza da musulmi mata da muminai maza da muminai mata, da masu tawali'u maza da masu tawali'u mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu hakuri maza da masu hakuri mata, da masu tsoron Allah maza da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata, da masu tsare farjojinsu maza da masu tsare farjojinsu mata, da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambaton Allah mata, Allah Yayi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma". (Suraul Ahzab 33:35)

Musulunci ya zamanto wata hanya da Uwar Muminai Umm Salama da kara kyautata irin kyawawan halayen da take da su. Hakika ta ba da himma wajen kara irin ilimin da take da shi da kuma irin wadannan dabi'u musamman bayan aurenta da Ma'aiki (s).

Bayan aurenta da Ma'aiki (s), Umm Salama ta ci gaba da yin iyakacin kokarinta wajen ganin ta dadada wa Ma'aiki (s), hakan ne ma ya sanya ta samun daukaka sama da sauran matan Manzon Allah (s). Ta kasance mai kaunar duk wani abin da Manzon Allah (s) yake kauna da kuma nesantar duk wani abin da ba ya so. Hakan ne ya sanya ta take girmama Nana Khadijah da bayyanar da irin falalolinta, take girmama Imam Ali (a.s) da kaunar Fatima al-Zahra (a.s), saboda Manzon Allah (s) ya kasance yana girmama su da kuma kaunarsu gaba daya.

Sakamakon kusancin da take da shi da Ma'aiki (s) da yadda take saurarensa cikin nitsuwa a duk lokacin da yake magana ya sanya ta zamantowa daga cikin ingantattun maruwaita hadisai da aka fi dogaro da maganganunsu. Ta ruwaito darurrrukan hadisai daga wajen Manzon Allah (s) da Zuriyarsa (a.s).

Irin wannan matsayi da gaskiya da take da shi ne ya sanya ta zamanto abin yarda da dogaron Manzon Allah (s) da Zuriyarsa (a.s), ta yadda sukan ba ta amana da kuma gaya mata sirrukansu. A matsayin misali wata rana Manzon Allah (s) ya sanar da ita abin da zai sami jikansa Imam Husain (a.s) a Karbala, sannan ya ba ta ajiyar wani sashi na kasar Karbala din yana ce mata: A duk lokacin da kika ga wannan kasar ta sauya zuwa jini to ki san cewa jikana Husain yayi shahada".

A ranar 10 ga watan Muharram, shekara ta 61 bayan hijirar Ma'aiki (s), tana kwance sai ta ga Ma'aiki (s) cikin mafarkin cikin yanayi na bacin rai duk jikinta kura yana ce mata: Na dawo ne daga Karbala wajen bisne gawawwakin shahidai". Ko da ta farka sai ta nufi wajen da wannan kasa take inda ta same ta ta sauya zuwa jini. A nan ne ta san cewa tabbas Imam Husain (a.s) yayi shahada. Don haka nan take ta  fara juyayi da zaman makoki.

Umm Salama ta kasance mai tsanani kauna da sadaukarwa ga Fatima al-Zahra ('yar Manzo) mijinta Imam Amirul Mumini Ali da 'ya'yansu Hasan da Husain (a.s) su kuma a nasu bangaren suna tsananin kaunarta da amicewa da ita kamar yadda za a iya gani da tabbatar da hakan cikin ayyuka da maganganunsu.

Bayan shekaru na biyayya da mika wuya ga Allah Madaukakin Sarki da ManzonSa (s) Uwar Muminai Umm Salama ta koma ga Mahiliccinta ne a shekara ta 62 bayan hijirar Ma'aiki (s) lokacin tana da shekaru 84 a duniya. An rufe ta a makabartar Baki'a. Ita ce matar Ma'aikin (s) ta karshe wajen barin duniya.