MENE NE MA'ANAR KALMAR 'MAULA'?:

Wani abin da ke da muhimmanci a nan, wanda kuma masu kokarin dushen hasken Amirul Muminina da sauran Ahlulbaiti (a.s) (duk da cewa dai sun gagara yin hakan) suke amfani da shi wajen sanya shakku cikin zukatan mutane, shi ne ma'anar kalmar "Maula" da ta zo cikin fadin Ma'aikin Allah (s) منْ كُنْتُ مَوْلاَهُ فَهذا عليٌّ مَوْلاَهُ (Duk wanda na kasance "maulansa" to Aliyu ma 'Maulansa' ne).

Su dai wadannan mutane suna kokari ne su fassara wannan kalma ne da wata fassara wacce za ta kautar da asalin abin da Manzon Allah (s) ya ke nufi cikin wannan kalami na sama. Yanzu bari mu yi dubi cikin abin da wadannan mutane suke cewa:

Su dai wadannan mutane suna cewa ne wannan kalma ta Maula ba tana nufin shugaba ba ne a nan face dai tana nufin wani abu ne daban. Sun ce ai wannan kalma tana da ma'anoni daban-daban da suka hada da Mataimaki, aboki, makwabci, shugaba, majibinci, da dai sauransu. Don haka suka ce Manzo (s) a nan ba yana nufin Aliyu shugaba ba ne face dai kawai yana nufin sauran ma'ana ne na wannan kalma, wato aboki, mataimaki ko kuma makwabci. A takaice dai kamar suna cewa Manzon Allah cewa ya yi: Duk wanda na kasance (abokinsa ko mataimakinsa ko makwabcinsa) to Aliyu ma (abokinsa ko mataimakisa ko makwabcinsa ne). Allah ka tsare mu da son zuciyar da za ta sanya mu rufe ido kan gaskiya da kuma canza kalaman Manzon Allah (s).

To yanzu bari mu yi bayani kan asalin ma'anar wannan kalma kamar yadda Manzo ya ke nufi, muna masu kafa hujja da wasu shaidu da suke tabbatar da cewa wannan kalma tana nufi shugaba (majibinci) ne ba wai aboki ko makwabci ba, kana daga baya kuma mu bayyanar da rashin gaskiyar ikirarin wadannan masu son zuciya.

A hakikanin gaskiya dai wannan kalma ta 'Maula' a mafi yawan wurare (musamman ma dai a wannan waje) ba ta daukan wata ma'ana ta daban in ba wannan ma'ana ta 'shugaba', 'majibinci' ba. Don kuwa a matsayin misali, wannan kalma ta 'Maula' ta zo har sau 18 a cikin Alkur'ani mai girma, kusan dukkansu suna ba da ma'anar shugabanci ne, kadan daga cikinsu ne suke ba da ma'ana ta aboki.

Don haka babu shakka cewa wannan kalma ta 'Maula' da Manzo ya fada tana nufin shugaba ne kuma majibincin al'amurra. Yanzu ba ri mu kawo dalilai da shaidun da suke nuni da wannan ikirari namu na cewa kalmar tana nufin shugaba ne:

Dalilan Da Suke Nuna Kalmar 'Maula' Tana Nufin Shugaba Ne.

Babbar hanyar da ake bi wajen ayyana ma'anar kalmar da take da ma'anoni da dama ita ce ta hanyar 'Qarina', wato abubuwan da suke kewaye da wannan abu, a nan ne za a iya tabbatar da ma'anar da wannan kalma take nufi daga cikin ma'anonin da take da su. Wadannan abubuwa kuwa sun hada da lokaci, wuri, maganganun da ake yi a lokacin da dai sauransu, dukkan wadannan abubuwa sukan taimaka wajen gano ma'anar da mai magana ya ke nufi lokacin da ya ambaci wannan kalma. Don haka idan muka yi dubi da wadannan abubuwa za mu ga cewa lalle Manzon Allah (s) yana nufin shugaba ne yayin da ya ambaci wannan kalma ta 'Maula'. Yanzu bari mu ga abubuwan da suke tabbatar da wannan ikirari na mu:

Shaida Ta Farko:

Ruwayoyi sun tabbatar da cewa kafin Manzon Allah (s) ya fadi wannan jumla ta Man Kuntu Maulahu... sai da ya tambayi sahaban da suke gurin cewa: "Ya ku mutane! Wane ne ya fi soyuwa ga muminai a kan kansu?", bayan da suka amsa masa da cewa 'Allah da ManzonSa', sai kuma ya sake ce musu: Hakika Allah Shi ne Majibincina ni kuma ni ne majibincin dukkan muminai, kuma ni ne na fi soyuwa a gare su a kan kawukansu, kafin nan sai ya fadi wannan jumla.

