FAKEWAR TAURARUWAR HUSAINI (A.S)

Kura dai ta lafa kofatan dawaki kuma sun yi shiru kamar yadda kuma aka mai da takubba cikin gidajensu kana masu kuma suka sunkuyar da kawukansu. Duniya kuma tana cikin wani irin hali na ban tsoro kamar yadda rana kuma cikin fushi ta yi yamma don faduwa. Wannan hamada ta Karbala kuma ta sunkuyar da kaitana kallon wannan mafi girman aikin zalunci da aka taba aikatawa a bayan kasa kamar yadda kuma bishiyoyin suka takura waje guda suna masu nadamar kasantuwa kusa da inda aka aikata wannan danyen aiki. Iska kuwa ta taso don rufe wadannan jikkuna masu tsarki da takubba, masu da dawaki suka yi wasa a kansu.

A daidai wannan lokaci kuwa ga Husaini (a.s), wannan ma'abucin karfafaffiyar akida, jikan Annabi kana kuma abin kauna al-Zahra (a.s), nan kwance ba tare da kai ba, an lalata jikinsa, an gutsure kansa mai tsarki, kaifin takobi ya raba tsakaninsa da jikinsa, ga jikinsa nan mai tsarki ba tare da wani tufafi ba, ba wani abin da ya rufe shi in ban da kurar filin daga da kuma albarkacin wannan jini mai tsarki. A bangare guda kuma ga wadannan mujirimai suna kallon irin wannan mummunan yanayi da ake ciki, suna tunanin kan wannan jiki mai tsarki na Husaini (a.s) da mabiyansa da suka yi shahada tare da shi.

Wannan yanayi dai ba abin kallo ba ne kamar yadda aika-aikan da aka aikata din ya yi munin gaske, jini dai sai gudu yake yi a kan kasa, jikkunan shahidai masu tsarki kuwa ga su nan a warwatse a filin daga kamar yadda taurari suke watse a sararin samaniyya. Wadannan jikkuna masu tsarki kuwa da suke watsen sun hada da na Shugaban Shahidai kana kuma jikan Manzon Allah (s.a.w.a), Husaini (a.s) da mutane sha bakwai na daga 'yan'uwa, 'ya'ya, 'ya'yan dan'uwa da baffansa da kuma wasu mutane sittin(1) daga cikin sahabbansa. A can daya bangare na wannan filin daga kuwa sansani ni ne na Imam Husain (a.s) wanda ba kowa cikinsa in ban da mata da kananan yara, sai kuma Aliyu bn Husain al-Sajjad (a.s) wanda rashin lafiyan da yake fama da shi ya hana shi fitowa filin dagan.

Daga nan kuma sai Umar bn Sa'ad, babban kwamandan wadannan sojoji ya umarci wasu mahaya daga cikin mutanensa da su yi sukuwa a kan kirji da kuma bayan Husaini (a.s), ba tare da bata lokaci ba suka amsa wannan umarni suka yi kaca-kaca da wannan jiki mai tsarki(2).

Bayan hakan kuwa sai dawakan abokan gaban suka koma kan jikkunan sauran shahidan suna sukuwa a kansu, bayan da suka gama kuma sai suka nufi sansanin Imam Husain (a.s) dake cike da mata da kananan yara.

Ganin haka sai mata da yaran suka fara ihu, suna cikin dimuwa ba su san inda za su yi ba ko kuma inda za su je su sami mafaka ba, matan suna kira zuwa ga taimako amma babu wani da zai taimaka musu, don ba abin da ake ji bayan sautin mata da yara sai karan takubba da kuma kofatan dawaki mai ban tsoro ainun.

Matan dai sai ci gaba suke yi da ihu suna neman taimako suna cewa: "Ina kake ne Ya Husaini? Ashe ba ka ga wadannan kuraye mashaya jini sun mamaye sansa-ninka ba? Ashe ba ka jin sautin kukan yara? Shin sautin mata ba ya isa zuwa gare ka ne? Ko kaddara ta raba tsakaninka da mu ne?.

Amma babu amsa, sojojin abokan gaba kuwa sai suka nufi wannan sansani na Imam Husain (a.s) suna kwace duk wani abin da suka gani a wajen mata da yaran. Suna masu fisge dan kunnen zinaren da ke kunnuwan yara da karfin gaske, kunnuwan yaran na zubar da jini, ga yaran kuma suna kuka suna neman taimakon iyayensu amma dai ba abin da iyayen za su iya musu ko kuma kare wadannan mujirimai daga aikata wannan aika-aika, don kuwa su ma ba su tsira ba, masu dukansu da bulali na yi masu kwace musu duk abubuwan da suke da shi na yi. Duk irin wannan mummunan yanayi da ake ciki, wuta kuma tana nan tana ci a wannan sansani, hayaki da bakin wutan kuwa duk sun rufe saman wannan fili na daga.

Dukkan wannan abu kuwa, wato yakin da aka yi, sace-sacen kayayyaki da kuma kame fursunonin yaki, duk an yi su ne da ranar wannan rana ta Ashura. Sojojin abokan gaban dai ba su nuna wata alamar tausayawa ga kananan yaran da suke cikin halin kunci haka nan iyaye matan da suke cikin halin dimautuwa ba.

