|
|
|
|
| |||
|
________________________
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bakin mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sayyid Muhammad Ali Husaini ta yi kakkausar suka da Allah wadai da kisan gillan da aka yi wa Shahid Hajj Imad Mughniya daya daga cikin manyan kwamandojin soji na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon yana mai bayyana hakan a matsayin babbar alamar ta'addancin kasa da kasa da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi. Har ila yau yayin yayin da yake magana kan wannan danyen aiki, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ya sake jaddada halalcin gwagwarmaya wajen fitar da 'yan mamaya a duk inda suka mamaye yana mai kiran kungiyoyin kasa da kasa da su dau matakan da suka dace wajen hana haramtacciyar kasar ci gaba da aikata irin wannan danyen aiki wanda ya ce a fili ya saba wa dokokin kasa da kasa.
Sayyid Muhammad Ali Husaini ya kara da cewa: "Babu shakka tarihin gwagwarmayar Mujahid Shahid Imad Mughniya wanda ya gudanar da rayuwarsa wajen jihadi da yakan 'yan mamaya wani sabon shafi ne na tarihin gwagwarmayar al'umma wajen yakan yahudawan sahyoniya 'yan mamaya. Ko shakka babu al'umma ba za su taba mantawa da wannan jarumin shahidi ba. Daga karshe kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran din ya mika sakon ta'aziyya da alfahari ga iyalan Shahid Mughniya da 'yan'uwansa da al'ummar Labanon baki daya musamman 'yan gwagwarmayar kasar.
|
||||