KOMOWAR FURSUNONIN YAKI

Rakuma dai suka kama hanyar Kufa suna dauke da iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) a matsayin fursuno-nin yaki. Sun kama hanyar ne kuwa a rana ta biyu da faruwar wannan aika-aika (sha daya ga watan Muharram).

Haka dai wannan ayari na fursunonin suka tsaga zafin hamada ba abin da ke tare da su in ban da tunanin wannan bala'i da kuma daren rabuwa mai ban tsoro, wato daren sha daya ga wata, wanda suka kasance a cikinsa a kan jikkunan shahidai da aka kashe.

A wannan lokaci dai wadannan iyalai na Manzon Allah (s.a.w.a) suna kewaye ne da wadannan marasa imani, mashaya jini, wadanda suke jin dadin ganin halin kuncin da wadannan fursunoni suke ciki da kuma kukan da mataye da kananan yara suke yi da kuma halin da Aliyu bn al-Husaini (a.s) yake cikin saboda tsananin rashin lafiya da kuma sarkokin da aka daure shi da su.

Haka dai wannan ayari suka shigo garin Kufa, mutanen garin Kufan kuwa suka fito bakin tituna cikin mamakin ganin halin da suke ciki, wasu suna tambaya wadannan fa su wane ne, wasu kuma wadanda suke da masaniyyar abin da ya faru suka kasance cikin damuwa, nadama da kuma kunya kan abin da ya janyo hakan.

Haka dai wannan ayari ya kutsa kansa cikin mutanen Kufa, wadanda suke a kan hanyarsu ta zuwa fadar Ubaidullah bn Ziyad, suna masu kuka da juyayin abin da ya samu Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) saboda ha'inci da suka yi wa shugaban musulmi kana kuma jikan Manzon Allah, Imam Husain (a.s). A halin yanzu ga su nan suna ganin iyalansa, matansa, matan sahabbansa a matsayin fursunonin yaki, suna fuskantar dukkan wani nau'i na azaba daga Iyalan Ziyad. A waje guda kuma ga kan jikan Manzon Allah nan an tsire shi a kan saman garin Kufa a kan mashi mai tsawon gaske, alhali kuwa su suka kira shi don ya zamanto shugaban al'umma kana mai shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici.

Zainab 'yar Aliyu bn Abi Talib (a.s) ta dubi wadannan mutane da suka taru hawaye na zuba mata saboda tunanin rashin dan'uwanta Husaini (a.s) da ta yi, cikin fushi ta ce musu su yi shiru da bakinsu don ta gabatar musu da jawabi. Nan take suka yi shiru don sauraron abin da Zainab, 'yar Fatima al-Zahra, 'yar'uwar Husaini (a.s) za ta gaya musu, ta fara da cewa:

"Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga Babana Muhammad da iyalansa tsarkaka zababbu. Bayan haka, Ya ku Mutanen Kufa, Ya ku ha'inai maciya amana; shin kuna kuka ne? To kada Allah Ya sa hawayenku ya bushe, sannan kuma kada wannan juyayi naku ya kare. Ku dai tamkar macen da ta kuncen igiyar da ta riga da ta kitsa ta ne(1), imaninku bai kasance ba face ha'inci da yaudara. Shin a cikinku akwai wani mutum in ban da mai da'awar karya na girman kai, wulakantacce, abin kyama, dan koran sarakuna, abin harin abokan gaba, tsiron da ke cikin bola(2), ko kuma kamar azurfar da ke cikin kabari(3)? Ya munana abin da zukatanku suka kitsa muku, Allah Yana fushi da ku, kuma lalle za ku tabbata cikin azaba. Shin kuna kuka da nuna juyayi ne? To wallahi ku yi kuka da yawa kana ku yi dariya kadan, don kuwa ayyukanku sun munana ta yadda ba za ku iya wanke su ba. Shin ya ya za ku iya goge laifin kashe silsilar Cikamakin Annabawa, ma'adinin sakon (Musulunci), shugaban matasan Aljanna, makomar zababbunku, makomar da kuke komawa yayin musiba, hasken hujjojinku kana kuma mai kare sunnoninku. Lalle laifin da kuka aikata ya munana, kuma ya koma gare ku, babu tuba gare ku. Hakika kokarinku ya gaza kamar yadda hannayenku ma suka gaza, kun yi asara, ba abin da kuka sa kawukanku a ciki face fushin Allah, kamar yadda wulakanci da kaskanci suka fada muku. Kaiconku Mutanen garin Kufa! Shin kun san yadda kuka keta hantar Manzon Allah? Kuma wace 'yarsa ce kuka keta huruminta? Kuma wani jininsa ne kuka zubar kana kuma wani haraminsa ne kuka keta? Hakika ayyukanku sun munana kwarai da gaske, wanda munin nasu ya cika sama da kasa. Shin za ku yi mamaki idan sama ya yi ruwan jini? Lallai azabar ranar lahira ya fi zafi kuma ba ku da mataimaki. Kada jinkirin da aka yi muku wajen azaba ya rude ku lallai Ubangijinku Yana nan a madakata(4)".

