DALILAN YUNKURIN IMAM HUSAINI (A.S)

Hakika Imam Husaini (a.s) bai boye dalilin fitarsa daga birnin Madina da kuma dalilan da suka sa ya shirya yakan Yazid ba. Ya riga da ya ba da gamsasshiyar amsa ga wadanda suke so su sani. Ya bayyana manufar wannan yunkuri nasa, da kuma tafarkin da zai bi wajen yakan wannan sabuwar gwamnati ta Umayyawa. Dukkan wadannan abubuwa dai suna cikin wasikar da ya aika wa kaninsa Muhammad bn Hanafiyyah, inda ya bayyana cewa, lalacewar yanayin siyasa, zamantakewa da akidun al'umma, bugu da kari kan nauyin da ke kansa na gyaran al'umma, su ne suka sanya shi barin Madina da kuma jagorantar wannan babban yunkuri na fada da mulkin zaluncin Umayyawa.

Wannan wasika ta sa tana nan kamar haka:

"Ni ban fito domin girman kai ko alfahari ba, ba kuma domin barna a bayan kasa ko zalunci ba. Abin da kawai ya fito da ni shi ne neman gyara a cikin al'ummar kakana, Manzon Allah (s.a.w.a.). Ina nufin yin umurni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, in kuma bi irin rayuwar kakana da babana.....(1)".

Daga nan kuma sai ya yi bayanin dalilin da ya sa yaki yarda ya yi mubaya'a wa Yazid, da cewa:

"Yazid dai lalatacce ne, mashayin giya, mai kashe rayukan da Allah Ya haramta, baya ga haka kuma yana bayyana wadannan munanan ayyuka nasa a fili. Don haka mutum kama ta ba zai taba yin bai'a wa mutum kamar Yazid ba(2)".

Hakika shari'an Musulunci ya shar'anta cewa dole duk wani shugaban da zai jagoranci al'umma ya kasance yana kula da ka'idar adalci da kuma rashin nuna bambanci. Dole ne ya ba riki shari'ar Musulunci da kuma bukatun al'umma sama da komai, ba ya halalta ya yi sako-sako da dokokin Allah. Dole ne ya nesanci zalunci da kuma yin amfani da matsayinsa wajen tara kudi, jin dadi da kuma wulakanta mutane, ko kuma fifita na kusa da shi ko kuma danginsa.

Sanannen abu ga Imam Husaini (as.) da kuma sauran al'umma cewa Yazid mutum ne da bai cancanci ya shugabanci al'umma ba, don kuwa mutum wanda babban burinsa shi ne yada fasadi a bayan kasa da kuma zaluntar bayin Allah. Yazid mutum ne da ya nitse cikin sabon Allah da suka da neman mata, shan giya wasa da birrai da dai duk sauran nau'o'i na wargi da wasa.

Baya ga haka kuma sanannen abu ne cewa dukkan al'umma sun yarda da cewa bai kamata a ba da shugabanci ga mutumin da ya rasa siffa wacce za ta kasance abin koyi ga al'umma ba cikin ayyuka da mu'amalolinsa, sannan kuma dole ne ya kasance mutum masanin siyasa da zamani. To idan duk mun fahimci haka, to ya ya za mu yi tsammanin mutum kamar Imam Husaini (a.s) - wanda ya kasance jika ya ke wa Manzon Allah (s) kana kuma dan Fatima da Aliyu (a.s), sannan kuma burin dukkan al'umman musulmi - zai mika kai ga wannan fajiri Yazid dan Mu'awiyyah.

To saboda wadannan dalilai ne ya sa Imam Husaini (a.s) ya ki ya yi bai'a wa Yazid, kuma ma ya dau makami don yakansa, kamar yadda ya bayyana wa mabiyansa a duk inda ya yada zango don su fahimci matsayarsa ta siyasa da kuma irin halin da ake ciki.