Daga wannan magana muna iya fahimtar abin da Manzo ya ke nufi a nan, shi ne kuwa batun shugabanci, don kuwa sai da ya tabbatar da shugabanci Ubangiji a kansa, sannan da kuma shugabancinsa akan muminai kafin ya fadi wannan jumla.

Idan kuwa ba haka ba ne da bai kawo batun shugabancin Ubangiji a kansa ba, don kuwa hada batun shugabancin Ubangiji a kansa da kuma shugabancinsa a kan muminai, shi ya ke tabbatar da shugabancin Ali a bayansa. Don kuwa Allah ai ba abokin kowa ba ne idan har an ce wannan kalma ta 'Maula' tana nufin aboki ne, ko kuma shin a wurin Ubangiji da Manzo tana iya daukan ma'anar shugabanci, amma a wajen Ali ba ta daukan wannan ma'ana sai dai kawai ma'anar aboki? Allah dai ya cece mu daga rufe idanuwanmu daga gaskiya.

Tambaya a nan dai ita ce mene ne fa'idar wannan dogon bayani na Manzo in ba don ya tabbatar wa mutane da shugabancin Ali a bayansa ba? Don haka wannan 'qarina' dai tana tabbatar mana da ma'anar wannan kalma ta 'Maula' da cewa shugaba ne, kuma kowa yana iya fahimtar hakan in ba wanda suka rufe idanuwa da zukatansu da son rai da kiyayya ba.

Shaida Ta Biyu:

Sannan kuma kafin fadin wannan jumla ta Man Kuntu Mawlahu, sai da Manzon Allah (s) ya tabbatar wa mutanen da suke gurin da jigogin akida, inda ya ke cewa: " Ashe ba za ku shaida cewa Babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah ba, kuma Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, kuma Aljanna gaskiya ce haka nan wuta ma gaskiya ce, mutuwa kuwa gaskiya kuma ranar tashin kiyama mai zuwa ce babu kokwanto cikinta, kuma Allah Zai ta da wadanda suke cikin kabari?"

Mene ne hadafin tabbatar da wannan batu na akida? Wannan ba wani abu ba ne face dai share fage kan abin da zai fadi nan gaba kadan, wato nada Amirul Muminina Ali (a.s) a matsayin halifansa. Idan kuwa ba haka ba ne to mene ne fa'idar duk wannan magana, don kawai ya ce wa mutane 'Aliyu abokinsu ne'? Manzon Allah ya fi karfin haka. Ai muna ganin babu bukatan sai ya yi ta wannan mukaddima kafin ya ce wa mutane Ali abokinsu ne, don kuwa daman ai shi ba ba ya gaba da su. Face dai saboda girman abin da zai fadi musu ne, da kuma sanin yadda wasu suke kiyayya da shi (Ali) ya sa ya zama dole ya sa su jaddada imaninsu tukun kafin ya gaya musu wannan kalami, kamar yadda za mu ga yadda wani ma ya yi musun hakan da nuna rashin yardarsa ga hakan (Shugabancin Ali), duk kuwa da batun jaddada imanin. Mai son karin bayani yana iya matsa nan don karin bayani.

Shaida Ta Uku:

Wani abin da ke nuni da batun shugabanci cikin kalmar 'Maula' shi labarin da Manzon Allah (s) ya bayar na kusatowan ajalinsa a farkon wannan huduba tasa kafin ya je ga batun Man Kuntu Maulahu..., inda yake cewa: "Lalle an kusan kirana kuma zan amsa(1)".

