"Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi
a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke daga gabanninku, tsamma-ninku, za ku yi takawa.
Kwanuka kidayayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana akan tafiya, sai (ya biya) adadi
daga wasu kwanuka na daban. Kuma a kan wadanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci
sai dai wanda ya kara alheri, to, shi ne mafi alheri a gare shi. Kuma ku yi azumi ne mafi alheri a gare ku,
idan kun kasance kuna sani". (Qur'an: 2:183-184) |