Allamah Fadhlullah Ya Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addanci Kan Mughniya:

________________________

Allamah Muhammad Husain Fadhlullah

Sakamakon shahadar babban mujahidi Shahid Hajj Imad Mughniya, Allamah Sayyid Muhammad Husain Fadhlullah ya fitar da wani bayani inda a ciki ya jinjina wa shugaba kuma babban dan gwagwarmaya Alhajj Imad Mughniya, Allah Yayi masa rahama.

A cikin wannan bayani, Allamah Sayyid Muhammad Husain Fadhlullah ya bayyana cewar:

"Hakika tafarkin jihadi da gwagwarmayar Musulunci na kasar Labanon, wacce ta zamanto babbar barazana ga gwamnatin yahudawan sahyoniya da sauran kasashen duniya ma'abuta girman kai da manufarsu a wannan yanki (Gabas ta tsakiya), sannan kuma wacce ta samu nasarar wayar da kan al'ummar musulmi da larabawa da sauran al'ummomin masoya 'yanci na duniya, wacce kuma ta zamanto abin karfafa gwuiwa ga gwagwarmayar Intifada Palastinawa a yankunan da aka mamaye, hakika wannan tafarki da dukkan abin da ta kumsa na Musulunci, larabci da dan'Adamtaka ta rasa wani rukuni daga cikin rukunanta na asasi kuma jarumi daga cikin jarumanta sakamakon shahadar babban mujahidi Alhajj Imad Mughniya (Allah Ya yi masa rahama) wanda ya kasance babbar alama ta mujahidai da suka yi nasara kan yahudawan sahyoniya makiya a shekarun 2000 da 2006".
Shahid Imad Mughniya

Allamah Sayyid Fadhlullah ya ci gaba da cewa: "Tafarkin wadannan al'ummomi wadanda suka rayu cikin daukaka ta Musulunci da suka samo ta daga tafarkin musulman farko a Badar, Ahzab, Khaibar da Ashura, sannan kuma suka rayuwa karkashin kulawa ta Musulunci wanda ke nuna damuwa ga matsalolin musulmi dukkansu, babu makawa za su ci gaba da rayuwa cikin daukaka hatta cikin mafi tsananin yanayi da babbar kalubale. Wannan tafarki dai shi ne ya riki mafi yawa daga cikin shahidai hatta cikin jagorori irin su Sayyid Abbas Musawi da Sheikh Ragib al-Harb wadanda muke cikin ranakun tunawa da shahadarsu".

Allamah Fadhlullah ya rufe sakon nasa da cewa: "A daidai lokacin da muke fuskantar wannan babban rashi a tafarki jihadi, yana da kyau mu ba da himma wajen fuskantar fagen gwagwarmaya da yakan 'yan mamaya don kara kaimi wajen fuskantar makiya, da tsayin daka wajen fuskantar duk wani kalubale da riko hannu bibbiyu ga tafarkin jihadin Musulunci wanda ke kokarin motsa al'umma daga musibar rashin nasara zuwa ga nasara da karin imani kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya ke cewa: "Wadanda mutane suak ce musu:'Lalle ne, mutane sun tara (rundunoni) saboda ku, don haka ku ji tsoronsu. Sai (wannan maganar) ta kara musu imani, kuma suka ce 'Allah Ya ishe mu, kuma madalla da wakili Shi". (Allah Ya yi gaskiya)