Daga nan sai tawagar fursunonin gidan Manzon Allah (s.a.w.a) suka wuce cikin hanyoyin garin Kufa zuwa fadar mulki don su gana da Ubaidullah bn Ziyad wanda yake zaune a fadar tasa yana karban gaisuwar mutanen da suka zo masa barka da samun nasarar da ya yi kan wadanda suka yi kokarin tunkude mulkin Umayyawa.

Ya zauna cikin girman kai alhali kan Husaini (a.s) yana gabansa yana wasa da shi da kuma bugun kan da bulaliyar da take hannunsa cikin farin ciki da annashuwa. Wannan yanayi dai ya sosa wa wani tsohon sahabi mai suna Zaid bn Arkam rai, sai ya kalli Ibn Ziyad wanda a daidai lokacin yana dukan fuskar Husaini (a.s) ya yi masa tsawa ya ce:

"Daga bulaliyarka daga wadannan laba guda biyu, na rantse da Ubangijin da babu wani ubangiji sai shi, na ga labban Manzon Allah (s.a.w.a) guda biyu a cikinsu (labban Husaini) a lokuta da yawan da ba zan iya kirga su ba". Daga nan sai ya fashe da kuka. Sai Ibn Ziyad ya ce: "Allah Ya sa idanuwanka su zubar da hawaye, shin kana kuka ne saboda nasarar da muka samu? Da ba don kai tsoho ba ne wanda hankalinsa ya fita daga gare shi ba, da na sare kanka".

Nan take Zayd bn Arkam ya fice daga fadar cikin fushi, yana mai share hawayen da ke zubo masa da kuma tunanin yadda yake daukan wannan abin kauna nasa Husaini a lokacin yana dan karami. Yayin fitarsa daga fadar, an jiyo shi yana cewa: "Daga yau Ya ku Larabawa kun zama bayi, kun kashe dan Fatima kuka dora Ibn Marjana (a matsayin shugabanku), alhali kuwa yana kashe mafiya daukakanku da kuma daukaka mafiya sharrinku, kun yarda da wulakanci, Allah wadaran wanda ya yarda da kaskanci(5)".

Fitan wannan tsohon sahabi ke da wuya sai aka shigo da fursunonin(6) yakin gidan Manzon Allah (s.a.w.a) cikin fadan mulki. Aka gabatar da mata da yara da Aliyu bn al-Husain al-Sajjad (a.s) gaban Ibn Ziyad, inda Ibn Ziyad din ya dubi Zainab, 'yar'uwan Husaini (a.s) wacce kuma ta dau tuta da kuma nauyin isar da sakonsa iya tsawon rayuwarta, ya ce mata:

"Godiya ta tabbata ga Allah da Ya wulakanta ku, Ya kashe ku da kuma bayyanar da ikirarinku na karya(7)".

