CIKIN HARAMIN AMINCI

Haka Husaini (a.s) ya isa birnin Wahayin Ubangiji da kuma aminci, wato birnin Makka inda ya sauka a gidan Abbas bn Abdul Mutallib don ci gaba da yunkurinsa na siyasa karkashin inuwar Dakin Allah Mai Alfarma.

Wannan isowa garin Makka dai da Imam din ya yi yana cike da abubuwan ban al'ajabi, saboda irin tarbar da mutanen Makka da kuma wadanda suka zo Umra suka yi masa suna cike da farin ciki da annashuwa. Nan take labarin isowar Imam Husaini (a.s) garin Makka da kuma fitarsa daga Madina bugu da kari kan kin amincewar da ya yi na yin mubaya'a wa Yazid ya yadu tsakanin al'umma. Isar wannan labari ke da wuya kuwa, sai ga tawagogi na jama'a da kuma wasiku suna isowa zuwa gare shi daga bangarori daban-daban suna masu mika mubaya'arsu gare shi da kuma kira gare shi da ya jagorance su don yin bore wa wannan azzalumar hukuma ta Yazid da kuma kawo karshenta bugu da kari kan kwance bai'ar da suka yi masa wacce ta kasance ne bisa tilasci da kuma tursasawa, wanda hakan ya saba wa shari'a ta Musulunci wajen zaben shugaba.

Don haka aka fara shirye-shiryen matakin farko na wannan yunkuri a bangarorin daban-daban na duniyar musulmi, inda al'ummomi sukan taru don tattaunawa kan wannan lamari. Hakika akwai wasu manufofi cikin wannan hijira ta Imam Husaini (a.s) daga Madina zuwa Makka, da suka hada da:

1- Jan hankulan al'umma, wayar musu da kai da kuma motsa lamirinsu don su fahimci dalilin zaban hakan.

2- Wayar da kawuka da kuma tuntuni kan yanayin siyasa da ake ciki karkashin irin koyarwa da ka'idoji na Musulunci da kuma yadda ya kamata hukuma ta kasance.

3- Tsara hanyoyin da za a bi wajen jagorantar al'um-ma don fuskantar wannan ja'irar hukuma tare da la'akari da lokaci, waje da kuma hanyoyin da za a bi wajen cimma wannan manufa.

4- Kaddamar da yunkurin da kuma sanar da faduwar hukumar zalunci ta Yazid da kuma kafa hukumar da ta dace da koyarwar Alkur'ani mai girma da Sunnar Manzon Allah (s.a.w.a) karkashin jagorancin Husaini (a.s).

Babu shakka, dukkan wadannan abubuwa kuwa muna iya ganinsu a fili cikin rubuce-rubuce da wasikun da Imam Husaini (a.s) ya aika da su da kuma jawabai da amsoshin tambayoyin da ya amsa a lokacin da jama'a suka tambaye shi kan irin wadannan mas'aloli.

Daga cikin irin sakamako mai kyau da hakan ya haifar kuwa sun hada har da boren da mutanen Iraki suka yi, helkwatar yunkurin siyasa na mabiya Ahlulbaiti (a.s) a wancan lokacin, da kuma irin kiran da suka yi wa Imam Husaini (a.s) na ya zo ya jagorance su. A wancan lokacin manyan shuwagabannin masu boren daga cikin mabiya Imam Husaini (a.s) a garin Kufa sun taru ne a gidan Sulaiman bn Sard al-Khuza'i, don tattaunawa kan yadda yanayin siyasa da zamantakewa ya ke, da kuma mutuwar Mu'awiyya da mika ragamar jagorancin al'umma da aka yi wa Yazid, bugu da kari kan wannan yunkuri na Imam Husaini (a.s) da kuma barinsa garin Madina zauwa Makka, kin mubaya'ar da ya yi wa Yazid da kuma sanarwar fuskantar ma'abuta hukumci na wancan lokaci da ya yi. A wannan taro dai Sulaiman bn Surd al-Khuza'i, ya gabatar da wani jawabi inda yake cewa:

