DAREN ASHURA (DAREN KARSHE)

A hakikanin gaskiya dai wannan bukata ta Husaini (a.s) na a bashi wannan dare ba wai don yin tunani kan matakin da zai dauka ba ne ko kuma ci gaba da darasin yadda yanayin yake ba ne, a'a ai tuni ya riga da ya wuce hakan, don kuwa komai dai ya riga da ya fito fili a gare shi. Face dai ya bukace ta ne don ya samu damar yin ibada da addu'oi, ban kwana da rubuta wasiyya da kuma tattanawa da iyalai, sahabbansa da kuma masoyansa, don ya riga da ya san abin da zai faru washe gari. Saboda haka ne ma ya ce wa dan'uwansa Abbas lokacin da ya sake tura shi zuwa wajen Ibn Sa'ad a karo na biyu cewa:

"Ka tafi gurinsu, idan har za ka iya ka sanya su bar mu har zuwa safiya da kuma rana, ko ma samu daman yin ibada ga Ubangijinmu cikin dare da kuma neman gafararSa, don kuwa Ya san ina son yin salla gare Shi, karatun Littafinsa da kuma yawaita addu'a da neman gafara(1)".

Wannan yanayi dai yanayi ne mai tada hankali, ga sojojin Umayyawa nan suna kewaye da Husaini tare da mabiyansa (a.s) ga mata da yara kanana daga gidan Manzon Allah (s.a.w.a) suna cikin halin tsoro da damuwa kan abin da zai faru washe gari. A waje guda kuma Husaini (a.s) yana ta kewaya tantunan yana mai tsara yadda za a kiyaye yara da mata daga hare-haren abokan gaba da suke cike da kiyayya da kuma gaba da wannan tawaga ta dakarun Musulunci.

Da yamma jim kadan kafin faduwar rana mai tsananin kuna da zafi, Imam Husain (a.s) ya tsaya gaba da mabiyansa yana mai sanar da su cewa abokan gaban fa shi suke so su kashe ba wani daga cikinsu ba, don haka kowane guda daga cikinsu yana iya amfani da duhun dare don tseratar da ransa daga kisa, to amma dukkansu suka ki amincewa da su tafi su bar shi suna masu jaddada kudurinsu na kasancewa tare da shi da kuma fada da sadaukarwa.

Dare dai ya yi kowace halitta ta nemi wajen fakewa da kuma hutawa in ban da Iyalan Manzon Allah (s.a.w.a) da masu taimaka musu (magoya bayansu), sun shafe dukkan daren ne, wasu na salla wasu kuma na addu'a, wasu kuwa suna karatun Alkur'ani da kuma neman gafarar Ubangiji, wasu kuma suna ban kwana da iyalansu da kuma gabatar musu da wasiyya, don kuwa suna ta shirin ganawa ne da Ubangijinsu Madaukaki Sarki. Har ila yau kuma suna ci gaba da gyara takubba da masunsu, haka dai suka kwana a matsayin baki na wannan kasa ta Karbala, alhali shi kuma tarihi yana jiran dakon abin da zai faru washe garin, kamar yadda takubba da masu kuma suka zamanto alkalumman da za su rubuta irin danyen aikin da aka yi na zubar da jini mai tsarki a wannan rana cikin littafin tarihi.

A wannan dare kuwa, Imam Husain (a.s) ya yi ban kwana da iyalai da masoyansa, ya ziyarci Sajjad, Zainab, Sukaina, Laila, Rabab da Bakir (a.s) yana mai isar musu da wasiyyarsa ta karshe, yana mai riko da alkawarin da yayi, ya sayar da kansa ga Allah, da kuma shawarar da ya yanke na shayar da bishiyar shiriya da imani da jininsa.

Haka dai wannan dare ya kasance, washe gari kuwa zai kasance babban abin tsoro ga Iyalan Muhammadu (s.a.w.a), don kuwa tuni dawaki da mahayansu wadanda kullum sai dada karuwa suke yi sun kewaye su, ga shi kuma fuskar Manzon Allah (s.a.w.a) ta yi nisa da su kamar yadda lamarin yake dangane da Mahaifinsu Amirul Muminina Ali(2) (a.s). Ga shi an nesanta su da birnin Madina inda kakansu Manzon Allah (s.a.w.a), Imam Hasan (a.s) da kuma Mahaifiyarsu al-Zahra suke da dawaki da mahaya(3), don haka suka kwana cikin bakunta suna masu fuskantar barazanar kisa da kamu a matsayin fursunonin yaki daga sojojin abokan gaba.

