Sanin Allah Da Bauta

v    Allah ne hakikanin haske, dukkan wani abu koma bayanSa, duhu.

v    Dukkanmu daga Allah muke; dukkan halittun kasa da sama na Allah ne; kuma wadannan alamu ne  na samuwar Allah, kuma duk a zuwa gare shi makoma take.

v    Dukkan manufofin Annabawa sun hadu a kan kalma daya ne, ita ce kuwa: Sanin Allah (ko ilimin sanin Allah).

v    Ainihin manufar wahayi ita ce isar da ilmi.

v    Allah Ya albarkace mu da ni’imominSa, don haka wajibi ne mu sarrafar da abin da Ya ba mu a tafarkinSa.

v    Dukkammu  daga Allah muke kuma wajibi ne mu kasance a bautarSa.

v    Abin da ke saukakar da bala’oi shi ne cewa dukkan abubuwa masu gushewa ne. Dole ne dukkammu mu tafi, don haka ya fi kyau dukkammnu mu sadaukar da kammu a tafarkinSa.

v    Ka mai da hankali zuwa ga Allah domin zukata su mai da hankali zuwa gare ka.

v    Zahirin aiki ba shi ne ma’auni ba, a’a imanin mutum ga aiki shi ne ma’auni.

v    Dukkan kowane baligi (mukallafi) a bayan kasa na fuskanatar jarrabawa daga Allah (Ubangiji).

v    Mukami da matsayin da mutum ke da shi, da dukkan wani aiki da ya doru a kansa na a matsayin jarrabawa ce a gare shi.

v    Yardar Allah ita ce ma’auni a Musulunci, ba mutane ba. Muna kimanta mutane da gaskiya ba gaskiya da mutane ba. Ma’auni shi ne adalci da gaskiya.

v    Ya kamata mu yi amfani da ma’aunin Ubangiji Allah.

v    Ku farka Ya ku jama’a, Hukuma ki farka , Ku farka dukkanku. Dukkanku gaban Allah kuke, za a kira ku gobe ku ba da bayani a kan abubuwan da kuka aikata da wajibanku. Kada ku manta da jinin Shahidanmu, kuma kada ku yi fada domin matsayi ko mukami.

v    Halittun kasa da sama a gaban Allah su ke, kada ka aikata zunubi a gaban Allah. Kada ka yi fada domin abubuwa marasa tushe, masu gushewa a gabanka. Ka yi aiki domin Allah.

v    A yanzun nan, dukkanmu a karkashin jarabawa muke.

v    Mutum na iya boyewa sauran halittu abubuwa, amma dukkan abubuwa game da mu na hannun Allah, kuma zai mayar mana da ayyukammu.

v    Ka kira Allah Marinjayi, domin kuwa Insha Allahu, zai saukaka maka matsalolinka.

v    Dukkan abubuwan da suka wajaba a kanmu na addini tausasawar Allah ne, amma muna tsammanin cewa wani nauyi ne.

v    Dole ne dukkammu, mu zama  bayin Allah, kuma mu sani cewa komai daga gare Shi yake.

v    Mizanin bambance na Allah daga na Shaidan yana a dubin ainihin aiki amma ba wanda yayi aikin ba.

v    Sa Allah a zuci, hijira daga mutum kansa zuwa ga Allah (wadda ita ce mafi girman hijira), hijira daga son rai (ko kai) zuwa ga gaskiya, da kuma daga wannan duniyan zuwa ga duniya ta boye sun zagaye ka.

v    Bayan dogara ga Allah, ka dogara ga karfin kanka wanda shi kan sa na Allah ne.

v    Ina gaya muku cewa, kada ku ji tsoron kowa sai Allah, kuma kada ku dogara da kowa sai Shi.

v    Komawa ga wanin Allah ya kan gindaya shinge mai duhu ga mutum.

v    Rashin tuna Allah na kara gurbata  zuciya, kuma ya kan sa galabar son zuciya da Shaidan a kan mutum da kara fasadi a kullum. Ambato da tuna Allah na sa wa zuciya sakina da tsaftace ta da mayar da ita madubin ganin hasken Allah. Tana tsarkakar da zuci da kare mutum  daga kangin son rai.

v    Ku sani cewa: babu wutar da tafi fushin Allah zafi.