A cikin wasikarsa ga mutanen Kufa, Imam Husaini (a.s) ya bayyana musu siffofin shugaba na kwarai, don ya wayar musu da kai da kuma bayyana musu wane ne ya cancanci ya zamanto shugaba. A cikin wasikar ya bayyana musu cewa:

"...Na rantse, shugaba shi ne wanda ya yi shari'a da Littafin Allah, wanda ya ke gudanar da gaskiya da kuma adalci, wanda kuma yake bayyanar da hakikanin addinin gaskiya, sannan kuma wanda ya ba da kansa don Allah(3)".

Haka nan kuma ya rubuta wa manyan shuwagabanni Basrah; wato Malik bn Mas'ma' al-Bukra, Al-Ahnaf bn Kais, al-Manzar bn al-Jarud, Mas'ud bn Amru, Kais bn Haitham da Amru bn Ubaid bn Mu'ammar wasika inda ya ke cewa:

"...Ina kiranku zuwa ga kiyaye Littafin Allah da Sunna ManzonSa (s) da kuma aiki da su. A halin yanzu an ajiye Sunnar Annabi (s) a gefe kana kuma an raya bidi'a. Matukar kuka riki wannan kalami nawa, to ni kuwa zan ja ku zuwa ga hanya madaidaiciya. Amincin Allah ya tabbata a gare ku(4)".

Hakika Imam Husaini (a.s) yana dubin gwamnati, siyasa, al'umma da kuma shugabanci ne a bisa mahanga ta Alkur'ani mai girma. To amma shi Yazid, sabanin haka, yana dubin wadannan al'amurra ne a bisa mahangar zalunci da babakere. Shugabanci, a wajen Imam Husaini (a.s), kamar wata mota ce wacce za a sanya mutane a kan tafarki shiriya da kuma isa zuwa ga hallarar Ubangiji, tafarki ne da sanya mutane a kan dokokin sama don su gina rayuwarsu akan tafarkin gasikya da kuma kyawawan dabi'u.

A fahimtarsa, gwamnatin Musulunci tana karkashin kulawa ne na Musulunci da dokokinsa, wanda ita ta hakan ne za ta tsara nata dokoki da kuma ka'idoji. Haka nan kuma jami'an gwamnatin ta Musulunci, suna da alhakin kare manufofin al'umma da jin dadinsu, a takaice dai za su kasance abin tambaya a gaba ga Allah da kuma al'umma, don da man a zabe su ne a matsayin masu hidima wa al'umma, ba masu zalunta da kuma wulakanta su ba.

Babu shakka, idan muka yi dubi da kyau cikin maganganu, wasiku da kuma tattaunawan da Imam Husaini (a.s) ya yi, bugu da kari kan irin yanayi na siyasa, tattalin arziki da zamantakewa da ake ciki a wancan lokacin, to lalle za mu iya fahimtar wasu al'amurra kamar haka:

(1). Hukumar zaluncin Umayyawa ta wancan lokacin tana zaluntar al'umma da kuma amfani da iko da karfin mulki ta hanyar da ba ta dace ba. Wasu 'yan tsirarru ne kawai suke amfanuwa da dukiyar al'umma. Wata jam'iyya ta kabila guda ce kawai take wasa da mulki, wannan jam'iyya kuwa ita ce jam'iyyar Umayyawa. Ta kasance tana wasa da mulki da dukiyar al'umma, alhali kuwa mafi yawan al'umma an haramta musu jin dadin rayuwarsu, kai a takaice dai gwamnati da kuma dukiayr al'umma sun zamanto kaya ne kawai na Umayyawa da masu goya musu baya.

(2). Kisan gilla, zalunci da ta'addanci sun zama ruwan dare game duniya.

(3). Ana wasa da dukiyar al'umma, kuma da dama daga cikin jami'an gwamnatin wancan lokacin ba su cancanci su zamanto masu kula da harkokin al'umma ba, saboda rashin cancanta.