Ba da dadewa ba dai wannan dare na sulhu ya kawo karshe, wannan rana mai ban tsoro ta shigo, ranar Juma'a, Ranar Ashura, Ranar Jini, Jihadi da kuma Shahada. Wannan rana kuwa ta shigo alhali kawukan takubba da masu an shirya su don kekketan jikkunan Imam Husain (a.s) tare da mabiyansa, masoya gaskiya da tabbatar da adalci.

Daga nan sai Umar bn Sa'ad ya fara shirya sojojinsa, inda ya ba da jagorancin sashin dama na sojojin ga Amru bn al-Hajjaj, sashin hagu kuwa ga Shimr bn Zil Jawshan, sashin masu kibau kuwa ga Urwah(4) bn Kais, dakarun kasa kuwa ga Shabath bn Rib'i, sannan kuma ya ba da tutan yaki ga bawansa Duraid(5).

Imam Husain (a.s) ya kalli wadannan sojojin masu zuwa yana mai tunani kansu, sai dai kuma duk da haka yana nan tsaye kyam kamar tubali, ya riga da ya dau matsaya, sannan kuma ya wulakantar da duniya a idanuwansa kamar yadda kuma ba ya ganin girman wadannan dakaru. Sahabbansa ma haka suka kasance, kamar yadda wani mawaki ya siffanta su:

Sun sanya zukatansa a kan makamansu suna masu,
               Rige-rige wajen ba da rayukansu.

Ko da wasa dai yawan wadannan sojoji bai razana shi (Husaini) ba, kamar yadda kuma yawan makamai da karfinsu bai sa shi yin kasa a gwuiwa ko kuma raunana azamarsa ba, face ma dai hakan ya kara masa karfin gwuiwa da kuma tabbatar da ruhinsa, inda ya daga hannayensa sama cikin kaskantar da kai ga Allah Madaukakin Sarki yana ganawa da shi:

"Ya Ubangiji Kai ne abin dogaro na yayin duk wata damuwa, kuma Kai ne abin komawa ta yayin duk wata wahala, kamar yadda kuma Kai ne kariya ta kan duk wani abin da ya fado min. Shin abubuwan bakin ciki nawa ne suka raunana zukata, suka bar ni ba tare da samun wata mafita ba wajen magance su, a lokacin da abokai suka rabu dani kana kuma abokan gaba kuma suka yi farin ciki, amma kuma na gabatar maKa da kukata saboda bukatar da nake da ita gare Ka ba ga waninKa ba, sannan kuma ka fitar da ni daga cikin irin wannan hali, don kuwa Kai ne majibincin dukkan ni'imomi, kuma Ma'abucin dukkan abubuwa masu kyau kana kuma Makomar dukkan bukatu(6)".




____________
(1)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 230 da kuma Tarikh al-Ummam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 316.
(2)- Wannan waki'a ta Ashura ta faru ne a Karbala inda Husaini ya yi shahada kana kuma aka rufe shi a gurin, Karbala dai tana da nisan kilomita 75 ne daga kabarin Imam Ali (a.s) da ke birnin Najaf.
(3)- Wannan tafiya ta Husaini (a.s) daga Madina zuwa Makka kana daga nan zuwa Karbala ta dauki kimanin kwanaki talatin, wanda nisan tafiya ta kai kimanin kilomita dubu biyu.
(4)- Wasu littafan tarihin kuwa suna kiransa da Uzrah.
(5)- Wasu littafan tarihin kuma sun kira shi da Zuwaid.
(6)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 321, kamar yadda kuma Shaikh al-Mufid ya ruwaito cikin al-Irshad, shafi na 233, daga Imam Ali bn Husain al-Sajjad (a.s) wanda ya ga yakin da aka yi a Karbala din amma dai bai shiga ciki ba saboda rashin lafiya, kamar yadda kuma dansa Muhammad al-Bakir (a.s) wanda yaro karami dan kimanin shekaru 4 a lokacin yakin shi ma ya gani. An ruwaito daga Sajjad (a.s) cewa: "Lokacin da dawakai suka nufo sansanin Husaini (a.s) sai ya daga hannayensa sama yana karanta wannan addu'a".