|
|
|
|
| |||
|
________________________
Kungiyar Amal ta kasar Labanon, cikin wani bayani da ta fitar, ta yi Allah wadai da kisan gillan da aka yi wa daya daga cikin manyan mujahidan fada da yahudawan sahyoniya da manufarsu ta mamaya Shahid Hajj Imad Mughniya (Allah Ya yi masa rahama). A cikin bayanin nata kungiyar Amal ta bayyana cewar: Kungiyar 'Amal' yayin da take mika sakon juyayinta ga mai girma shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah da sauran dakarun kungiyar gwagwarmayar Musulunci, har ila yau kuma tana jinjinawa wannan babban mujahidi wanda yana daga cikin mutanen da suka assasa harkar gwagwarmayar adawa da mamayan yahudawan sahyoniya a kudancin Labanon kuma daya daga cikin wadanda suka samar da gagarumar nasarar da gwagwarmayar al'ummarmu ta samu wajen fuskantar 'yan mamaya da nasarorin da aka samu yayin yakin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar kan kasar Labanon wanda na karshensa shi ne yakin shekara ta 2006".
Kungiyar 'Amal' cikin wannan bayani nata ta ci gaba da cewa: "Kungiyar 'Amal' tana kiran al'ummar Labanon da su hada kansu waje guda wajen fuskantar babbar makiyar kasar Labanon haramtacciyar kasar Labanon wadda ake zargi da aikata wannan mummunan aiki da kuma riko da nauyin da ke kansu musamman a irin halin da kasarmu take ciki sakamakon makircin makiya". Shi ma a nasa bangaren mai ba da shawarar kan harkokin siyasa ga shugaban majalisar kasar Labanon Nabi Berri wato Ali Hasan Khalil, cikin wata tattaunawa da tashar talabijin din Al-Manar mallakan kungiyar Hizbullah ta yi da shi, ya yi Allah wadai da wannan danyen aiki na ta'addanci yana mai cewa rashin Shahid Imad Mughniya babbar hasara ce ga al'ummar Labanon.
|
||||