(4). Lalacewar dabi'a ta zamanto wani lamari da babu mai inkarinsa, rashawa da cin hanci sun game ko ina, musamman ma a bangaren jami'an gwamnati.

(5). Ba a girmama duk wata doka, ta Ubangiji ce ko kuma ma ta 'yan'Adamtaka. Son rai da bukatun masu mulki shi ne ke kan gaba da shari'a da dokokin Ubangiji.

(6). Gwamnati ta samar da kuma daukan nauyin wasu mutane marasa tsoron Allah don lalata hadisan Ma'aiki (s) da kuma kirkiro wasu darikoki irin su al-Mujabbira (masu akidar cewa dukkan ayyukan 'yan'Adam Allah ne ya ke tilasta musu yin su) da dai sauransu don biyan bukatun Umayyawa masu mulki da kuma kare irin ayyukan da suke yi.

(7). Da dai abubuwa makamantan hakan, wadanda lokaci ba zai ba mu daman kawo su ba.

To amma hakika, tarihi ya bayyana mana irin lalacewar da al'umma suka yi da kuma rashin kula da dokokin Allah musammam ma daga wajen masu mulki. A saboda, muna iya ganin wajibcin da ya hau kan Imam Husaini (a.s) na ya mike tsaye wajen kawo gyara da kuma kawar da irin wannan karen tsaye da ake wa dokokin Allah da kuma na zamantakewa. A hakikanin gaskiya a irin wannan yanayi babu wani abin da ya hau kan Imam Husaini (a.s) da kuma dukkan bayin Allah face su mike tsaye don kawar da wannan mummunan yanayi.

A matsayin misali, mu dauki yanayin tsaro na al'umma kawai, wanda Alkur'ani mai girma ya ba shi muhimmanci cikin fadin Madaukakin Sarki cewa:

( فَلْيَعْبُدُ رَبَّ هَذا الْبَيْتِ الذي أطْعَمَهُمْ مِنْ جُوعٍ وَ امَنَهُمْ مِنْ خوْفٍ ) (...lalle ne wanda ya kashe rai ba da wani rai ba, ko barna a cikin kasa, to kamar ya kashe mutane duka ne, kuma wanda ya raya rai, to, kamar ya rayar da mutane ne gaba daya. Kuma lalle ne, hakika, ManzanninMu, sun je musu da hujjoji bayyanannu, sa'an nan kuma lalle ne, masu yawa daga gare su, a bayan wannan, hakika masu barna ne a cikin kasa). (Suratu Kuraish: 106: 3-4)

مَنْ قَتَلَ نَفْسًا بِغَيْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِي الأرْضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ النَّاسَ جَميعًا ومَنْ أَحْياها فَكأَنَّمَا أحْيَا النَّاسَ جَميعًا ولَقَدْ جاءتْهُمْ رُسُلُنا بالبَيِّناتِ ثُمَّ إنَّ كَثيراً مِنْهُمْ بَعْدَ ذالكَ في الأرْضِ لَمُسْرِفُونَ

"....Lalle ne wanda ya kashe rai ba da wani rai ba, ko barna a cikin kasa, to kamar ya kashe mutane duka ne, kuma wanda ya raya rai, to, kamar ya rayar da mutane ne gaba daya. Kuma lalle ne, hakika, ManzanninMu sun je musu da hujjoji bayyanannu, sa'an nan kuma lalle ne, masu yawa daga gare su, a bayan wannan, hakika, masu barna ne a cikin kasa". (Suratul Ma'ida: 5: 32)

Sananne abu ne cewa masu mulkin wancan lokacin sun zare takubbansu da kuma bulalinsu don zaluntar al'umma, haka nan kuma sun bude gidajen kurkukunsu don sanya da kuma azabtar da duk wani wanda ya ki yarda ya mika musu kai. Haka nan kuma sun kasance masu tsananin kaushin hali ga masu adawa da mulkinsu na danniya, musamman ma ga mabiya Ahlulbaiti da jagororin adawa daga cikin mataimaka Hasan da Husaini (a.s).

