|
|
| |||
|
Gabatarwa Wannan littafi ba wani abu ba ne illa digo daga
tabkin Alkausara daga rubuce-rubuce da kalmomin hikimar mashahurin mai ilmin
nan na dukkan lokuta, mai martaba Imam Khumaini (Allah Ya kara masa aminci).
Wannan tabki ne mai zankon gaske wanda yake
shi ne nufin masu jin kishirwa, matafiya a tafarkin Allah kuma shi ne
ainihin guzurinsu na ainihi, abin shan
wadanda zukatansu ke konewa, hasken hanya ga wadanda ke bin tafarkin juyinsa na
addinin Ubangiji. Wannan littafi ya kunshi zababbun jimloli daga
kalamomin Imam Khumaini (r.a) sakonninsa da ta’alifofinsa, wanda an shirya shi
ne a kashi hudu a karkashin Akida da Imani, ilmi, siyasa da zamantakewa. Domin
tabbatar da amana, a wuraren da cikon jimla na bukatar sa kalma ko harafi, an
tabbaka haka ta hanyar sa su a cikin da kuma inda an bukaci sauya kalma, an sa
kalmar asali a sun bada shaida cewa ba wani kalami ko rubutun alkalaminsa
wadanda bai yi imani ko aikata a cikin
zurfin zuci-yarsa ba. Imam Khumaini (Allah Ya kara masa aminci) ya karanci
kuma ya samu kwarewa tun a lokacin yarantarsa, a ilimin falsafa, irfani, fikihu
da usuli da albarkatunsu a marhala ko mataki na koli. Ya fito da wadannan
mabudan haske na Allah a cikin littafansa masu daraja kamar su Misbahul
Hidayat (Hasken Mai Jagora), Sirrus Salat (Asirin Salla), Aadabus
Salat (Ladubban Salla), Arba’una Hadis (Sharhin Hadisai Arba’in) da
kuma a cikin sauran littafansa na fikihu, Usulu da Akhlaki[1].
Imam Khumaini (r.a) ya kira al’umma da harshen Alkur’ani da sunna. Kalamominsa
masu sauki ne kuma sanannu ne da kuma tarshe da fadin gaskiya da tsarki. A bisa hakikanin gaskiya, wannan shi ne asirin
ainihin tasiri mai ban mamaki na kalamomin Imam da sakonsa, wadanda suka farkar
da dabi’ar mutane da harrakarwa da kuma dunguzasu zuwa ga tunkarar dukkan wani
abu komai hadarinsa. To, Alhamdu lillahi, shekara hudu bayan wafatin
wannan ruhi mai tsarki, muna ganin yadda tunaninsa da fikirorinsa masu daraja
suka zama asasin harkokin Musulunci da har ma wadanda ba na Musuluncin ba, da
suka taso ko ina a duniya. Kuma sun zama al’amurran da ba za a taba shafe su
ba, wadanda sun firgita shuwagabannin kafirai, wanda har ma su kansu sun yi
ikirari da hakan. Kuma yau, a shekara ta hudu daga kaurar wannan Imamun
Jarumai da kuma Sufaye, domin tunawa da wannan Imamin da hannuwansa masu
albarka wadanda tamkar sakamakon gaskiyar Wilaya da salihancin Imama ne, ya
amsa shakuwar zukatanmu, kuma wanda kalamominsa na ilhami sun…….ke a
Wannan littafi “Kalmomin Hikama Da Nasihohi” ya kunshi kalmomi na furuci da rubutu wadanda wannan Salihin Mutum ya ayyana, kafin kowane abu, shaida wa hakikanin inganci da gaskiyar tafarkinsa ta hanyar samuwarsa a fagen aiki da manufofinsa a aikace. Dukkan wadanda suka ga harkar wannan ruhi na daga Ubangiji, tun farkonsa har zuwa kai ga manufarsa, da kuma dukkan wadanda suka sadu da shi. [1] . Mai Martaba Imam Khumaini (r.a),
Baya ga wadannan littattafai da aka ambata a sama, ya rubuta manyan littattafa
da makaloli daban-daban kan fikhu, falsafa, irfani da kuma na akhlaki. A ‘yan
kwanakin baya-bayan nan ne Cibiyar Bincike da Kuma Wallafa Ayyukan Imam
Khumaini (r.a) ta buga littafin nan nasa na wakoki da aka sanya wa suna
“Diwanin Imam”. A halin yanzu muna da: laccocin wannan bawan Allah har guda
1026, sakonni guda 319, wasiku guda 203, hira guda 118 da kuma fatawoyi guda
197, wadanda an buga wadansunsu a cikin littattafa kamarsu Sahifatun Nur
(mujalladai 22) da kuma Kawthar (mujalladai 4)
|
||||