Nan take Zainab ta mayar masa da kakkausar martani da ya jijjiga duk wadanda suke wannan fada, inda ta ce:

"Godiya ta tabbata ga Allah da Ya karrama mu da Annabinsa Muhammadu (s.a.w.a), Ya kuma tsarkake mu tsarkakewa(8), sannan kuma ya wulakanta fasiki, fajiri wanda ba shi daga cikinmu".

Sai Ibn Ziyad ya ce: "Ya ya kika ga yadda Allah Ya yi da iyalanki?". Sai ta ce:

"Allah Ya rubuta musu mutuwa, don haka suka gaggauta zuwa makomarsu, kuma da sannu Allah Zai tada kai da su, kuma za ka amsa tambayoyi a gabanSa(9)".

Haka dai maganganu masu zafi suka ci gaba da fitowa daga bakin Zainab da Ibn Ziyad har lokacin da aka zo da Aliyu bn Husain al-Sajjad (a.s) don tsayawa gaba ga Ibn Ziyad. Sai Ibn Ziyad ya tambaye shi: 'Kai wane ne?', sai Imam Sajjad (a.s) ya amsa masa da cewa:

"Ni ne Aliyu bn al-Husain".

Sai Ibn Ziyad ya sake tambayarsa: "A'a ashe Allah bai kashe Aliyu bn Husain ba?, nan take sai al-Sajjad (a.s) ya mayar masa da martani da cewa:

"Lalle ina da wani kani da ake kiransa shi ma Aliyu, amma mutanen sun kashe shi".

Sai Ibn Ziyad ya ce: "A'a Allah ne dai Ya kashe shi", nan take sai al-Sajjad ya mayar masa da martani:

"A'a, Allah Yana daukan rai ne lokacin mutuwarta".

Wannan kalami na al-Sajjad dai ya bata wa Ibn Ziyad rai, don haka sai ya dubi sojojinsa yana ce musu: 'Ku sare kansa'. Ganin haka sai Zainab ta zabura ta ce:

"Ya Ibn Ziyad zubar da jininmu ya ishe ka haka nan, wallahi ba zan rabu da shi ba, idan har za ka kashe shi sai dai ni ma ka kashe ni tare da shi(10)".

Ibn Ziyad dai ya amince da wannan bukata ta Zainab, don haka sai ya fita ya tafi masallaci don yin jawabi ga mutane da kuma sanar da su batun kashe Husain (a.s) da kuma 'nasarar' da Yazid ya samu. Daga cikin wadanda suke gurin har da Abdullah bn Afif al-Azdi(11) wanda kuma ya ji shi yana cewa: "Godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya bayyanar da gaskiya da ma'abutanta da kuma ba wa Amirul Muminina Yazid da 'yan kungiyarsa nasara, Ya kuma wulakanta makaryaci dan makaryaci Husain bn Ali da 'yan shi'ansa(12)".

Wannan kalami dai ya bata wa Abdullah rai don haka sai ya mike don fuskantar Umayyawa duk kuwa da karfin takobi da bulali da suke da shi, yana mai cewa: "Ya Ibn Marjana, kai da babanka ne makaryaci kuma dan makaryaci da kuma wanda ya dora ka akan karagar mulki da kuma babansa. Ya Ibn Marjana, shin za ka kashe 'ya'yan Annabawa ne sannan ka yi magana da kalaman masu gaskatawa(13)".

Wannan kalami na Abdullah dai ya yi girma wa Ibn Ziyad da kuma bata masa rai alhali kuwa ga shi nan yana cikin giyan mulki, babu wani abin da kawai zai sa ya huce face dai ya kashe shi, don haka sai ya ba da umarnin a kashe shi. To sai dai kuma hakan bai samu ba don kuwa kimanin mutane dari bakwai daga cikin kabilar su Abdullah din sun mike da kuma nuna rashin amincewa da hakan.

To amma Ibn Ziyad dai bai hakura, don sai da ya aike da sojojinsa cikin dare suka tafi gidan Abdullah bn Afif din suka fito da shi, suka kashe shi da kuma tsire gawarsa. Ta haka ne dai ya samu ya yi shahada yana mai jaddada kalmar gaskiya ga ja'irin shugaba.

