|
|
|
|
| |||
|
(Rahoton Tashar Al-Manar) ________________________
Mujahid Shahid Imad Mughniya sabon shahidin kasar Labanon, yayi shahada ne sakamakon ayyukan ta'addancin yahudawan sahyoniya bayan Sheikh Ragib Harb da Sayyid Abbas Musawi da Shahidai Sa'id Harb, Abu Ali Ridha Yasin, da Abu Hasan Salama, Ali Husain Salih da Galib Awali. A yayin da yake gabatar da jawabi wajen taron juyayin shahadar Shahid al-Mujahid Galib Awali a ranar 19/7/2004 a dakin taro na Sayyidush Shu'ada', shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrullah ya bayyana cewar: "A yau Shahid ya shiga cikin jerin jagorori shahidai da jaruman mujahidai masu neman shahada, wadanda suka tsara mana tafarkinmu da jininsu mai tsarki don su zamanto mana mila-milan kan hanya masu haske da suka haskaka mana tafarkinmu, sun bar mana babban misali sannan kuma suka 'yanto mana da yankunanmu, sannan kuma suka ci gaba da kare mana kasarmu da taimakon 'yan gwagwarmayar Palastinu, har yanzu kuma suna ci gaba da rike tuta. Wannan tuta da muka yi wa Allah alkawari gaba daya da ita cewa ba za ta taba faduwa a kasa ba, za mu ci gaba da rike ta daga hannu zuwa hannu, daga kafada zuwa kafada har mun daga ta a kan duwatsunmu sannan kuma a kan kubbar masallacin Al-Aqsanmu sannan kuma sai mun tabbatar ba wani dan mamaya a dukkanin kasarmu Labanon da Palastinu da sauran kasashen Larabawa da na musulmi baki daya". Don haka wannan tuta da za a ci gaba da riko da ita daga hannu zuwa hannu daga kafada zuwa kafada, a shekarun 1980 tana hannun Shehin Shahidan gwagwarmayar Musulunci Sheikh Rajib al-Harb ne, da ita ne aka dau matsayin 'gaisawa da yahudawa alama ce ta yarda da su' sannan kuma aka ruda sahyoniyawa makiya. Lokacin da 'yan mamaya suka gaza wajen rufe sautinsa bayan da suka sace shi sai suka kashe shi a ranar 16 ga watan Fabrairu a daren juma'ar shekarar 1984, sai jininsa mai tsarki da ya zuba ya share (mana) tafarkin jihadi da gwagwarmaya. A irin wannan rana ta shahadarsa a shekarar 1992 Shehin Shahidan gwagwarmayar Musulunci (Sheikh Rajib al-Harb) ya mika tutar shahada ga shugaban kungiyar Hizbullah (na lokacin) Sayyid Abbas Musawi tutar shahada hakan kuwa a kusa da kauyen Jabshit ne jin kadan bayan halartar taron tunawa da shekaru takwas da shahadar Sheikh Rajib al-Harb da aka gudanar a kauyen Jabshit din ne sakamakon ruwan mamakai masu linzami da jiragen yakin makiya yahudawan sahyoniya suka yi wa motarsa ne inda yayi shahada tare da matarsa da dan karamin dansa Husain alhali wasiyyarsa ita ce 'ku ci gaba da riko da tafarkin gwagwarmaya ne'. Yahudawan sahyoniya makiya sun ci gaba da wannan aikin ta'addanci nasu inda suka kashe Mujahid Abu Ali Ridha Yasin daya daga cikin jagororin kungiyar Hizbullah a watan Maris na shekarar 1995, inda nan take aka mayar musu da martani da kai hare-hare kan matsugunan yahudawa. Bayan watanni takwas kuma suka kashe mujahid Sa'id Harb ta hanyar sanya bomb cikin motarsa a nan ma dai kungiyar Hizbullah ba tayi wata wata ba ta mayar da martani da kai wasu hare-hare da harba makamai masu linzami zuwa matsugunan yahudawa a daidai wannan ranar. A watan Agustan shekarar 1999 haramtacciyar kasar Isra'ila ta sake kashe wani jigo na kungiyar gwagwarmayar Musuluncin (Hizbullah) wato Ali Hasan Dib Abu Hasan Salama ta hanyar tayar da bomb a hanyarsa sun yi hakan ne ta hanyar amfani da wani dan amshin shatansu mai suna Mahmud Rafi' wanda yana da hannu kuma wajen kisan gillan da suka yi wa wani jigo cikin Hizbullah din Shahid Mujahid Ali Husain Salih bayan da suka tayar da bomb din da suka sa cikin motarsa da ke tsaye a kofar gidansa a watan Agustan 2003. Bayan watanni goma sha daya kuma sun sake kashe Mujahid Galib Muhammad Awali shi ma ta sanyar sanya bomb cikin motarsa da tayar da shi daga nesa a yankin Mu'awwiz dake kudancin birnin Beirut.
|
||||