Gyara Kai Da Fada Da Son Zuciya

v    Ba za mu iya gyaran kasarmu ba, matukar ba mu fara da gyaran kanmu ba.

v    Dole ne kowa ya fara da kansa, aikinsa da akidarsa da kuma dabi’unsa, ya yi su daidai da dokokin Musulunci, sannan bayan haka sai ya dauri aniyar gyaran wadansu.

v    Idan kuna son kasarku ta zama mai hakikanin mulkin kai, ta yadda wasu ba za su iya katsalandan a cikinta ba, to ku fara da kanku.

v    Ku gyara kanku, kasarku ita ma za ta gyaru.

v    Abin da ke da muhimmanci ga kowannenmu shi ne fara yaki da zuciya da bin son ranmu da kuma kin gamsuwa da cewa da wannan gyaran zahirin komai zai yi daidai, dole ne mu fara da zukatanmu da kwakwalenmu, kuma kullum mu yi kokari mu ga cewa ranarmu ta biyu ta fi ranar da ta gabata.

v    Ilimin kyautata dabi’u na Musulunci kamar su gyaran hali da tsarkake zuciya da shiga tafarkin kusanci ga Allah na daga muhimman fannonin ilimi na yaki da zuciya wadanda suka zamanto wajibi a kan makarantun addini su koyar da su gaba daya.

v    Ilimi da tsarkake zuciya ne suke sa mutum ya kai ga matsayin ‘yan Adamtaka.

v    Mantawa da amfanin kai ita ce share fagen kaiwa ga kamalar ‘yan Adamtak.

v    Mu yi nazarin ayyukanmu na duniya kafin a gabatar da su ga Imamuz Zaman (a.s) sa’an nan a isar da su ga Allah Madaukakin Sarki.

v    Ku yi aikin da in kuka dauke guzurinku daga nan za ku tashi da farar fuska a gaban Allah.

v    Yana kanmu mu tsarkake zukatanmu domin mu amfana da hasken Ubangiji da haske Alkur’ani.

v    Wajibi ne ku gyara kanku ta hanyar da za ku iya yunkurowa domin gyaran kai da nufin biyayya wa umurnin Allah.

v    Idan muka gyara kanmu, tabbatacce ne cewa, manufarmu ita ma za ta yadu a duniya.

v    Gyaran ruhi da tsarkake shi yana kan gaba kafin dukkan wani gyare-gyare. Jihadin ginin kasa na farawa ne da jihadin mutum a kan kansa.

v    Ku ginu! Wajibi ne mu gina kanmu! Ku yi kokarin fara jihadin ginin kai ta hanyar farawa da kanku, zai zamanto dukkan abin da ku ke yi, na Ubangiji ne.

v    Wajibi ne mu samu juyin juya hali a zukatanmu, ruhinmu ya canja dole ne ya sami juyin juya hali. Wajibi ne mu canza idan ya zuwa yanzu ruhinmu ya kasance a karkashin Shaidan da dagutu, to lalle ne mu canza.

v    A ruhin da ba a tsarkake ba, ilimi zai zama shingen duhu.

v    Wajibi ne na addini cewa idan a cikinmu ba ma jituwa da wasu, to a maganganunmu da ayyukanmu da wa’azinmu mu zama mun sabawa wa son ranmu a aikace.

v    Idan ba a tsarkake zuciya ba to ilimi ya fi jahilci cutarwa.

v    Magana ta fi ratsa zuciya da tasiri ne idan ta fito daga tsarkakakkiyar zuciya.

v    Idan mutum ya iya ya take “Ni” a karkashin kafarsa ya canza ta zuwa “Shi”, to zai iya gyara dukkan abubuwa su zama daidai.

v    A wani lokaci ilimin tauhudi na kai mutum wuta, kuma wani lokaci ilimin irfani ma ya kan kai mutum wutan, wani lokaci ilimin fikihu da ilimin kyautata dabi’u na kai mutum wuta! Ba wai da ilimi kawai ake gyara ba, tsarkake zuciya ake bukata.

v    Ilimin Tauhidi, shi ma idan ya ta’allaka da wanin Allah ne to yana daga shamakin duhu.

v    Allah Ya kiyaye, mutum ya shiga cikin al’umma kuma ya samu girma da karbuwa a cikin jama’a, kafin ya tsarkake zuciya daga bin son rai, domin babu shakka zai yi hasara ya halaka kansa.

v    Duk wanda ya dogara ga Allah zai ci nasara.

v    Idan kuka fita faga wannan duniya, wadda ita ce fagen ginin rayuwar lafiya, kun makara kuma ba za ku iya tsarkake rayukanku daga fasadi ba.

v    Ina tsoron cewa kada ta hanyar sauraren kalamominmu kuma saboda mu, su shiga aljanna mu kuma mu shiga wuta domin ba mu tsarkake kanmu ba.

v    Bukin idi na hakika shi ne lokacin da mutum ya samu yardar Allah, ya gyara kansa da zuciyarsa.

v   Jama’ar kasa, ko wata al’umma ba za ta iya cimma manufofinta ba har sai ta tsarkake da kuma gyara kanta.