Sakon Jagora Imam Khamene'i Ga Sayyid Nasrallah Kan Shahadar Imad Mughniya":

________________________

Dan'uwa Madaukaki Hujjatul Islam Sayyid Hasan Nasrullah Shahadar dan'uwa mujahidi ma'abucin sadaukarwa da tsananin shaukin jihadi a tafarkin Allah Hajj Imad Mughniya babbar nasara ce da makoma mai kyau gare shi sannan kuma abin alfahari ga al'ummar Labanon da suka sami nasarar samar da irin wannan madaukakin mutum da mika shi ga tafarkin 'yanci da gwagwarmaya da zalunci.

Duk da cewa rashin wannan madaukaki mutum ma'abucin sadaukarwa lamari ne mai sosa rai ga dukkan madaukakan mutane da dukkanin wadanda suka sanshi musamman iyayensa, matarsa da 'ya'yansa, abokansa da sauransu, to sai dai rayuwa da mutuwar mutane irinsa lamari ne da ke kara wa al'umma karfin gwuiwa kuma abin koyi ga matasa sannan da kuma shata tafarki da hanyar isa ga wannan tafarkin.
Jagoran Imam Khamene'i Yana Tattaunawa Da Sayyid Hasan Nasrallah

Dole ne yahudawan sahyoniya mashaya jini su san cewa jinin shahidai irinsu Imad Mughniya zai tayar da darurrukan Imad Mughniya ne wanda hakan zai kara karfin gwagwarmaya da tsayin daka a gaban zalunci, fasadi da wuce haddi. Mutane irin wannan babban shahidi sun sadaukar da rayuwarsu ta jin dadi na duniya ga tafarkin kare wadanda aka zalunta da fada da zalunci da girman kan duniya. Wannan  yanayi ne da ke sanya mutum mika kai a matsayin girmamawa (gare su). Yardar (Aljannar) Allah ta tabbata a gare shi da dukkanin masu jihadi a tafarkin gaskiya.

Ina mika sakon taya murnata da kuma juyayi gare ka da iyalansa da sauran matasan kungiyar Hizbullah da 'yan gwagwarmaya da dukkan al'ummar Labanon dangane da wannan shahada.

Wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu.

Sayyid Ali Khamene'i

14/02/2008