Ayari fursunonin yakin gidan Manzon Allah (s.a.w.a) da ya hada da mata, kananan yara da kuma Imam Aliyu bn Husaini al-Sajjad(1)(a.s) sun kama hanya(2) zuwa Kufa, su kuma jikkunan shahidai masu tsarki aka barsu a cikin wannan kasa mai zafin gaske.
Haka dai aka bar wadannan jikkuna masu tsarki a filin dagan, a nan ga jikin Husaini (a.s) a daya bangaren kuma ga na dan'uwansa Abbas, a can kuma ga taurarin jikkunan iyalan gidan Abu Talib, a daya bangaren kuma ga jikkunan sauran sahabban Husaini (a.s). Wadannan jikkuna dai sun cika filin dagan da ya kasance kamar sama a gare su, su kuma kamar taurari a gare shi.
Imam Sajjad (a.s) dai a wannan lokaci yana cikin igiyoyi da sarkoki ne da aka daure shi da su alhali kuwa yana cikin bakin cikin da zubar da hawaye kan abin da ya gani. Haka dai wannan ayari ta fursunonin yakin gidan Annabi suka yi ban kwana da jikkunan shadidai suna masu burin da ma a ce an bar su tare da su. Haka suka bar wannan wuri wanda ya zamanto wajen juyayin wannan abu da ya faru ga mawaka da masu juyayi.
To yanzu kuma bari mu koma wajen Bani Asad, wajen mutanen al-Ghadhiriyyah, wadanda wannan yaki ya faru ne kusa da matsuguninsu. Bayan wucewar sojojin Umar bn Sa'ad, sai suka fito suna neman wadannan jikkuna masu tsarki da aka barsu na kwanaki uku cikin zafin rana, iska mai karfi kana ga dabbobin daji(3).
Su dai wadannan mutane daga Banu Asad, mazauna al-Ghadhiriyya, sai suka nufi inda jikkunan Husaini da sahabbansa (a.s) suke, suka yi musu salla da kuma rufe jikin Husaini (a.s) a inda ya ke a halin yanzu, suka kuma rufe dansa Aliyu bn Husaini al-Asgar (karami) a wajen kafarsa, sannan kuma suka tona babban rami kusa da kafar Husaini (a.s) din suka hada gaba dayan shahidan suka rufe, sannan kuma suka rufe Abbas a inda aka kashe shi akan hanyar al-Ghadhiriyyah, wato inda kabarinsa ya ke a halin yanzu(4).
Haka dai jikin Husaini (a.s) ya kasance a kabarinsa da ke kusa da kogin Furat da ke Karbala(5), wajen da zukata muminai yake son ziyarta, kamar yadda kuma ya kasance fitila wacce take haskaka tafarkin ma'abuta yunkuri. Ta haka ne ya samu haduwa da shahidai, masu gaskatawa, salihai da Annabawa, kuma wadannan sun kyautatu su zamanto abokan tafiya.
Haka dai wadannan mutane suka bude hanya ga ma'abuta yunkuri da kuma ma'abuta neman 'yanci.