"Yanzu dai ga shi Mu'awiyyah dai ya mutu, Husaini kuma ya ki mika mubaya'arsa ga wadannan jama'a (Umayyawa), kuma a halin yanzu ma yana Makka, to ku 'yan shi'ansa kuma 'yan shi'an mahaifinsa ne. Idan har kun san cewa za ku iya taimakonsa da kuma yakan abokan gabansa, kuma za mu ba da rayuwanmu saboda shi, to ku rubuta masa da kuma sanar da shi hakan, amma idan har kuna tsoron rashin nasara da kuma rauni, to ka da ku sanya shi rasa ransa". Sai suka ce: "A'a, wallahi za mu yaki abokan gabansa, kuma za mu ba da rayukanmu saboda shi". Daga nan sai ya ce musu; "To ku rubuta masa". Sai kuwa suka rubuta masa cewa:

"Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai, amincin Allah ya tabbata a gare ka. Lalle muna gode wa Allah Madaukakin Sarki wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi. Bayan haka, muna gode wa Allah da ya kaskantar da makiyinka, azzalumi, wanda ya zalunci al'umma, ya hana ta hakkokinta, ya kwace mata dukkan ganimarta ba tare da yardarta ba, haka nan kuma ya kashe mafiya daukaka daga cikinta kuma ya bar mafi sharrin cikinta. A halin yanzu ba mu da wani shugaba a tare da mu, don haka ka zo gare mu ko watakila Allah Madaukakin Sarki zai hada mu karkashin gaskiya dalilinka. A halin yanzu Nu'uman bn Bashir shi ne ya ke gidan gwamnati (yake rike da al'amurra), to sai dai ba ma haduwa da shi a sallar juma'a ko kuma idi, idan har mun tabbatar cewa za ka zo to za mu kore shi daga garin zuwa Sham, idan har Allah Ya so. Amincin Allah ya tabbata a gare ka".

Daga nan sai suka ba wa Abdullahi bn Sab' al-Hamdani da Abdullahi bn Wal wannan wasika ya kai Imam Husaini (a.s), kana bayan kwanaki biyu kuma suka sake rubuta wata wasikar, daga nan kuma wasu mutane kimanin 250 kuma suka rubuta wasu wasikun zuwa ga Imam Husaini, daga nan kuma suka sake aikawa da wani manzo zuwa gare shi suna kiransa da ya iso gare su. Daga nan kuma sai Shabath bn Rib'i, Hajjar bn Abjur, Yazid bn al-Harith, Yazid bn Ruwaym, Urwah bn Kays, Umar bn al-Hajjaj al-Zubaidi da Muhammad bn Umayr al-Tamimi suka rubuta masa wasiku suna kiransa da ya iso zuwa gare su(1).

Haka wasiku suka dinga zuwa daga Kufan zuwa ga Imam Husaini (a.s) dukkansu kuwa abu guda suke dauke da shi: "A halin yanzu ba mu da shugaba, don haka ka iso zuwa gare mu, ko watakila Allah Ya hada mu a kan gaskiya (shiriya) a dalilinka. Wasu wasikun kuma suna dauke da cewa: "Jama'a dai suna jiranka, ba su da wani mutum a zuciyarsu in ba kai ba, don haka ka gaggauta, gaggautawa".

Daga nan sai Imam Husaini (a.s) ya rubuta wasika ga mutanen Kufan yana kiransu da su tsai da magana guda kana kuma su cika alkawari, don kuwa Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) suna da mummunan tajruba dangane da mutanen Irakin saboda abin da suka yi wa Imam Ali (a.s) da kuma dansa Hasan. Don haka ya rubuta musu amsar wadannan wasiku na su ya tura musu da ita ta hanyar dan baffansa Muslim bn Akil, don ya gano masa yadda lamurra suke da kuma gane masa hakika, da kuma karba masa mubaya'a daga gare su. Ya zo cikin wasikar cewa:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Wasika daga Husaini bn Ali zuwa ga Shuwagabannin muminai da musulmi. Bayan haka, Hani da Sa'id sun kawo min wasikunku, su ne manzanninku guda biyu zuwa gare ni. Hakika na fahimci dukkanin abin da kuka ce, abin da sakonninku suka kumsa kuwa shi ne cewa; 'Ba mu da shugaba don haka ka iso zuwa gare mu, don ko ta hanyarka Allah Zai shiryar da mu zuwa ga gaskiya. Don haka ga dan'uwana nan kuma dan baffana abin yardana Muslim bn Akil na aiko shi zuwa gare ku. To idan har ya rubuta min cewa ra'ayin shuwagabanninku ya hadu kan abu guda kamar yadda manzanninku suka bayyana min kana kuma na karanta cikin wasikunku, to ba tare da bata lokaci ba zan iso zuwa gare ku, da yardar Allah. Na rantse da rayuwata, babu shugaba face wanda ya yi aiki da Littafi (Alkur'ani), mai tsaida adalci, wanda ya ke bin tafarkin gaskiya, wanda kuma ya mika kansa gaba daya ga Allah Madaukakin Sarki. Amincin Allah ya tabbata a gare ku
(2)".