v    Kamar yadda yake wajibi a kan mu na kare kan mu, mu fitar da kan mu daga duhu zuwa ga haske, haka kuma yake wajibin mu ne mu kira wasu a kan haka.

v    Wajibi ne mu yi kira ba zuwa ga kan mu ba, ba zuwa ga duniya ba, a’a zuwa ga Allah kawai.

v    Ka yi karatun darasinka saboda Allah kawai.

v    Idan mutum ya yi yunkuri saboda son ransa kawai ba don Allah ba, ba zai je ko ina ba. Domin abin da ba na Allah ba, ba zai dore ba.

v    Allah samamme ne kada ka gafala da  Shi ! Allah Ya na nan, dukkan mu Ya na lura da mu.

v    Niyyarka ta zama saboda Allah, ka dauki mataki saboda Allah.

v    Dukkan duniya gurin Allah ne, dukkan abin da ke faruwa na faruwa ne a gurin Allah.

v    Ka zamo a sane koda yaushe cewa dukkan abin da ka aikata a gaban Allah yake, idanduna dake kiftawa a gabanSa suke, harsuna da ke magana a gabanSa suke, hannuwa da ke aiki a gabanSa suke, kuma gobe, dole ne mu bada amsa a kan su duka.

v    Dukkan mu a gaban Allah muke, kuma dukkan mu za mu mutu.

v    Ku isar wa zuciyarku cewa dukkan abin da kuka aikata a gaban Allah suke.

v    Ku sanar da zuciyarku wadda take lullubabbiya katangaggiya cewa dukkan halittar sammai da  kassai, tun daga kan mafi daukakar daukakakku har zuwa kan mafi kaskancin kaskantattu duka a gurin Ubangiji suke kuma dukkansu na karkashin kudurarSa mai rinjaye.

v    Ni’imomin Allah fitina da jarrabawa ce wa bayinSa.

v    Abin da ke fitar da mutum daga rarrawa shi ne ambaton Allah.

v    Yawancin koken da salihai waliyan Allah ke yi ya biyo ne saboda zafin radadin ciwon rabuwa da masoyi, da kuma abubuwan al’ajabi da yake aikatawa.

v    Dukkan martabobin da Annabawa da Salihan bayin Allah suka cimma, sun samu ne daga tsinke alakar zukatunsu zuwa ga duk wanin Allah, da kuma allakar da zukatansu ga Allah.

v    Samun izinin zuwa ga kafar saduwa  da Allah ya allaku ne ga tsinke dukkan alaka da wanin Allah, wanda abu ne da ba dukkan mutane ke cimma shi ba.

v    Sa kanka ka yi nitso cikin wannan kogi, kogin Ubangiji Allah, kogin Annabci, kogin Кur’ani mai girma.

v    Ka sani cewa, shukura domin rahamomin Allah na boye da na bayyane wani nau’i ne na bauta, kuma wajibi ne na ibada wanda ya wajaba akan kowa, daidai gwargwadon abin da mutum ke iyawa, koda yake, babu wani abin halitta da ke iya wa Allah godiyar da za ta kamance Shi.

v    Ba wani shakka cewa, soyayya wa Allah, bauta masa da tsarkake Shi na bukatar ilimi da sanin matsayinSa mai maras iyakan girma, kyakkyawan siffofinSa da girmanSa. Idan akwai rashin ilimi da sanin wadannan abubuwa, ba za a taba cimma bin wadannan manufofi ba.

v    Кa'idojin bauta su ne cewa babu wani karfi ko kudura abin bauta ma sai Allah, da kuma babu abin soyayya sai Allah da waliyansa.

v    Ainihin yabo na Allah ne kawai kuma bai zama na waninsa ba, koda kuwa yabo ga huren fulawa ko tuffaha kuka yaba  to yabo ne wa Allah.

v    Idan ayyukanka ba saboda Allah ba ne, kuma ka fita daga hadin kan musulunci, to lalle zaka zama saniyar ware.

v    Idan har manufarka Ubangiji ne sai kuma abin duniya ya biyo baya ya koma ya zama na Allah. Dukkan abin da kowannen mu ke da shi daga Allah ne, dole ne mu sarrafar da dukkan karfinmu dominSa.