|
|
| |||
|
Shahada Da Shahidai
v
Shahada
daukaka ce madawwamiya.
v
Shahada
abin alfaharin waliyai ce, mu ma abin alfaharinmu ce.
v
Tsoro
na ga wanda akidarsa ba shahada ce ba.
v
Shahada
sirrin nasara ce.
v
Al’ummar
da ke fatan shahada ta ci nasara.
v
Ku
idan kuka yi galaba a duniya kunci nasara haka idan kuka yi shahada duk dai ku
ne masu nasara.
v
Shahada
a tafarkin Musulunci abin alfahari ne gare mu dukanmu.
v
Shahada
albarka ce mai girma gare mu.
v
Wannan
irin jin neman da kuma zama a shirye domin sadaukar da kai shi ne ya sa al’umma
hannu rabbana ta yi galaba a
v
Al’ummar
da matanta da mazajenta a shirye suke da su bayar da rayukansu kuma suna neman shahada, babu
wani karfi da zai iya kalubalantarta.
v
Jinin
shahidanmu ci gaba ne na tsarkakekken jinin shahidan
v
Al’ummar
da shahada abin daukaka ne gare ta, to taci nasara.
v
Al’ummar
da ke son yin shahada ba ta da wani jin
tsoro.
v
Jama’ar
al’umarmu ta bayar da jini domin a samu Jamhuriyar Musulunci .
v
Jama’ar
al’ummarmu sun kasance masu burin shahada ne, kuma da burin shahadan ne wannan
yunkurin ya tabbata da ya kuma ci gaba.
v
Daga
Allah mu ke dukanmu, dukkan halittu daga Allah suke baki daya, alamun samuwar
Allah ne, kuma komai zai koma zuwa gare Shi ne. Don haka abin da ya fi komawar
ta zama ta hanyar zabin da zabar wa kai,
mutum ya zabi shahada a tafarkin Allah, kuma mutum ya zabi mutuwa a tafarkin
Allah da a kashe shi domin Musulunci.
v
Mutuwa
a
v
“Jar
Mutuwa” tafi “bakar mutuwa”.
v
Wace
irin gafala da jahilci bayin duniya suke da ita, wadanda suke neman ma’anar
shahada a shafukan littattafa na dabi’a, suke kuma neman siffofinsu a cikin
wake da take da harzuka, suke kuma amfani da fasahar sakar zuci da liffan
hankali domin gano su. Har abada ba za su taba fahimtan haka sai da kauna.
v
Shahidan
juyin Musulunci mai girma, kamar shahidan farkon Musulunci suna da daukaka a
wurin Allah kuma Allah Madaukakin Sarki da Shuwagabannin Musulunci na himmatuwa
da su.
v
Kun
ci nasara ne saboda kun rungumi shahada kuma wadanda ke tsoron mutuwa da
shahada su ne masu karyewa.
v
Ashe
shahada ba gado ba ce daga shugabanninmu wadanda suka dauki rayuwa tamkar imani
da gwagwarmaya, wadanda kuma suka kare
Musulunci da jininsu, kuma suka gadar da ita ga al’ummarmu ma’abuciyar shahada.
v
Ina
sanar wa jama’armu da miliyoyin mutanenmu cewa babu wani juyin da aka tabbatar
da shi ba tare da neman shahada, sadaukarwa, kokari, wahala, shan wuya, tsadar
kaya da rashinsu da matsa lamba ba.
v
Shahada
a tafarkin Allah ba wata aba ce da za a kwatanta darajarta a ma’aunin dan Adam
da abin duniya ba.
v
Shugabanmu
shi ne wannan yaro[1]
dan shekara 12 wanda karamar zuciyarsa tafi darurrukan harsunanmu da
alkalummanmu, wanda ya rungumi nakiya ya fada da ita a karkashin tankar yaki ta
abokan gaba ya rugurguza ta tare da kansa ya sha daga kogin shahada.
v
Farin
cikina ga wadanda suka mayarwa Allah da abin da ya ba su (rayuwa), mu kuwa mu
ne kashin bayansu da muka saura.
v
Ya
saura gare mu da mu bayyana raunukanmu kuma mu nuna godiyarmu wa wadannan
mayakan Musulunci wadanda suke neman shahada kuma ta hanyar jaruntaka suke kare
kasarsu ta Musulunci da kuma tsarkakakken jininsu suka yada haske domin nuna wa
al’ummomin da suke a cikin kangi hanya.
v
Son
barka ga wadannan shahidai saboda abin da suka samu na jin dadin debe kewa da
saduwa da Annabawa da Waliyai da kuma shahidan farkon Musulunci. Fiye da wannan
kuma shi ne, barkansu da kaiwa ga ni’imar Allah wadda ita ce yardar Allah mafi girma.
v
Ya
ku shahidai; ku zama masu sanyin idaniya a kusaci da Allah, al’ummarku ba su yi
sako-sako da cin nasarar da kuka samar ba.
v
Ku
(shihidai) shaidu ne na hakika, wadanda ake tunawa da daukaka da jaruntaka kuma
mafi dacewar bayi abin koyin bayin Allah masu tsarkin niyya, lalle kun tabbatar
da mika wuyanku ga Allah Ta’ala da kuma bautarku gare shi ta hanyar ba da
jininku da rayukanku.