A daidai wannan lokaci kuma Imam Husaini (a.s) ma yana ba wa mutanen Basra muhimmanci, inda ya rubuta musu wata wasika, da take dauke da cewa:

"Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai.
Bayan haka, hakika Allah Madaukakin Sarki Ya zabi Muhammadu a kan dukkan talikai, Ya kuma karrama shi da annabci da kuma zabansa a matsayin Manzo, daga nan kuma Ya dauke shi zuwa gare Shi bayan ya isar da sakonSa zuwa gare su. Mu dai mu ne Iyalan gidansa, waliyansa, wasiyyansa, magadansa kuma wadanda suka fi cancanta da matsayinsa daga cikin mutane. To sai dai kuma duk da haka, wadannan mutane (Umayyawa) sun tattara iko zuwa gare su, amma dai muka yi hakuri da hakan don saboda guje wa rarrabuwa da kuma son zaman lafiya, duk da cewa muna sane da cewa mu ne muka fi cancanta da wannan al'amari sama da wadanda suka yi fashinsa. Don haka ga manzona gare ku tare da wannan wasika, ina kiranku zuwa ga Littafin Allah da kuma Sunnar Annabinsa (a.s). A halin da ake ciki an wulakanta Sunna kana kuma an rayar da bidi'a, to matukar dai kuka saurari wadannan kalmomi nawa, zan shiryar da ku zuwa ga tafarkin shiriya
(3)".

Ta haka ne labarin wannan yunkuri na Imam Husaini (a.s) ya isa garin Basra, wanda ya kasance mafi girman matattara na ayyukan siyasa da wayewa a duniyar musulmi in ban da garin Kufa a wancan lokacin. Manyan masu adawa da hukumar Umayyawa suna a wannan gari na Basra ne kamar yadda kuma dukkan ra'ayin al'ummar garin yana adawa da mulkin Umayyawan, don kuwa sun fuskanci matsanancin yanayi a lokacin mulkin gwamnonin Mu'awiyya. Don haka sai aka shirya wani taro a gidan daya daga cikin matayen da suka yi tsundum cikin harkar siyasa, wacce kuma tana daga cikin mabiya Ahlulbaiti (a.s) da ake kira Mariya, mahalarta wannan taro dai sun yanke shawarar taimakon Imam Husaini (a.s) da kuma yi masa bai'a, don haka sai suka rubuta masa wannan shawara da suka yanke. Ibn Athir ya ambato batun wannan taro a cikin littafinsa al-Kamil fi al-Tarikh, inda yake cewa:

" 'Yan shi'an garin Basra sun taru a gidan wata mace daga kabilar Abdul Kais wacce ake ce ma Mariya bint Sa'ada. Ita ma ta kasance 'yar shi'a ce wacce kuma 'yan shi'an suke daukan gidanta a matsayin wajen taron tattaunawarsu. Bayan haka wani mutum wanda shi ma daga zuriyar Abdul Kais din yake mai suna Yazid bn Banit ya kuduri aniyar fita don taimaka wa Husaini (a.s), shi dai wannan mutum yana da 'ya'yaye guda goma don haka sai ya ce musu: 'wane ne daga cikinku zai fita tare da ni?, biyu daga cikinsu, wato Abdullah da Ubaidullah, suka amsa masa, kuma suka fita tare da shi, da kuma haduwa da Husaini (a.s) a Makka, daga nan kuma suka fita tare zuwa Karbala inda suka yi shahada can(4)".