Wannan kalami dai na Manzon Allah (s) yana nuni ne da cewa Manzo din yana kokarin ayyana wa musulmi shugaba ne da kuma wanda zai kasance halifa a bayansa don toshe duk wata kafa da za ta iya tasowa nan gaba. Idan kuwa ba haka ba ne, wato ba shugabanci ba ne, kawai yana so ne ya tabbatar da abokanta, to ai ka ga babu bukatan ya ce wa mutane zai koma ga Mahaliccinsa, don haka ya saba wa hankali, alhali kuwa shi ne mafi girman masu hankali.

Shaida ta Hudu:

Fadin Manzon Allah (s) cewa: "Allahu Akbar (Allah Mai Girma) Kan Cika Wannan Addini, da Kuma Cika Ni'ima, da Kuma Yardar Da Ubangijina ya yi da Wannan Sako Nawa da Kuma Wilayar Aliyu a Bayana(2)", bayan da ya fadi jumlar: "Man Kuntu Maulahu"

Idan har kalmar 'Maula' tana nufin aboki ko mataimaki ne, to ya ya za a yi tabbatar da abokantakan Ali ta zamanto cikan addini da kuma ni'ima?, a fili dai ya ke cewa abin nufi a nan shi ne shugabancin Ali bayan Manzon Allah (s). Idan kuwa har wannan kalma tana nufin abokantaka ne, sannan kuma abokantakan ta kasance ita ce cikan addinin Musulunci, to hakan ma da ta kasance babbar falala gare shi da kuma wajibcin binsa, tun da dai abokantaka da shi cikan addini ne da kuma ni'imar Ubangiji.

To shin yanzu kuma akwai wata shakka kuma kan cewa ma'anar Maula ita ce halifanci da shugabanci?

Shaida ta Biyar

Wani babban abin da ke nuni da shugabancin Ali cikin wannan kalma ta 'Maula' kuma shi ne barka da taya murnar da Abubakar da Umar da sauran sahabbai masu yawa suka yi wa Ali bayan fadin Manzon Allah (s): Man Kuntu Maulahu.... Ruwayoyi sun bayyana cewa Abubakar da Umar su ne mutanen farko da suka zo suka samu Ali (a.s) suka masa barka da cewa: "Barka-Barka Ya Dan Abu Talib, A yau ka zama Shugabana da kuma shugaban dukkan muminai (maza da mata)(3)".

Abin tambaya a nan shi ne shin wai wani matsayi ne Ali (a.s) ya samu da har wadannan "Manyan Mutane" biyu za su yi masa barka da ta ya shi murnar? shin matsayi ne na shugabanci ko kuma dai abokantaka ne? Shakka babu dai matsayi na abokantaka dai bai kai ma ya sa su yi masa barka ba, don haka babu wani abin da ya rage face dai mu yarda cewa matsayi ne na shugabanci da jagoranci, don kuwa abokantaka tsakaninsu ba wani abu ba ne bako da har zai sa a taya shi murna.

Don haka wannan babbar hujja ce ta cewa kalmar 'Maula' a nan tana nufin shugaba ne. Ina masu cewa abokantaka ne? To a ina kuka samo wannan zance naku? Don kuwa manyan sahabbai ma dai ba su dauke kalmar a matsayin haka ba, su sun fahimce ta ne a matsayin shugabanci.

Shaida ta Shida:

Ruwayoyin da suka ambato wannan lamari na 'Ghadir Khum' sun tabbatar da cewa lokacin da Manzon Allah (s) ya tsaida da wadannan dubban al'umma don isar musu da wannan sako mai muhimmanci ana cikin tsananin zafin rana ne sannan ga kuma gajiya a jikin mutane, don haka abu ne da ba zai taba yiyuwa ba Manzo (s) ya tara mutane a cikin irin wannan yanayi don kawai ya ce musu 'Aliyu abokinku ne', don kuwa shi mutum ne mai tausayawa hatta makiyansa ballantana mabiyansa. Idan dai har makasudin wannan taro shi ne kawai a ce wa mutane Aliyu abokinsu ne, to babu yadda za a yi Manzo ya tara su cikin irin wannan zafin rana.

