Imani Da Darajar Kyautata Dabi'u

v    Idan imani ya shiga  zuciya, ayyuka za su gyaru.

v    Imani da Allah haske ne, imani da Allah na kore dukkan duhu daga hanyar mumini.

v    Imani na nufin cewa zuciya ta fahimci kuma ta karbi abin da hankali ya fahimta. wadanda suke tare da Allah, kuma suke sane da Allah, suke imani da Allah, to Allah zai fitar da su daga dukkan duhu Ya kai su ga haske na hakika.

v    Ka sani cewa hakikanin ilimi da imani wanda ya ginu daga ilimi, haske ne.

v    Barazana da rashawa sukan damu wadanda ba su da imani ne.

v    Masu da’war imani suna da yawa, amma muminai kalilan ne.

v    Idan aka karfafa imanin mutane to za a iya yin dukkan abubuwa cikin sauki.

v    Kasancewa kadan a “adadi” ba shi da muhimmanci, mallakar imani mai karfi shi ne muhimmi.

v    Ma’aunin alheri shi ne cewa mutum ya zama mumini, kuma ya zama mai hakuri mai sanya wasu su yi dauriya, ya fadi gaskiya da sa wasu su fadi gaskiyar.

v    Ba zan iya yarda da cewa mutumin da ba ya da kyawawan dabi’u zai yi wa mutane hidima ba.

v    Ku yi kokarin karfafa kyawawan dabi’u a wannan al’ummar. Ta hanyar kyawawan dabi’u ne za ku iya kare mulkin kanku kuma ku kai ga matakan martabar kamala.

v    Darajar kyakkyawan dabi’u daraja ce ta har abada.

v    Dukkkan musibu daga raunin imani ne.

v    Daukaka tare da takawa take.

v    Cike gurbin hasarar abin duniya tafi cike gurbin kyawawan dābi’u sauki.

v    wadanda ke aiki saboda Allah ba su taba hasara, wadanda kuma suke aiki domin duniya su ne masu hasara, idan kuma ba su cimma masa ba, sun yi babban hasara kuma sun bata rayuwarsu a banza.

v    Mu masu sa tsammani ne a gurin Allah , mu ba masu debe tsammani ga Allah ba ne, kuma albarkacin sa tsammaninmu ga Allah za mu shawo kan dukkan matsaloli.

v    Ina da tabbacin cewa muddin wannan al’umma tana sa Allah a rai, to babu wani karfi da ke iya cutar da ita.

v    Idan al’ummarmu ta ci gaba da tafiya gaba saboda Allah da kuma samun yardar Manzon Allah (s.a.w.a.), dukkan manufofinta za su samu.

v    Kada ku yi tunanin cewa fadar “White House” ta Amirka da fadar :Kremlin” ta Rasha na rayuwa a cikin kwanciyar hankali ne, suna rayuwa ne cikin tsoro, wannan kuwa na faruwa ne domin su mabiya Shaidan ne kuma Shaidan ba zai bar mutum ya samu natsuwa ba.

v    Idan imani da Allah da kuma aiki dominSa ya shiga fannonin zamantakewa, siyasa da tattalin arziki da kuma sauran nishadodin mutum, za a shawo kan mafi rikirkicewar matsaloli a duniyar yau cikin sauki.