Lokacin da wasikar Imam Husaini (a.s) ta shiga hannun mutanen Basra, wasu daga cikin mutanen garin sun amsa wannan kira nasa, irin su Yazid bn Mas'ud, wanda ya tara kabilar Bani Tamim, Bani Hanzala da Bani Sa'ad, ya kira su zuwa ga taimakon Husaini (a.s) da nesantar ha'intarsa. Ga kadan daga cikin abin da ya ce:

"Yazid, wanda sananne ne wajen shan giya da fajirci, ya dare kujerar halifancin al'ummar musulmi ba tare da yardarsu ba, wanda ba wani abin da ya sani na ilmi ko kuma gaskiya, kai mutum ne wanda hatta takun kafarsa ba ya iya bambancewa. Na rantse da Allah, yunkuri don fuskantarsa nesa ba kusa ba ya fi yaki da mushrikai. A bangare guda kuma, wannan dai shi ne Husaini bn Ali kuma dan Manzon Allah (s.a.w.a), ma'abucin girma da daukaka na asali wanda ba za a taba kwatanta shi ba, ma'abucin ilmin da ba ya yankewa. Lalle shi ne wanda ya fi dacewa da wannan al'amari (na jagorantar al'umma), saboda irin hidimar da ya yi wa Musulunci da kuma kusancin da ya ke da shi da Manzon Allah (s.a.w.a). Shi mutum ne mai tausayawa ga kanana kana kuma mai kyautatawa ga manya, shi madaukakin shugaba ne a wajen mutanensa, kuma Jagora ga al'umma don ya zamanto hujjar Allah ga al'umma kana kuma jan kunnuwa al'umma ta hanyarsa. Don haka kada ku rufe idanuwanku daga hasken gaskiya haka nan kuma kada ku fada cikin ramin karya da bata. Hakika Sakhr bn Kais ya shiga mawuyacin halin a yakin Jamal saboda ayyukanku, don haka ku wanke wannan (mummunan) aiki naku ta hanyar fita da kuma taimakon dan Manzon Allah (s.a.w.a). Lalle babu wani daga cikinku da zai gaza wajen taimakonsa face Allah Madaukakin Sarki ya gadar da kaskanci ga zuriyarsa da kuma karanci gare su. A halin yanzu gani nan na sanya kayayyakin yaki, a shirye nake wajen fita filin daga, lalle duk wanda ba a kashe shi ba, to lalle kuwa zai mutu, wanda kuma ya gudu ba dai zai tsere wa mutuwa ba. Ku kyautata amsa gare ni, Allah Ya yi muku rahama".

Daga nan sai Bani Hanzala suka ce: "Ya Baban Khalid, mu kibau ne cikin kwarinka kana kuma dakarun kabilarka, matukar dai ka jefa mu to kuwa za ka sami inda kake son ka samu, kuma idan har ka yi yaki da mu to za ka samu nasara. Wallahi babu yadda za ka kaddamar da yaki ba tare da mu ba, kamar yadda kuma ba za ka fuskanci wahala kai kadai ba tare da mu ba, lalle za mu taimaka maka da takubbanmu, kuma za mu kare ka da jikkunanmu. Don haka idan har ka shirya wa yakin, to bisimillah".

Daga nan sai Banu Sa'ad bn Yazid suka mike suka ce:

"Ya Baban Khalid, hakika mafi kin abu a gare mu shi ne saba maka da kuma kin yarda da ra'ayinka, lalle Sakhr bn Kais ya umarce mu da barin yaki don haka sai muka yarda da sulhu kuma muka kare mutumcinmu. Don haka ka dan ba mu lokaci don tattaunawa tsakaninmu, daga baya za mu zo maka da abin da muka tsaya akai".

Sai kuma Banu Amir bn Tamim suka mike suka ce:

"Ya Baban Khalid, mu dai mu ne Banu Amir, zuriyar mahaifinka, kana kuma halifofinka, ba za mu taba amincewa ba kan abin da ka yi fushi da shi, kamar yadda kuma ba za mu zauna a gida ba matukar dai ka kuduri aniyar fita, don haka al'amari dai yana hannunka, idan ka kira mu za mu amsa maka, idan kuma ka umarce mu za mu aikata abin da ka ce, don haka komai na hannunka".

