Sayyid Nasrallah: Jinin Hajj Imad Mughniya Zai Kawo Karshen H.K.Isra'ila:

________________________

Sayyid Hasan Nasrallah Yayin Da Yake Gabatar Da Jawabin

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar jinin Hajj Imad Mughniya zai kawo karshen haramtacciyar kasar Isra'ila ko shakka babu cikin hakan.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabin da aka watsa ta hanyar talabijin a wajen jana'izar daya daga cikin manyan kwamandojin sojin sojin kungiyar Hizbullah Shahid Hajj Imad Mughniya (Hajj Ridhwan) wanda yayi shahada sakamakon harin ta'addancin da haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai masa a birnin Damaskus na kasar Siriya yana mai cewa: Idan har jinin Sheikh Rajib al-Harb (shugaban kungiyar Hizbullah din da yayi shahada) da suka zubar ya fitar da su daga mafi yawa daga cikin yankunan kasar Labanon da suka mamaye, Idan jinin Sayyid Abbas Musawi (shi ma shugaban Hizbullah din ne da yayi shahada) da suka zubar ya fitar da su daga kan iyakan da suka mamaye in banda gonakin Shab'a, to lalle jinin Imad Mughniya zai kawar da su daga rayuwa, insha Allah.

Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana shahid Imad Mughniya a matsayin daya daga cikin dakarun da ba a san da su ba wadanda suka ba da dukkanin rayuwarsu wajen kare manufar al'umma.

Sayyid Hasan Nasrullah ya bayyana cewar yahudawan sahyoniya suna ganin sun yi nasara sakamakon kasha Hajj Imad Mughniya to amma mu muna ganin hakan a matsayin wata babbar bushara ce ga gagarumar nasarar da za a samu nan gaba, yana mai cewa: wajibi ne daga yau (wato ranar shahadar shahid Imad Mughniya) mu fara kirga kwanakin faduwar (haramtacciyar) gwamnatin Isra'ila.

Sayyid Nasrallah ya ja kunnen yahudawan da cewa kada su dauki wannan magana tasa da sauki, su yi tuntuni sosai cikinta yana mai kara tabbatar musu da maganar da Bin Goriyon mutumin da ya assasa haramtacciyar kasar Isra'ilan wanda ya ce haramtacciyar kasar za ta fadi kasa warwas a duk lokacin da ta fuskanci rashin nasara a yakin da ta yi.

Yayin da yake mayar da martini ga masu tunanin cewa kungiyar tasa za ta yi raunin gaske sakamakon kisan gillan da aka yi wa Shahid Imad Mughniya, shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar: Ina so in sanar da masoya da abokan gaba cewa babu wani rauni da aka samu cikin kungiyar Hizbullah, babu shakka 'yan'uwan (shahid) Imad za su ci gaba da tafarkinsa da jihadinsa. Jinin Hajj Ridhwan ya kara mana karfi da tsayin daka da hadin kai ne wajen ci gaba da wannan tafarki.

Sayyid Hasan Nasrallah ya kara da cewa: Hajj Imad shi da 'yan'uwansa sun gama dukkan shirin da ya kamata su yi babu abin da ya rage face dan abu kadan, don haka Sayyid Hasan yace: a halin yanzu kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana cikin dukkanin shirin da take bukata wajen fuskantar duk wani wuce haddi daga wajen haramtacciyar kasar Isra'ila.

Yayin da ya koma kan kisan gillan da yahudawan sahyoniyan suka yi wa shahid Imad Mughniya a kasar Siriya, Sayyid Hasan Nasrullah ya bayyana cewar tun da dai yahudawan sahoyoniyan sun zabi a fadada rikicin da ke gudana tsakaninsu zuwa wajen kasashen biyu to dakarun Hizbullah a shirye suke shige ka fasa.