IMAM HUSAINI (A.S) A MADINA

Tun farko dai Imam Husaini (a.s) ya fahimci makircin Umayyawa, ya riga da ya san cewa akwai wani babban bala'i da yake gaf da fadawa al'umma. Don haka nauyin shari'a da ke kansa yana tunkuda shi, a matsayin shugaban al'umma, na ya mike, musamman ma saboda la'akari da cewa a halin da ake ciki al'ummar ba ta da wani wanda zai 'yanto ta in ba shi ba. Don haka zamansa a Madina ya zamanto ba zai kasance mai amfanarwa ba, don kuwa yanayi na siyasa ya riga da ya lalace haka nan kuma al'umma suna cikin damuwa da dimuwa, haka nan kuma tuni an yi watsi da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Imam Hasan (a.s) da Mu'awiyya, wacce Mu'awiyya ya sa kafa ya shure ta. A bangare guda kuma ga Walid da Marwan nan suna ta matsa masa lamba don ya yi mubaya'a wa Yazid, don kuwa a karo na biyu sun sake aiko masa da wasu mutane biyu suna kiransa da ya halarci fada, inda ya amsa musu da cewa:

"Ku bari gobe ni da ku za mu ga abin da zai faru(1).

Don haka ne sai Imam Husaini (a.s) ya yanke kudurin daukan matakin da ya dace cikin gaggawa kan yanayin siyasar da ake ciki mai hatsarin gaske wanda ya samo asali bayan darewar karagar mulkin musulmi da Yazid ya yi, wanda hakan, a karo na farko, ya saba wa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Imam Hasan (a.s) da Mu'awiyya. A mataki na biyu kuma hakan ya saba wa tafarkin da musulmi suka sani kuma suka zaba, sannan kuma da rashin cancanta da Yazidu yake da shi na darewa kan karagar mulkin musulmi a mataki na uku, sannan a mataki na hudu kuwa hayewa kujerar ikon musulmi da 'yan gidan Bani Umayya suka yi, haka nan kuma a mataki na biyar shi ne irin kaucewa tafarkin Musulunci, adalci da kuma daidaito tsakanin al'umma da kuma yin karen tsaye wa doka da oda. Irin wadannan abubuwa ne dai suka sanya Imam Husaini (a.s) ya kuduri aniyar tafiya birnin Makka don tabbatar da al'amurra bisa tsari da kuma shiryawa fuskantar wannan haramtacciyar hukuma.

Don haka a dare na biyu na ganawar da aka yi tsakanin Imam Husaini (a.s) da Walid, gwamnan Madina da Marwan bn Hakam, daya daga cikin jiga-jigan mulkin Umayyawa a Madina kana kuma mai tsara musu abin da za su yi, Imam Husaini (a.s) ya fara shirya tsarin da ya dace, inda ya tara iyalansa da sahabbansa suka kama hanyar garin Makka. Daga nan ne dai aka haifar da matakin farko na wannan babban yunkuri, haka nan kuma kogin jini ya fara gudana duk tsawon tarihi. Ta haka ne Imam Husaini (a.s) ya fara wannan tafarki nasa yana mai cike da sanin cewa al'umma ta riga da ta shiga cikin wani irin muwayacin hali na siyasa da ci gaba, haka nan kuma Umayyawa sun riga da sun kame al'amurra, don haka akwai bukatar ya motsa lamiran al'umma da kuma zukatansu a siyasance.

Hakika babu wanda zai iya haifar da manyan lamurra da canje-canjen siyasa in ba gwarzayen shuwagabanni ma'abuta akida wadanda suke da matsayi a zukatan al'umma da kuma shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici ba. A wancan lokacin kuwa babu wani mutum da ya mallaki irin wadannan siffofi in ba Imam Husaini (a.s) ba, don ya riga da ya san yana da karfin da zai iya jijjiga gwamnatin Umayyawa da kuma zaizayar da kujerar mulkin Yazid. Ya riga da ya san cewa yana iya haifar da abubuwa guda biyu, ko dai nasara ko kuma shahada, kuma share fagen yin jihadi da yunkuri akan azzalumin sarki ga al'umma. Idan har ya samu nasara, to zai tabbatar da adalcin Musulunci, idan kuwa ya yi shahada, to jininsa zai ci gaba da gudana cikin magudanan rayuwa da kuma haifar da yunkuri da kuma sayar da lambunan shahada.

