|
|
| |||
|
Annabawan Allah
v
Annabawa
sun zo ne domin sanya kudurorin da aka tanada zuwa na aiwatarwa da kuma su kai
dan’Adam zuwa ga ainihin dan’Adam na gaskiya.
v
Dukkan
kokarin Annabawa ya kadaita ne wajen kiran dan’Adam zuwa ga hanya madaidaiciya
(gaskiya) da sa shi ya bi tafarkinta.
v
An
aiko Annabawa ne domin su kubutar da
halayen mutane da zukatansu da ruhinsu daga dukkan duhu sannan su maye gurbinsu
da haske.
v
Annabawa
sun zo ne domin kiran mutane daga duhu zuwa ga haske.
v
Sakon
Annabawa ya kawo canje-canje na kimiya da irfani, sanin Allah a duniya ya sauya
sandararriyar falsafar kasar Girka (Greek) wadda su kansu Girkawa suka kago
wadda ta kasance mai muhimmanci har yanzu zuwa wata fahimta ta ilimin irfani da
kai wa ga hakika ta gaskiya irin ta manyan masana hakika.
v
Abin
da Annabawa suke bukata shi ne sauya dukkan al’amura na rayuwa da na halitta da
kuma mutum su dace da yardar Allah.
v
Albarkar
aiko Mafificin Annabawa albarka ce da tun da, kama daga farkon halitta zuwa
karshen lokaci, ba a samu ba kuma ba za a taba samun irin ta ba.
v
“Zillullah”
(wato inuwar Allah) shi ne Shugaban Manzanni wanda shi a kan kansa babu wani
abu daga gare shi, duk komai wahayi ne.
v
Tsira
da amincin Allah Mai girma su tabbata ga Annabi Isa dan Maryama (a.s), Ruhullah
Manzon Allah Mai girma wanda ya kasance yana tayar da matattu. Tsira da amincin
Allah su tabbata ga mahaifiyarsa tsarkakakkiya Maryama, wacce, ta hanyar hura
ruhin Allah, ta haifi wannan irin da mai albarka ga wadanda ke jin kishirwar
rahamar Allah.
v
(Jawabi
ga limaman Kirista) Domin samun yardar Allah da aikata abin da Isa (a.s) ya
umurta, ku kada kararrawar cocin ku domin kare Iraniyawa raunana da kuma yin
tir da zaluncin azzalumai.
v
Ainihin
aikin Annabawa shi ne magance son rai gwargwadon iko kuma su shiryar da zuciya.
v
Mu
masu neman abu mafi alheri ga al’umma ne; mu mabiya Annabawa ne wadanda sun zo
domin gyaran al’umma, sun zo ne domin ja-gorancin al’umma zuwa ga sa’ada.
v
Idan
da dukkan Anabawa za su hadu wuri guda, ba za su taba sabawa da juna ba.
v
Idan
dukkan Annabawa (a.s) za su zo a lokaci guda, ba za su taba samun sabani da
juna ba.
v
Annabawa
basu daukar takobi wa kowa sai kawai a kan wadanda takobin shi ne magani a gare
su, wadanda suke kawo fasadi a cikin al’umma.
v
Hikimar
Annabawa ita ce gallaza wa kafirai da makiya bil adama, da kuma rausasawa ga
junansu, wannan gallazawar ita kanta rahama ce.
v
Annabawa
sun kasance suna jin tausayin kafirai da munafukai da yin mamakin yadda suka
zama yadda suke. v
A
farkon kiransu, Annabawa sun fuskanci masu hannu da shunin al’umma ne, Annabi
Musa (a.s) ya fuskanci Fir’auna. Masu galihu su ne suka fi cancantar a fuskance
su don su shiryu.
|
||||