ARADU DAGA SAMA AKAN MAI MUSUN HALIFANCI ALI (A.S):

Sanannen abu ne cewa daga cikin musulmi na wancan lokacin akwai wadanda shaidan ya yi musu shifta kana ya sanya musu kiyayya da Amirul Muminina Ali bn Abi Talib (a.s) saboda wasu dalilai na su na son rai da kuma rashin tsoron Allah Madaukakin Sarki, don haka wannan zaben da Allah da ManzonSa suka yi wa Ali a matsayin halifa bai yi musu dadi ba, don haka suka nuna rashin amincewarsu a fili duk kuwa da cewa wasu sun ki yin hakan saboda wasu dalilai na siyasa.

To daga cikin irin wadannan mutane akwai wani mutum da ake kira Nu'uman bn Harith al-Fahri, shi wannan mutumin ya kasance mai tsananin gaba da Imam Ali (a.s) da kuma Ahlulbaiti (a.s). Don haka lokacin da labarin wannan lamari na zaben Ali a matsayin halifan Manzo (s) ya isa gare shi sai hankali ya tashi da kuma motsa masa wannan tsohuwar gaba tasa, don haka sai ya nufi wajen Manzon Allah (s) cikin fushi da nufin tambayarsa me ya sa ya yi haka. Sai dai wannan wawa kana kuma jahili ba kauye baisan cewa (ko kuma da gangan ya nuna hakan ) lamarin ba wai daga wajen Manzo ne ba, a'a lamarin daga wajen Allah ne.

Don haka sai ya nuki gari da nufin zai je gurin Manzo (s) da jin dalilin yin hakan. Ko da isansa wajen Manzon Allah (s) sai ya daga sautinsa cikin fushi yana cewa: Ya Muhammad! (yana mai karya umarnin Allah na cewa: "Kada ku sanya kiran Manzo a tsakaninku kamar kiran sashenku ga sashe..."). Sai Manzo (s) ya daga kansa sama don ganin wanda yake kiransa, da kuma biya masa bukatansa.

Sai wannan mutumin ya ce: "Ya Muhammadu!...Ka umurce mu da mu shaida babu wani abin bautawa sai Allah, muka yarda. Kana kuma ka umarce mu da mu shaida kai Manzon Allah ne, muka amince da hakan. Haka nan kuma ka umarce mu da yin salla, da ba da zakka da kuma yin aikin hajji, duk dai muka amince da hakan. To amma duk hakan bai ishe ka ba, har sai da ka daga hannun dan baffanka (Ali) da kuma fifita shi a kanmu kana mai cewa: Duk wanda na kasance shugabansa to ya Ali ma shugabansa ne. Shin wannan lamari daga gare ka ne ko kuma daga wajen Allah ne?".

Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un, subhanallah, shin wannan wani irin cin mutumci ne da rashin ladabi ga Manzon Tsira, shin hakan ya dace ga mutum irin Manzon Allah wanda a koda yaushe ya kasance mai tausaya wa mabiyansa da ma dukkan al'umma? Allah Ya tsare mu da butulci!!!!!!.

To amma da yake Manzon Allah mai rahama ne, sai ya dubi wannan bakauye cikin fara'a da jin kai ya ce masa:

"Ya kai wannan mutum....na rantse da wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, wanda lamari daga Allah ne".

To me ya rage kuma? Ashe ba shi kenan ba? Ashe akwai wani abin da ya rage face dai yin da'a da mika wuya? To amma ina, nan take sai wannan mutumin ya juya yana guna-guni yana cewa:

"Ya Allah idan har abin da Muhammadu ya fadi gaskiya ne, to ka sauko min da duwatsu daga sama, ko kuma ka zo min da azaba mai tsanani".

To nan take kuwa sai Allah ya jefi shi da wani dutse daga sama a kansa ya fita ta duburansa, ya fadi mushe macacce. Wannan shi ne sakamakon gaba da Amirul Muminina Ali (a.s) kenan.

Daga nan sai aya ta sauko wa Manzon Allah (s) tana cewa:

سأَل سائِلٌ بعذابٍ واقع للكَفرين ليسَ له دافع منَ الله ذي المعارج

Wani mai tambaya ya yi tambaya game da azaba, mai aukuwa. Ga kafirai, ba ta da mai tunkudewa. Daga Allah Mai Matakala. (Suratul Ma'arij, 70:1-3)

To mai karatu wannan dai shi ne sakamakon gaba da hukumcin Allah. Kuma wannan aya tana tabbatar mana da cewa gaba da kin yarda da wannan hukumci na Ubangiji, wato nada Ali (a.s) a matsayin halifan Annabi na kai mutum ya kafirta da kuma fuskantar fushin Allah, kamar yadda wannan aya ta tabbatar.

Don karin bayani kan wannan aya da kuma dalilin saukarta, mai karatu na iya koma ga wadannan masdarori na kasa:

  1. Tafsirul Kurtabi, yayin da yake bayani kan ayar.
  2. Tafsirul Gharib al-Kur'an na Hafiz al-Harawi, shi ma yayin tafsirin ayar.
  3. Tafsir Abi al-Sa'ud juzu'i na 8 shafi na 292.
  4. Tafsir al-Sirajul Munir na al-Sharini al-Shafi'i, juzu'i na 2, shafi na 364.
  5. Tafsir al-Manar, yayin tafsirin ayar.
  6. Tafsir Majma'ul Bayan na Tabrisi, yayin tafsirin ayar.
  7. Tafsir al-Mizan na Allamah Tabataba'i, yayin tafsirin ayar.
  8. Tafsir al-Safi, yayin tafsirin ayar.
  9. Fara'id al-Simtain na Sheik al-Islam al-Humuwainii, babi na 13.
  10. Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbagh al-Maliki, shafi na 26.
  11. Faizul Qadir, sharhin al-Jami al-Sagir, juzu'i na 6, shafi na 218.
  12. Siratul Halabiyya, juzu'i na 3, shafi na 302.
  13. Sharh al-Jami' al-Sagir na Suyuti, juzu'i na 2, shafi na 387.
  14. Nurul Absar na Shabalanji al-Shafi'i, shafi na 78.
  15. Da dai sauransu.

Hakan dai ya isa ga mai son sanin gaskiya da kuma riko da ita.