Wannan tawaga maras yawa, mai cike da kuduri da sadaukarwa, wacce Imam Husaini (a.s) ya fito da ita daga birnin Kakansa Annabi Muhammadu (s.a.w.a) zuwa birnin Makka don tabbatar da tafarkinsa da kuma sakon Musulunci mai tsarki, ta riga da ta tsara tafarkin na siyasa da kuma sanar da akidarta daga jiga-jigan addinin Musulunci. Haka nan kuma ta tsara yadda ya kamata a yi mu'amala da ja'irin shugaba kana azzalumi. Ta haka ne ya tabbatar da mafarin gwagwarmaya da yunkuri da halalcin hakan a karon farko cikin tarihin Musulunci wajen fuskantar ja'irar gwamnati.

A wannan lokaci Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) sun taru a bayan Imam Husaini (a.s) suka kama wannan hanya(2) mai nisan gaske. Imam Husaini (a.s) ya kama wannan hanya ne tare da 'yan'uwansa, 'ya'yansa, 'ya'yan dan'uwansa da kuma mafi yawa daga cikin Ahlulbaiti, in ban da Muhammad bn Hanafiyya, wanda saboda girman wannan lamari da kuma galabar da son da yake wa Husaini (a.s) ta yi masa ya sa har ya tsaya yana ba shi shawara da cewa:

"Ka guji mika mubaya'arka ga Yazid, ka kuma nisanci garuruwa gwagwadon iyawanka, daga nan ka aika da manzonka ga jama'a da su biyo ka. Idan har mutane suka mika maka mubaya'arsu, to ka gode wa Allah a kan hakan, idan kuwa suka mika ta ga waninka, to Allah ba zai rage maka komai daga addininka da kuma hankalinka ba, haka nan kuma mutumci da daukakarka ba za su tafi ba saboda hakan. Ni ina tsoron kada ka shiga wani gari sannan a sami sabani tsakanin mutanen garin a kanka; wasu su kasance tare da kai wasu kuma a kanka. Za su yi fada tsakaninsu kuma ka kasance abin nufi ga kawukan masunsu. Ta haka sai ya zamanto mafi daukakan al'umma, ta bangare uwa da uba, shi ne zai kasance wanda za a zubar da jininsa kuma wanda za a wulakanta iyalansa…". Daga nan sai Imam Husaini (a.s) ya ce masa: "To ina zan je Ya dan'uwana?". Sai ya ce masa: "Ka tafi Makka ka zauna a can, idan har gurin ya kasance amintacce gare ka, to zai kasance maka tafarkin isa ga burinka. Idan kuwa har gurin bai kasance haka ba gare ka, to ka tafi cikin hamada da kuma duwatsu, kana mai tafiya daga nan zuwa can don ka ga yadda halayen mutane suke dangane da wannan al'amari. Hakika za ka dau matsaya da yanke hukumci ne a lokacin da kake fuskantar al'amur-ra kai tsaye, lamurra za su kasance maka da sauki sama da idan kana dubinsu ba kai tsaye ba".

Sai Imam Husaini (a.s) ya ce masa: "Ya dan'uwana! Hakika ka ba ni shawara kuma ka nuna damuwarka, ina fatan wannan shawara taka ta kasance daidai, insha Allah".

Daga nan sai ya shiga cikin masallaci.

