|
|
|
|
| |||
|
________________________
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai "Daga muminai akwai wadansu mazaje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah alkawari a kansa, a cikinsu akwai wanda ya biya bukatarsa, kuma daga cikinsu akwai wanda ke jira. Kuma ba su musanya ba, musanyawa".(Allah Yayi gaskiya) Cikin farin ciki da alfahari muna sanar da shahadar babban mujahidi kuma shugaba daga cikin shugabannin gwagwarmayar Musulunci ta Labanon. Bayan rayuwa dake cike da jihadi, sadaukarwa da gagarumin shaukin shahada da saduwa da masoya, dan'uwa kuma jagora Hajj Imad Mughniya (Hajj Ridhwan) ya yi shahada sakamakon ta'addancin yahudawan sahyoniya. Tun da jimawa yahudawan sahyoniya da manyan kasashen duniya ma'abuta girman kai suke neman wannan Jagora, Allah Ya yi masa rahama, tun sama da shekaru ashirin suke nemansa ruwa a jallo, har lokacin da Allah Ya zabe shi a matsayin shahidi a hannun makasan Annabawa, masu yada fasadi a bayan kasa wadanda sun riga da sun san cewa rikicinmu da su rikici ne na tsawon lokaci, sannan kuma jinin shahidan jagororinmu a koda yaushe ya kan kara wa gwagwarmayarmu daukaka da karfi ne kamar yadda ya faru da jagororinmu shahidai Sayyid Abbas Musawi da Sheikh Ragib al-Harb, amincin Allah Ya tabbata a gare su.
A daidai lokacin da muke girmama babban shahidinmu, mun dauki alkawari ga ruhinsa mai tsarki cewa za mu ci gaba da wannan tafarki nasa na jihadi har sai mu sami cikakkiyar nasara da yardar Allah.
Sannan muna isar da sakon farin cikinmu ga iyalansa da 'yan'uwansa mujahidai saboda wannan matsayi mai girma a wajen Allah da Ya samu, kamar yadda kuma muke mika sakon ta'aziyyarmu saboda rashin wannan babban kwamanda abin kauna.
|
||||