Sai ya ce: "Wallahi ya ku Banu Sa'ad, idan har kuka aikata haka (wato kuka juya wa Husaini baya), to lalle Allah ba zai taba daga takubba a kan wuyayenku ba matukar dai kuna da takubba a hannunku".

Daga nan sai ya rubuta wa Imam Husaini (a.s) wasika, yana mai cewa:

"Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Kai, bayan haka: Lalle wasikarka ta iso kuma na fahimci abin da kake kira na zuwa gare shi na amsa kiranka da kuma ba da nawa gudummawar wajen taimakonka, hakika Allah ba zai taba barin wannan duniya ba tare da wani mutum mai aikata alheri da kuma shiryar da mutane zuwa ga madaidaiciyar hanya ba. Ku ne hujjar Allah a bayan kasa a kan bayinSa, haka nan kuma amanarSa a bayan kasa, kuma ku ne asalin reshen bishiyar Zaitun ta Muhamma-diya, shi (Annabi) ne jikin bishiyar, ku kuma ku ne rassanta. Don haka ka iso zuwa gare mu, Allah ya biya maka bukatunka. Na yi nasarar janyo hankulan Banu Tamim wajen yi maka biyayya kamar yadda mayunwacin rakumi yake sauri zuwa ga ruwa bayan wani lokaci mai tsawo na wahalar tafiya da kishin ruwa. Haka nan kuma na sami nasarar janyo hankulan Banu Sa'ad da kuma wanke zukatansu da ruwan saman da ya biyo bayan tsawa da kuma rugugi".

Lokacin da Imam Husaini (a.s) ya karanta wannan wasika sai ya ce:

"Ina rokon Allah da Ya amintar da kai ranar tsoro, Ya kuma arzurtaka da dauakaka da kuma shayar da kai ranar mafi girman kishirwa".

To sai dai kuma lokacin da Yazid bn Mas'ud ya yi shirin fita don tafiya wajen Imam Husaini (a.s), sai labari ya zo masa cewa an kashe Imam din. A bangare guda kuma Munthir bn Jarood, sai ya dauki wasikar da kuma wanda ya zo da ita ya kai ga Ubaidullah bn Ziyad, yana mai tsoron cewa kada wasikar ta kasance wani makirci ne daga Ubaidullah bn Ziyad, wanda ya ke auren 'yarsa Bahriyya. Daga nan sai Ubaidullah ya sa aka tsire wannan dan aika, kana kuma ya hau kan mimbari yana mai yin barazana da mummunar azaba ga mutanen Basra kan abin da suke yadawa da kuma kin biyayyan da suke nunawa. Bayan da gari ya waye kuma, sai ya nada kaninsa Usman bn Ziyad a matsayin gwamnan Basra, shi kuma ba tare da bata lokaci ba ya nufi garin Kufa(5).

Ta haka ne dai wannan matsaya ta fito fili, kamar yadda kuma aka gano hanyoyin da za a bi wajen kadda-mar da wannan gagarumin yunkuri, kamar yadda kuma ta hakan ne Imam Husaini (a.s) din ya dinga motsa lamiran mutane da kuma jagorantar harkar daga garin Makka cikin tsawon watannin Sha'aban, Ramalana, Shawwal, Zil Ka'ada da kuma wasu ranaku na Zil Hajji. Don haka ne ma lokacin da Muslim bn Akil, manzon Husain (a.s) ya karanta wa mutanen Kufa wasikar Imam Husaini (a.s) sai suka fashe da kuka suna kiransa da ya gaggauta isowa.

To bayan isowar dukkan bayanai masu kwantar da rai zuwa ga Imam Husaini (a.s) dangane shirin mutanen Kufa wajen goyon bayan wannan gagarumin yunkuri, sai kasar Irakin ta kasance wurin da ya fi dacewa na bayyanar da wannan yunkuri da kuma kafa gwamnatin Musulunci na hakika.




____________
(1)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 202, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, juzu'i na 4, shafi na 261, da kuma al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 20.
(2)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 204, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, juzu'i na 4, shafi na 262, da kuma al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 21.
(3)- Maktal al-Husain na al-Mukarram, shafi na 141 da 142.
(4)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 263 da al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 21.
(5)- Maktal al-Husain na Ibn Dawus, shafi na 17 zuwa sama.