Addinin Musulunci

v    Musulunci shi ne addini mafifici kuma shi ne mafi tsarki a cikin dukkan addinan duniya.

v    Musulunci ya zo ne domin ‘yan Adam, ba Musulmai ko Iraniyawa kadai ba. An aiko Annabawa ga mutane ne, haka Annabin Musulunci an aiko shi ga dukkan mutane ne.

v    Musulunci ya zo domin gyara bil Adama ne.

v    Musulunci addinin gyaran mutum ne.

v    Abin da Musulunci ya damu da shi shi ne ginawa da tarbiyantar da mutum domin kuwa don hakan ya zo.

v    Musulunci yana fada da duk wani abin da zai mai da mutum maras amfani kuma abin kyama.

v    Musulunci addini ne da aka saukar don ya karfafa ko gina ‘yan’Adam.

v    Don haka, Musulunci mafita ce ga dukkan wani al’amari na duniyan nan da ma daya duniyar.

v    Tare da irin wannan makaranta ingantacciya kamar Musulunci, babu wani dalili da zai sa Iraniyawa za su koyi nau’in rayuwar yammaci ko gurguzu ba.

v    Idan aka musuluntar  da komai, za a samu tsarkakakkiyar al’umma.

v    Musulunci domin gyaran al’umma yake.

v    Dokokin Musulunci ingatattu, cikkakku da masu taimakawa ne.

v    Musulunci na ba da karfi a kan tunani da nazari da kiran mutum ya watsar da camfe-camfe da kangin masu ikon koma baya da rashin ‘yan adamtaka, don haka, ta yaya irin wannan imani ba zai zama daidai da ci gaba da yunkurin dan adam ba, wanda yana fitowa ne daga kwarewarsa ne?

v    Musulunci na a mataki na koli a ci gaba, haka kuma masanansa na addini.

v    Musulunci ya yarda da dukkan abubuwan ci gaba na zamani sai dai wadanda ke gurbata dabi’u da bata kyawawan ayyuka. Musulunci ya yi watsi da abubuwan da ke sabawa maslahar al’umma, amma kuma yana karfafa abubuwan da ke dacewa da dukkan bukatun al’umma.

v    Abubuwan da Musulunci ke inkarinsu su ne wadanda ke janyo matasammu zuwa fasadi.

v    Doka daya ce, Musulunci, ta hukumcin Allah kawai.

v    Muna imanin cewa akidar da ke iya shiryarwa da sa ci gaban al’umma ita ce kawai Musulunci. Kuma idan duniya na son fitowa daga duhun matsalolin da take ciki a yau, da kuma samun rayuwa ta ‘yan adamtaka, to wajibi ta shiga sahu guda da Musulunci.

v    Musulunci ya zo ne domin ceton dan adam.

v    Musulunci ya zo ne domin ci gaba, kuma musulunci na da ra’ayi mai kyau game da ci gaba.

v    Zaman Musulunci a abu shamili da kuma zama gama gari, zai sa duk wanda ya fahimce shi ya yarda da cewa: Musulunci ya wuce haddin tunanin mutum kuma ba zai iya zamowa abin da karfin kimiya ko kwakwalwar (ko basirar) mutum ke iya kirkirowa ba.

v    Musulunci ba mallakar wata kasa ce ba, bai san Baturke ko Bafarishe (Bairaniye) ko Balarabe ba ko Ba’ajame ba, Musulunci na kowa ne, abubuwa kuma irin su zuri’a, launin fata, kabila ko yare ba su da matsayi.

v    A Musulunci al’amarin tushe ko zuri’a ba  abin zance ne ba, Larabawa ko wadanda ba Larabawa ba da sauran kabilu ba abin  tattaunawa bane a Musulunci. Musulunci ya zo ne domin gina mutum da ilmintar da shi. Muhimmin abu a Musulunci shi ne tarbiyantar da mutum da kuma gina shi.

v    Musulunci ya zo ya hada kan dukkan al’ummomin duniya, Balarabe, Ba’ajame, Baturke ko Bafarishe dukkansu zuwa ga ginin  babbar al’umma daya, wato, al’ummar Musulunci, domin cewa wadanda ke neman danne kasashen musulmi da cibiyoyin Musulunci sun kasa yin haka ne sabili da kasaicin al’ummar da Musulunci ya gina wadda ta kumshi kabiloli daban-daban.

v    Abin da ya hado dukkan kungiyoyin kabiloli daban-daban a karkashin runfa guda shi ne kudurar Musulunci.  

v    Na sha fadin cewa zuri’a, harshe,kasanci, ko mazauni a bayan kasa ba muhimman abubuwa ba ne a Musulunci.

v    Dokar Musulunci ba ta ha’inci a tsakanin mutane.

v    Musulunci akidar mutanen da ke a tafarkin neman gaskiya da adalci ne; akidar wadanda ke neman ‘yanci da mulkin kai ne; kuma akidar masu fada da ‘yan mulkin mallaka ne.

v    Wajibi ne mu yi kokarin rusa bangunan jahilci da camfe-camfe ta yadda za mu sami daman isa ga wannan tsarkakakken addini na Annabi Muhammadu (s.a.w.a.).