Shi ma a nasa bangaren, Umar bn Ali bn Abi Talib (kanin Imam Husaini) ya zanta da shi kan wannan yunkuri nasa, Sayyid Ibn Tawus ya nakalto cewa: Wasu jama'a sun bayyana min cewa, suna masu ruwaito wa daga Umar, wanda ya kawo a karshen littafinsa na al-Shafi yana mai komar da maganar zuwa ga kakansa Muhammad bn Umar cewa: "Na ji babana, Umar bn Ali bn Abi Talib (a.s) yana zantawa da baffanina iyalan gidan Akil cewa: Lokacin da dan'uwana Husaini ya ki amincewa da yin bai'a wa Yazid a Madina, sai na tafi wajensa na same shi shi kadai, sai na ce masa: In kasance fansanka Ya Baban Abdullah! Dan'uwanka Abu Muhammad al-Hasan ya gaya min cewa babansa (a.s) ya ce masa..., daga nan sai na fara kuka har ana jin sautina. Sai ya rungume ni yana mai cewa: Ya gaya maka cewa za a kashe ni ko? Sai na ce: Allah Ya tsare ka daga haka, Ya kai dan Manzon Allah. Sai ya ce min: Ina rokonka don mahaifinka, ya ba ka labarin za a kashe ni ne? sai na ce masa: Eh, to amma mai zai hana ka yin musu bai'ar? Sai ya ce min: Babana ya gaya min cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya ba shi labarin kashe shi da za a yi da kuma ni, kuma cewa kabarina zai kasance kusa da nasa ne, shin kana tsammanin ka san abin da ban sani ba ne? lalle har abada ba zan aikata haka ba. Babu makawa Fatima za ta kai kukanta ga mahaifinta kan irin mummunar mu'amalar da al'ummarsa suka yi ga zuriyarta, kuma babu wani mutumin da zai shiga aljanna alhali yana cutar da zuriyarta(3)".

A wannan lokaci dai babu wani abin da ya saura wa Imam Husaini (a.s) face barin birnin Madina da kuma bayyana wa al'umma wannan kuduri nasa. Hakika bai ji wani rauni ba wajen ci gaba da wannan tafarki nasa duk kuwa da nuna damuwar da wasu magoya bayansa suka yi na cewa za a kashe shi, amma dai haka ya tsaya kyam kamar dutse.

An ruwaito cewa Ummu Salama, matar Manzon Allah (s.a.w.a) ta zo gurinsa (Husain) tana shawartarsa da ka da ya fita, ta ce masa ta ji kakansa Manzon Allah yana cewa za a kashe shi. Sai ya nemi uzuri daga gare ta yana mai cewa: "Ya mahaifiyata, na san cewa za a kashe ni". Haka nan ma Abdullahi bn Umar bn al-Khattab ya zo wajensa yana bukatarsa da ya sake tunani kan fitarsa daga Madina ya kuma yarda ya yi mubaya'a wa Yazid, amma dai Imam Husaini (a.s) ya ki amincewa da wannan bukata, don kuwa babu yadda za a yi ya yi shiru kan irin zaluncin da Umayyawa suke yi wa al'umma, don haka sai ya ce masa:

"Ya Aba Abdurrahman! Ashe ba ka san cewa rayuwa ba ta da wata kima a wajen Allah ba, ta yadda har za a mika kan (Annabi) Yahya bn Zakariyya ga wata karuwa daga cikin karuwan Yahudawa ba? Hakika Allah ya jinkirta wa Yahudawa ne bai gaggauta saukar musu da azaba ba(4)".




____________
(1)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 16.
(2)- Imam Husaini (a.s) ya kama hanyar garin Makka ne a ranar uku ga watan Sha'aban shekara ta 60 bayan hijira. Shaik al-Mufid a cikin littafinsa al-Irshad ya bayyana cewa Imam Husaini (a.s) ya bar Madina ne daren Lahadi kwanaki biyu kafin mutuwar watan Rajab, shekara ta 60 B.H.
(3)- Maktal al-Husain na Ibn Tawus, shafi na 12.
(4)- Kamar na sama, shafi na 14.