Don haka, tun da dai har Manzo ya tara al'ummarsa cikin wannan yanayi mai tsananin wahala, to lalle akwai wani sako mai muhimmanci da ya fi zance abokantaka, a'a ai daman muminai 'yan uwa da abokan juna ne, kamar yadda Alkur'ani mai girma ya sha jaddadawa, don haka babu bukatan a sake gaya wa mutane cikin irin wannan zafin rana mai tsananin gaske. Lalle dai akwai wani sako mai muhimmanci, shi ne kuwa batun shugabanci Ali akan sauran muminai bayan Manzon Allah (s).

Shaida Ta Bakwai:

Abu na gaba da ke tabbatar mana da batun shugabancin Ali cikin wannan kalami na Man Kuntu Maulahu.. shi ne abin da Amirul Muminina Ali (a.s) ya rubuta wa Mu'awiyya bn Abi Sufyan cikin baitocin wake cewa:

                      وأوجب لي ولايته عليكم
رسول الله يوم غدير خم

Ya wajabta min wilayarsa a kanku  *  Manzon Allah a ranar Ghadir Khum(4).

Wadannan baitoci dai na Amirul Muminina (a.s) suna nuni da cewa shi ma dai yana ganin ma'anar kalmar 'Maula' dai shi ne shugabanci ne. Shin masu cewa wannan kalma tana nufin aboki ne, sun fi shi sanin ma'anar kalmar ne?.

Shaida ta Takwas:

Ba wai Amirul Muminina (a.s) da Abubakar da Umar da ma wasu sahabbai ne kawai suke ganin wannan kalma ta 'Maula' tana nufin shugaba ba ne, har ma da Hassan bn Thabit, mawakin Manzon Allah (s), don kuwa ruwayoyi sun ruwaito cewa bayan wannan lamari na Ghadir, ya bukaci Manzo (s) da ya ba shi umarnin rera wake wa Amirul Muminina (a.s) a wannan rana inda yake cewa:

فقال له قُمْ يا علي فإنني*   رضيتك من بعدي امامًا وهاديً

Sai ya ce masa 'Tashi Ya Ali don ni  *   Na amince maka ka zama shugaba kuma mai shiryarwa a bayana.

Daga wadannan baitoci za mu fahimci cewa shi ma dai Hassan bn Thabit bai fahimci wata ma'ana ga wannan kalma ta 'Maula' ba in banda shugaba da majibincin al'amurra.

Mai karatu bayan wadannan dalilai da abubuwa da muka gabatar, shin har ya zuwa yanzu kuma akwai wani shakka kan cewa abin da Manzon Allah (s) ya ke nufi cikin wannan kalma ta 'Maula' shi ne halifanci da kuma shugabancin al'umma? Shin ya ya za a yi mutum ya dinga rudin kansa kan cewa kalmar tana nufin aboki ne?

Allah dai Ya tsare mu da son rai da son zuciya da guje wa gaskiya don dai kawai ba ta yi daidai da son zuciyarmu ba.



____________
(1)- Dubi littafin Al-Ghadir na Allamah Amini: Juzu'i na 1, shafi na 26,27,30,32,33,34,36,47,176, inda ya kawo masdarin wannan magana cikin littattafan Ahlussunna irinsu: Sahih Tirmizi, juzu'i na 2, shafi na 298; Al-Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki, shafi na 45, Al-Manaqib al-Thalatha na Ibn Futuh, shafi na 19, Al-Bidayah wa al-Nihayah na Ibn Kathir, juzu'i na 5, shafi na 209 da juzu'i na 7, shafi na 348, Sawa'iq al-Muhriqa: shafi na 25 da Al-Zawa'id na al-Haithami, juzu'i na 9, shafi na 165...da dai sauransu.
(2)- Dubi Juzu'i na farko na Littafin al-Ghadeer na Allamah Amini, shafi na 230.
(3)- Dubi littafin al-Ghadeer na Allamah Amini, juzu'i na 1, shafi na 270 da 283, haka nan kuma Sawa'ik al-Muhrika na ibn Hajr, Musnad Ahmad bn Hambal juzu'i na 4 shafi na 281, tafsir al-Tha'alabi, da dai sauransu
(4)- Al-Ghadir na Allamah Amini, juzu'i na 2, shafi na 3-25.