v    Hakika shaidanu suna kokarin su rusa wannan addini na Musulunci.

v    A yau, Musulunci yana kalubalantar duk wani nau’i na kafirci.

v    Lalle, a halin yanzu babu wani karfi da zai iya fuskantar Musulunci.

v    Ku rike Musulunci a matsayin shugabanku kuma mai shiryar da ku sannan ku mika masa wuya.

v    Musulunci ya fi zama abin kauna bisa ga yadda muke tsammani.

v    Makarantar Musulunci, makaranta ce ta tsarkakarwa da gogewa.

v    Musulunci na daidaitar da abubuwan duniya ta hanyar da za su hadu da na lahira (addini).

v    Musulunci ya fadi komai, amma mai wuyan ya saura ga Musulmai.

v    Babbar matsalar Musulmai, ita ce rabuwarsu da Musulunci da Alkur’ani.

v    Idan al’ummomi za su fahimci Musulunci, to za su san cewa duk abin da suke nema suna iya samunsa a Musulunci.

v    Duk cutarwa da wannan duniya ta fuskanta an same shi sakamakon rashin fahimtar Musulunci daga wasu mutane.

v    Masu mummunar ra’ayi na Musulunci su ne wadanda ba su fahimci Musulunci ba.

v    Ina kira gare ku da kada ku juya wa Musulunci baya, kada ku juya wa malamai baya, domin wadannan wasu falaloli ne na Ubangiji, kada ku  bari su kubuce muku.

v    Hakika martabar Musulunci da malamai yana fuskantar barazana daga ‘yan waje.

v    Musulunci yana umurtan gwamnatoci da su zama masu hidima (ga mutane).

v    Musulunci ya kasance mai hidima ga marasa galihu.

v    Musulunci zai tabbatar da farin ciki da jin dadinku a nan duniya da kuma lahira.

v    Hakika Musulunci ya kawo mana komai.

v    Musulunci ya zo ne don ya ceto raunana.

v    Musulunci shi ne addinin ‘yanci da  walawa.

v    Musulunci ya yarda da neman abin duniya don kare mutumci.

v    Musulunci na samar da kwanciyar hankali kuma yana kiyaye hanyoyin cimma buri.

v    Dokokin Musulunci sun yi daidai da bukatun dan Adam kuma wadannan dokoki a fili suke.

v    A dukkan janibobi na siyasa, tattalin arziki, al’adu da taimakekkeniya, Musulunci yana da hanyar hakikanin ci gaban dan Adam.

v    Makarantar Musulunci ba ta allaku da madda ba, ita makaranta ce ta dabi’u masu kyau wadda ta yarda da abubuwan madda a karkashin Ahalak, dabi’u na gari da tsarkake zuciya.

v    Musulunci bai zama na ginin dabi’u masu kyau kawai ba, ko na abubuwan madda kawai ba, ya hada duka. Shi ne cewa, Musulunci da Alkur’ani mai girma sun zo ne domin bunkasa da gina mutum a dukkan nau’oin rayuwarsa.

v    Musulunci mulkin Uluhiya ne nau’i daya shine na siyasa, nau’i dayan kuwa na ginin dabi’u masu kyau ne.

v    Musulunci akida ne na ibada da siyasa; sannan ibada ko bauta suna cikin al’amurran siyasa da kuma nau’oinsa na ibada ya kunshi siyasa.

v    Manzon Allah (s.a.w.a.) ya assasa ginshikin siyasa a addini. Kuma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya assasar da hukumcin gwamnati.

v    Dokoki da fatawoyin siyasa na Musulunci sun fi na ibada yawa.

v    Nishadin siyasa wajibi ne na addini a Musulunci.

v    Da rantsuwa da Allah, Musulunci, a dukkansa siyasa ce.

v    Kiyaye hakkin mutane ra’ayi ne na Musulunci.

v    Addinin Musulunci siyasa ce ta kowace hanya, har a cikin ibada.

v    Musulunci yana da shirye-shirye a kan komai, da dukkan rayuka.

v    Musulunci ya  tsara hanyoyin wa dukkan rayuwar mutum daga lokacin haihuwarsa zuwa shigarsa cikin kabari.

v    Al’amurran zamantakewa da siyasa na mutum anfi ba su alfarma bisa ga na ibada a wurin lura da dokokin Musulunci.

v    Musulunci na da tsari na rayuwa da tsari na gwamnati.

v    Dokokin Musulunci suna sa ci gaba na koli, da tabbatar da ‘yanci, mulkin kai da bunkasa.

v    Kasar da ke aiwatar da dokokin Musulunc, da gaskiya, za ta zama kasa mafi ci gaba.

v    Shi kansa Musulunci, ya kasance daya daga cikin wadanda suka kawo ko kafa manyan hanyoyin ci gaba da kuma wayewa a duniya.

v    Musulunci da fadin Allahu Akbar ne suka kai ku ga cin nasara.

v    Musulunci ne ya iza ku kuma ya ba ku irin wannan karfi har kuka yi tsayuwar daka a gaban karfafan rundunonin Shaidan ba ku tsorata ba.

v    Ba da ‘yancin zartarwa ga wadanda ke da nufin yi wa Musulunci da jama’a makirci, ha’inci ne.