|
|
| |||
|
Watan Muharram Da Waki'ar Ashura
v
Watan
Muharram wata ne da adalci ya tunkari zalunci kuma gaskiya ta kalubalanci karya
kuma tabbatar da cewa a ko da yaushe a tarihi gaskiya na rinjayar karya.
v
Muharram wata ne wanda Musulunci ya
sake rayuwa ta hannun Shugaban dukkan mujahidai (Imam Husain) kuma aka tserar
da shi daga makircin banu Umayya[1]
lalatattu wadanda suka kai addinin Musulunci ga halaka.
v
Jinin Shugaban Shahidai (Imam
Husainin) ne yake haifar da yunkuri a cikin jinin jama’ar Musulmi.
v
A mazhabar Shi’a, Muharram wata ne
wanda a cikinsa aka ci nasara da jini da kuma sadaukar da kai.
v
Muharram watan babban yunkurin Shugaban
Shahidai ne na farin cikin waliyan Allah wanda ta hanyar yunkurinsa na tinkarar
Dagutu, ya karantar da Bil Adama yadda ake ginuwa a yi tsayuwar daka da kuma
cewa hanyar rusa azzalumai da karya ma’abuta mulkin
v
Lokacin yunkuri da jaruntaka da
sadaukar da kai na farawa ne da shigowar
watan Muharram. Wata ne wanda jini ya yi galaba a
v
Sun kashe Shugaban Shahidai tare da
mabiyansa da danginsa, amma sakonsa ya isa zuwa gaba.
v
Shahadar mai martaba Imam Husain (a.s)
ta rayar da akidar Musulunci.
v
Rayar da bukin Ashura (goma ga watan
Muharram lokacin da Imam Husaini ya yi shahada), na da muhimmanci a al’amurran
ibada da siyasa.
v
Juyin Musulunci na
v
Gwabzawar Karbala ta ruguza fadar
azzalumai da jini, mu kuma Karbalarmu ta rusa fadar shedana ce.
v
Ku raya
v
Al’amarin
v
Wajibi ne ga jama’ar al’ummarmu da su
raya al’amarin Ashura a bisa yadda Musulunci ya tsara tare da dukkan hallara.
v
Ku kula da watan Muharram, domin
dukkan abubuwa da muke da su daga gare shi ne.
v
Watan Muharram da Safar su ne suka
raya Musulunci.
v
Duk wannan hadewar kalma guda din
wanda shi ne asasin cin nasararmu, ya samo asali ne daga albarkacin zaman
makoki da tarurrukan juyayi da kuma wa’azce-wa’azcen da yada Musulunci.
v
A yi kokarin ganin an yi taron makoki
da zaman juyayi domin tunawa da Shahadar Salihan Bayi, Farin Cikin Raunana
(Imam Husaini (a.s) ), tare da cikowar yawan jama’a da kuzari mai yawa, domin
wadannan bukunna suna ishara ne ga ranar cin nasarar hankali a kan jahilci,
adalci a kan zalunci, amana a kan ha’inci da kuma hukumcin Musulunci a kan na
Dagutu. A daga tutocin Ashura da ke shafe da jini a matsayin ishara ga isowar
ranar ramuwar gayyar wadanda aka zalunta a
v
Muharram wata ne, wanda mutane a
cikinsa a shirye suke su saurari gaskiya.
v
Yin kuka domin bakin ciki wa Imam
Husaini (a.s) da rayar da yunkurin da tabbatar da gaskiyar cewa mutane marasa
yawa sun tunkari babban azzalumin sarki, dukkan haka suna a matsayin abubuwan
da ke wanzuwa a yau.
v
Dukan kirji a jerin gwano, dole ne ya
zama yana da ma’auni.
v Ashura
rana ce ta zaman makokin al’ummar da aka zalunta, ranar sake haifar da
Musulunci da Musulmai. [1] .
Bani Umayya sunan wata gidan sarauta ce wadda suka hau karagar shugabancin
al’umman Musulmi a shekara ta 40 bayan hijira (662 A.D) bayan halifofin nan
guda hudu, har zuwa shekara ta 132 bayan hijira (750 A.D). Shugaban wannan
masarauta shi ne Mu’awiyya ibn Abu Sufyan, wanda ya assasa wannan mulki na kama
karya wanda a fili ya saba wa koyarwa ta Musulunci. Hakika tarihi ya shaida
irin zalunci da babakeren da ya faru a duniyar musulmi lokacin mulkin Banu
Umayya, kamar su kisan gilla, bacewa, tsare mabiya Ahlulbaiti a cikin fursunoni
da kuma kashe Imam Husaini (a.s) da mabiya Yazid ibn Mu’awiyya suka yi.
|
||||