|
|
|
|
| |||||
Bukukuwan da ranaku idi dai suna da wani matsayi da muhimmanci cikin rayuwar kowace al'umma, don kuwa irin wadannan ranaku suna nuni ne da wani muhimmin lamari da ya
faru cikin rayuwar wannan al'umma. Wasu idin da kuma ranakun bukukuwan sun fi wasu muhimmanci a idon wannan al'umman, shi ya sa ma za ka ga sun fi ba wa wasu ranaku na idin
muhimmanci a kan wasu. Hakika abin da ya ke auna irin muhimmancin da wasu ranakun suke da su a kan wasu kuwa shi ne irin muhimmancin da abin da ya faru a wadannan ranaku yake
da shi a idon al'umman ne wajen ci gabansu da kuma 'yantar da su daga wani bala'i da dai sauransu.
A saboda haka ne ma a wajenmu musulmi wasu ranakun sun fi wasu ranakun muhimmanci, a matsayin misali, ranar Juma'a tafi dukkan ranakun mako muhimmanci, haka nan kuma a shekara
ranakun idi sun fi sauran ranakun muhimmanci da kuma daukaka da dai sauransu. To sai su musulmi irin wadannan ranaku a wajensu ba wai kawai ranaku ne na bukukuwa ba kawai, a'a ranaku
ne na nuna godiya ga Allah da kuma neman yardarSa.
To a halin da ake ciki dai kuma a mafi yawa daga cikin al'umman musulmi sun san ranaku guda biyu ne kawai a matsayin ranakun idi, wato "Ranar Karamar Salla" (Idul Fitr) da kuma "Babbar
Salla" (Idul Adhha). To sai dai kuma tarihi da kuma ruwayoyi daga dukkan bangarori biyu na musulmi (Shi'a da Sunna) sun tabbatar da cewa akwai wani idin kuma na daban a tsakanin
al'umman musulmi, to sai dai kuma saboda wasu dalilai na siyasa an batar da wannan rana ta idi daga al'umma, wato da dama daga cikin al'umman an hana su su san wannan rana, duk kuwa
da cewa shi ne idin da ya fi sauran idodi guda biyun da musulman suka sansu matsayin a wajen Ubangiji da kuma ManzonSa (s), kamar yadda muka gani a hadisin da muka kawo a farkon wannan
shafi.
Mene Ne Idul Ghadir?
Babu shakka wannan ita ce tambayar da duk wanda ya ji wannan kalma (Idul Ghadir) a karo na farko zai tambaya, wato mene ne Idul Ghadir? Kuma wane ne ya sanya wannan rana ta Ghadir ta zamanto idi ga al'ummar
musulmi ballantana ma a ce ita ce tafi?
To hakika wannan ba tambaye ce mai wuyar amsawa ba haka nan kuma ba abu ne da za su ki yarda da shi matukar dai suka ji cewa wanda ya sanya wannan rana a matsayin idi kuma ya ce shi ne idin da ya fi
kowane idi falala da daukaka shi ne Manzon Allah (s). Hakan kuwa ya faru ne a wannan rana ta 18 ga watan Zul Hajji shekara ta goma bayan hijira lokacin da ya nada Imam Ali (a.s) a matsayin halifansa
a bayansa wanda zai ci gaba da shiryar da al'umma bayan rasuwarsa hakan kuwa a bisa umarnin Ubangiji ne. Bayan wannan nadi sai Manzon Allah (s) ya zauna dukkan al'umman musulmi suna zuwa suna masa barka da shi da
Imam Ali saboda wannan lamari da ya faru. An ruwaito shi a wannan rana yana cewa: "Ku taya ni farin ciki......ku taya ni farin ciki...Don kuwa Allah Madaukakin Sarki Ya kebe ni da annabci kana kuma ya kebance
Ahlulbaitina da Imamanci (halifanci"(1) Hakika tarihi bai taba ruwaito cewa akwai wani abin da ya taba faruwa cikin rayuwar Manzon Allah (s) da ya faranta masa rai har ya ce "Ku taya ni farin ciki ...Ku taya ni farin ciki... ba, in banda Ranar Ghadir. Hatta ranar aurensa da Nana Khadijah bai fadi haka ba, haka nan hatta a ranar da ya yi hijira da kuma kubuta daga hannun kafiran Makka, bai fadi hakan ba. Haka nan kuma a ranar "Fathu Makka" da kuma nasarar da musulmi suka samu a kan kafirai, bai fadi hakan ba, da dai sauran dukkan ranakun da za ka iya tunani na farin ciki da suka sami Manzon Allah (s) cikin rayuwarsa, bai fadi wannan kalma na "Ku taya ni murna" ba. Rana guda kawai da ya fadi hakan ita ce "Ranar Ghadir", inda ba ma wai sau guda kawai ya fada ba, face dai ya ci gaba ne da maimaita wannan kalma. To abin tambaya a nan shi ne me ya sa hakan? Me ya faru ne a wannan rana har ya sa Manzo din ya ke ta nanata wannan kalma? Shin wannan abu da ya faru ya fi sauran dukkan abubuwan farin ciki ne da suka faru a rayuwar Manzo din muhimmanci? Idan haka ne wani muhimmanci wannan abu ya ke da shi? Ga Karin Bayani A takaice dai amsa ga tambaya ta farko ita ce cewa dai Manzon Allah (s) ya fahimci girman wannan rana ce da kuma daukakan da take da ita sama da sauran ranaku. Za mu iya fahimta hakan ne kuwa daga cikin wannan hadisi da muka kawo a saman wannan shafi, wato cewa: "Ranar Ghadir Khum Ita ce Mafi Girman Idin Al'ummata, Rana ce da Allah Ta'ala Ya Umarce Ni In Nada Dan'uwana Aliyu bn Abi Talib Alama Ga Al'ummata Wacce Za Su Shiriya Da Ita A Bayana, Rana ce da Allah Ya Cika Addini a Cikinta Kana Kuma Ya Cika Ni'ima a Cikinta Sannan Kuma Ya Yarda da Musulunci A Matsayin Addini Gare Su.(2)" Daga cikin wannan hadisi dai za mu iya fahimtar wasu abubuwa kamar haka:
To bayan Manzon Allah (s) A'imma Ahlulbaiti (a.s) sun ci gaba da daukan wannan rana a matsayin ranar idi, ranar bukukuwa da kuma tara al'umma a ci abinci da dai sauran nau'oi na bukukuwa don nuna farin ciki kan wannan rana. Don karin bayani bari mu kawo wa mai karatu wasu daga cikin hadisan da aka ruwaito daga Ahlulbaiti (a.s) da suke nuni da yadda suke nuna farin cikinsu a wannan rana da kuma yadda suke ganin ranar:
Don haka ne ma musulmi musamman mabiya Ahlulbaiti (a.s) suke girmama wannan rana da kuma daukanta a matsayin ranar idi, inda suke bukukuwa don nuna murnarsu da kuma mika godiyarsu ga Allah Madaukakin Sarki saboda ni'imar
da ya yi musu a wannan rana.
____________ (1)- Sharaful Mustafa na Hafiz Abi Sa'id al-Naisaburi. (2)- Dubi littafin "Al-Ghadir" na Allamah Amini, juzu'i na 1, shafi na 283. |
||||||