v
Кasar
da kowa a shirye yake domin sadaukar da rayuwarsa da yin shahada, da me kuma
ake tsoratar da ita?
v
Hikima
ita ce mutum ya yunkura don yin jihadi ba
tare da kwarmato na siyasa da shaidan ba, kuma ya sadaukar da kansa
saboda manufar, ba wai saboda son rai ba wannan shi ne tafarkin addinin mutanen
Allah.
v
Ina
sanar da ku ya ku ‘yan ‘uwana muminai, zai fi mana kwarai idan miyagun Amirka
da Rasha suka halaka mu kuma ta hanyar zub da jininmu mu koma ga Allah tare da
mutunci, a
v
Kada
ku ji tsoro! Ku ne masu nasara InshaAllahu ko mun kashe ko kuma an kashe mu
gaskiya tana tare da mu. Idan aka kashe mu zai kasance a tafarkin Allah, kuma
idan muka kashe, wannan shi ma domin Allah ne, wannan kuwa ita ce nasara.
v
Sadaukarwa
da fansa su ne makamashin juyi guda biyu kamar kuma yadda shahada da shirin ta
larura ce a kowane juyi.
v
Mai
jihadi a tafarkin Allah, ya wuce a kimanta kyawon aikinsa da ma’aunin alatun
duniya.
v
Mu
mazauna bayan kasa ko kuma halittun duniyar taurari yaya za mu iya sanin mene
ne abin da aka tanadawa shahidai a gurin Ubangiji?
v
Duniya
tare da dukkan kimarta da dadinta ta yi kadan kwarai ta zama wani bangare ko
matsayi ga wadanda suka yi yaki a tafarkin Allah.
v
Idan
ka kashe mu Insha Allahu, za mu shiga aljanna, kuma idan muka kashe, a nan ma
zamu shiga aljanna.
v
Idan
aka kashe ku, kuna daga cikin ‘yan aljanna haka kuma idan kuka kashe to kuna
daga cikin ‘yan aljanna.
v
Idan
muka kashe mun rabauta ko kuma aka kashe mu duk dai mun rabauta.
v
Matukar
dai mun gaji wancan jinin, ma’abuta samun shahidai da matasan da suka saura, mu
nutse cikin jinin shahidai, kada mu zauna haka kawai, mu yi iyakar kokarinmu mu
ga mun kai gacin burin sadaukarwarsu.
v
Shahada
kyauta ce daga Allah Madaukakin Sarki ga wadanda suka cancance ta.
v
Kuka
ga shahidi yana rura wutan yunkuri ne.
v
Kuka
wa shahidin da ya sadaukar da komansa a tafarkin Musulunci al’amari ne na
siyasa kuma yana da tasiri mai yawa wurin ciyar da juyin gaba. Mu yi amfani da
irin wadannan tarurruka.
v
Makabartar
shahidai da jikkunansu da kuma jikkunan nakasassun yaki, harsuna ne masu ba da
shaida game da girman matabbatar ruhinsu mai dorewa.
v
Jinin
matasanmu ya yi galaba a
v
Ya
ya za a yi mutanen da ke ganin karfinsu a jinin shahidanmu, ba za su yi ma
mutum tasiri ba?
v
Hidima
a Bonyad Shahid[2]
(Mu’assasar Shahidai) ya fi kowane irin hidima.
v Ina
daukar shahada a tafarkin Allah kuma domin manufofi na addini a matsayin
daukaka madawwamiya. [1] .
A nan Imam yana nufin wani saurayiin sojan sa kai (Basijii) mai suna Husaini
Fahmidi ne. wannan saurayi ko da yake a lokacin yana da shekara 12 ne amma ya
nuna jaruntaka kwarai da gaske lokacin yakin Iran da Iraki wanda aka shafe
shekaru takwas ana yi sakamakon ziga kasar Iraki da kasashen Turai, musamman
kasar Amirka, suka yi don ta fada wa Iran. Saboda jarunta da kwazon wannan
yaro, kwamandojin yaki sukan barshi ya halarci fagen fama. Babban jaruntar da ya
yi shi ne lokacin da ya sanya bama-bamai a jikinsa ya fada cikin rundunar
abokan gaba don hana tankokin yakinsu kai hari, inda bama-baman suka fashe
tankokin suka tarwatse shi kuma ya yi shahada. Wannan irin jarumta ya burge
kowa, al’amarin da ya bude kofa ga sauran sojoji don su yi koyi. A sabili da
haka ne ma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanya hotonsa a jikin kudinta na
riyal 100 da riyal 1000 don tunawa da kuma girmama wannan babban aiki da ya yi. [2] .
Ran 15/3/1980, Imam Khumaini (r.a) ya ba da umurnin kafa wata cibiya da sunan
“Mu’assasar Shahidan Gwagwarmayar Musulunci” don kulawa da iyalan shahidai da
kuma sojojin da suka sami nakasa. A cikin sakon da ya aika wa Hujjatul Islami
wal Muslimin Mahdi Karrubi, Imam ya ba da umurnin cewa lallai ne a bada
muhimmanci ga iyalan shahidai da sojojin da suka sami nakasa, don su sami
ingantaccen ililmi, aikin yi da kuma kula da lafiyarsu. A halin yanzu wannan
cibiya ta samar da ilimi da kuma ababan jin dadi ga wadannan iyalai da
‘ya’yayensu a duk fadin kasar Iran.
|
||||