Wannan gaba da kiyayya ta Ibn Ziyad dai ba ta kare ba, face dai sai da ya fito garin Kufa a rana ta biyu yana yawo da kan Husaini (a.s) a kan titunan garin, yana mai tsoratar da mutanen garin da kuma raunana ruhin masu son yi masa tawaye. Daga nan aka dawo da wannan kai mai albarka zuwa fada, don wucewa da shi zuwa Sham a kan mashi mai tsawo(14).

Haka dai aka wuce da wadannan kawuka, na Husain (a.s) na gaba kana sauran kuma suna baya suka keta hamadan kasar Iraki. A baya gare su kuma ga Zainab (a.s) wacce ta karbi tutan wannan yunkuri tun daga ranar da aka kashe Husaini (a.s). Kamar yadda kuma sauran mata da yara da Aliyu bn Husaini (a.s) wanda yake cikin sarka tun daga kafarsa har wuya(15) suke biye, an dora su dukkansu akan rakuma marasa sirdi(16).

Haka dai aka wuce da wadannan kawuka da kuma fursunonin yakin zuwa Damaskus babban fadar gwamnatin Umayyawa, bisa umarnin Yazid bn Mu'awiyya cikin wasikar da ya aike wa Ibn Ziyad yana mai ce masa 'ka gaggauta aiko da fursunonun yakin zuwa wajena(17), ta hakan kuwa yana so ne ya bayyanar da tsananin kiyayyarsa ga Iyalan Manzon Allah (s.a.w.a) da za su tsaya a gabansa alhali suna cikin mawuyacin hali.




____________
(1)- Wannan ibara ce da take nuni da irin ha'inci da rashin cika alkawarin da mutanen Kufan suka yi.
(2)- Tsiron da ke cikin bola: Duk tsiron da ke rayuwa cikin najasar dabbobi, zahirinsa na da kyau to amma jijiyoyinsa suna cikin kazanta da kashi dabbobi.
(3)- Azurfan da take cikin kabari, zahirinta na da haske amma babu komai a kasanta in ban da mutuwa. Hakan gugan zana ne da ke nufin ha'inci.
(4)- Wannan huduba tana cikin Maktal al-Husaini na al-Khawarizmi, juzu'i na 2, shafi na 40-42.
(5)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 243, Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 349 da kuma Ibn Kathir, juzu'i na 8, shafi na 190.
(6)- Arayin gidan Manzon Allah (s.a.w.a) sun iso garin Kufa ne daga Karbala rana ta biyu bayan isowar kan Husaini (a.s) ne.
(7) - Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 244.
(8)- Anan tana nuni ne da ayar nan mai girma ta cikin Suratul Ahzab 33:33, inda Allah Ya ke cewa: "Allah kawai na nufin ya tafiyar da kazamta ne daga gare ku, Ya ku Mutanen babban gida, Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa".
(9)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 244.
(10)- Kamar na sama.
(11)- Yana daga cikin mabiya Imam Ali (a.s) da kuma Ahlulbaiti.
(12)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 244.
(13)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafin 351, da Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 83, haka nan kuma al-Kufi cikin littafinsa Al-Futuh ya kawo wani abu daga cikin labarin al-Azdi da kuma yadda ya yi shahada, dubi juzu'i na 3, shafi na 144 zuwa gaba.
(14)- An ba wa Jazr bn Kais nauyin daukan kan Husaini (a.s) da sauran kawukan sahabbansa daga Kufa zuwa wajen Yazid bn Mu'awiyya a garin Damaskus.
(15)- Ibn Athir cikin al-Kamil fi al-Tarikh, juzu'i na 4, shafi na 83.
(16)- Ibn Athir cikin al-Kamil fi al-Tarikh, juzu'i na 4, shafi na 83 da kuma A'atham al-Kufi cikin al-Futuh juzu'i na3, shafi na 147.
(17)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir juzu'i na 4, shafi na 84 da kuma Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi 354.