Daga nan sai aka yanke kawukan(3) shahidan aka tsire su a kan masu sannan aka raba su ga wadannan sojoji. Sai suka kama hanya suka bar sauran jikkuna masu tsarkin a wannan fili, alhali kawukan kuma suna tsire a kawukan masu, kan Husaini (a.s) ne a gaba akan wani mashi mai tsawon gaske da Khiwalla bn Yazid al-Asbahi da Hamid bn Muslim al-Azdi suke rike da shi. Sauran kawukan kuwa an ba da su ne ga Shimr bn Zil-Jawshan, Kais bn al-Ash'ath da Amru bn al-Hajjaj, wadanda suka wuce da kawukan Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma sahabban Husaini (a.s) a matsayin wata kyauta don neman kusanci da Ubaidullah bn Ziyad, a daidai wannan lokaci kuwa ga mata da kananan yara nan suna ganin kawukan mazajensu, iyaye, 'ya'ya, 'yan'uwa, kawunnai da masoyansu a tsire suna zubar da jinin da ke rubuta wasu haruffa da za su ci gaba da zama cikin tarihi har abada.

Kafin mu yi ban kwana da wannan fili na Karbala, bari mu dan yi dubi cikin zancen wani mawaki(4) wanda bayan karni sha uku da faruwan wannan lamari ya rera wata wakar da yake siffanta wannan lamari mai tada hankali, yana mai nuna juyayinsa ga Husaini (a.s) kamar ka ce yana gefen Zainab da al-Rubab(5) ne. Bari mu ji abin da ya ke cewa:

Sun kasance cikin dimuwa ba su kula da zancensa ba,
             Face dai suka amsa masa da kibau da suka.
Lokacin da kafiran Umayyawa suka nuna fushinsu,
             Kan cewa ba a cutar da zuciyar Annabi ba.
Sai suka dirka a jikin Husaini da takubbansu,
             Inda ya kasance wajen sunkuyawar takubba.
Zuciyarsa ta takura saboda tsananin kishirwa,
             Ba don karfin halinta ba da ta fashe baki daya.
Na ji zafi saboda jikinka maras tufafi dake kan kasa,
             Wanda ba abin da ya rufe shi in ban da jini.
Fuskarsa cikin kasa, alhali idon duk mai kadaita Allah,
             Zai so jikinka ya zamanto likkafaninsa.
Na ji zafin tsire kanka da aka yi a kan mashi,
             An kumshe shi cikin wani mayafi.
Yana karanta ayoyin Littafin (Allah) a wannan hali,
             Alhali kuwa sun daga Littafin a kan mashin.
Bari Littafin Allah ya yi kuka don abin da ya same shi,
             Bari Musulunci yayi kuka saboda wannan rashi.

Haka dai al'amurra suka ci gaba da faruwa cikin bakin ciki da damuwa da daga hankali wanda tarihi bai taba ganin irinsa ba, kana kuma ya ci gaba da kasantuwa cikin tarihin har karshen duniya.

Haka dai wannan tawaga ta kayuka ta ci gaba da tsaga turbayan hamada karkashin jagorancin wadannan mashaya jini, suna bugun dawakinsu don su yi sauri, su isa Kufa don yin albishir wa shugabansu kan wannan aika-aika da suka aikata. Kan Husaini (a.s) ne a gaba sai kuma sauran kawukan mabiyansa a matsayin kyauta kana su kuma su sami nasu ladan.

Sun zubar da jinin bayin Allah, sun kashe Shugaba mai shiryarwa don su sami dan wani abu takaitacce daga la'anannen shugabansu Ubaidullah bn Ziyad.




____________
(1)- Al-Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki shafi na 193 da kuma Maktal al-Husaini na Ibn Dawus, shafi na 60.
(2)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 347 da Maktal al-Husain na Ibn Dawus, shafi na 56.
(3)- Ibn Dawus ya bayyana cewa wadannan kawuka na sahabban Imam Husain (a.s) dai guda 78 ne, inda aka raba su tsakanin kabilun da suka yi wannan aika-aika don samun kusanci da su zuwa ga Ubaidullah bn Ziyad, gwamnan Yazid bn Mu'awiyya a Kufa. Kabilar Kinda wacce Kais bn al-Ash'ath ke wakilta ta samu kawuka guda 13, Hawazin kuwa wacce Shimr bn Zil-Jawshan ke wakilta sun samu kawuka 12, Tamim kuwa 17, Bani Asad 16, Mazhaj kuwa 7 sannan sauran mutane kuma suka zo da kawuka 13. Don karin bayani dubi Maktal al-Husain na Ibn Dawus, shafi na 60 da 61. Shaikh al-Mufid ma cikin littafinsa Al-Irshad shafi na 243 ya ruwaito cewa sahabban Husaini (a.s) su 72, haka ma Dabari cikin Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4 shafi na 348.
(4)- Shi ne mawakin nan mai suna Sayyid Ridha al-Hindi.
(5)- Al-Rubab dai ita ce matar Husaini (a.s) babanta kuma shi ne Imru al-Kais kuma ita ce mahaifiyar Sukaina 'yar Imam Husain (a.s) da kuma Abdullah, jaririn nan da aka kashe ranar Ashura.