Daya daga cikin masu adawa da wannan gwamnati ya bayyana yadda yanayi ya kasance a wancan lokacin, yana mai magana da sahabbansa cewa:

"Za a kashe ku, kana a sare hannuwa da kafafunku, haka nan kuma a cire muku idanuwa da karfe mai tsananin zafi. Kuma a giciye ku a jikin icen dabino, ba don komai ba sai don kauna mutanen gidan Annabinku...(5)".

Misali, Mu'awiyya dan Abu Sufyan, ya kuduri aniyar ganin bayan shuwagabannin 'yan adawa da hukumarsa daga cikin mabiya Ahlulbaiti (a.s), don haka ya kashe wani adadi daga cikinsu da har ya zuwa yanzu tarihi bai tantance yawansu ba. Daga cikin su kuwa har da akwai:

Daga cikin irin wadannan mutane da ya kashe akwai Hijr bn Adi, daya daga cikin fitattun sahabban Manzon Allah (s)(6).

Irin kisan gilla da Mu'awiyan ya yi wa wannan bawan Allah ya sa har Imam Husaini (a.s) ya rubuta wa Mu'awiyya wasika yana bayyana matsayin wannan bawan Allah, kamar haka:

Ashe ba kai ne ka kashe Hijr dan kabilar Kinda tare da sahabbansa, wadanda suke yin Allah wadai da zalunci, mutanen da suke ganin abin da ake aikatawa a halin yanzu a matsayin kafirce wa imani, sannan kuma ba sa jin tsoron zargin mai zargi ba? Ka kashe su cikin mummunan yanayi, bayan ka yi alkawarin ba su aminci da tsaro (yana mai nuni da sashi na biyar na yarjejeniyar sulhun da aka cimma tsakanin Imam Hasan da Mu'awiyya), kan cewa ba za ka kama su da laifi kan abin da ya gudana tsakaninka da su, ko kuma kan wata gaba da kake yi da su ba.....(7)".

Mu'awiyya dai ya kashe Hijr bn Adi ne tare da wasu sahabbansa, saboda nuna adawa da rashin amincewa da suka yi ga hukumarsa da kuma yarda da jagorancin Imam Ali da 'ya'yansa (a.s) da suka yi. Sahabban Hijr din su ne:

1- Sharik bn Shaddad al-Hadhrami.
2- Sayfi bn Shaddad al-Shaibani.
3- Abdurrahman bn Hassan al-Inzi.
4- Kabisah bn Rabi'ah al-Ibsi.
5- Kidam bn Hayyan al-Inzi
6- Mihriz bn Shihab bn Bujayr bn Sufyan bn Khalid bn Munkir al-Tamimi.

Baya ga wadannan kuma, Mu'awiyya ya kashe wasu daga cikin manyan mutane masu fadi a ji wadanda suka mika kansu ga Imam Ali da kuma 'ya'yansa (a.s), daga cikinsu kuwa akwai:

1- Amru bn al-Humk al-Khuza'iy: Shi sahabi ne, muhajiri, wanda yake da matsayi mai girma a wajen Manzon Allah (s.a.w.a), an kashe shi ne a garin Musil, aka gutsure kansa da wucewa da shi zuwa birnin Damaskus, fadar Mu'awiyya. Kansa dai shi ne kai na farko a tarihin Musulunci da aka dauka daga wani gari zuwa wani gari. Daga baya kuma sai fadawan Mu'awiyya suka kai kan ga matarsa wacce ita ma take daure a kurkuku da nufin kara cutar da ita, to amma koda suka wurga kan a kan cinyanta sai ta rungume shi tana sumbantar bakinsa, tana mai cewa:

"Kun boye min shi na tsawon lokaci, kafin kuka miko min shi matacce a matsayin kyauta, to maraba da wannan kyauta da ba za a taba wulakanta ta ko kuma kinta ba(8)".

2- Abullah bn Yahya al-Hadhrami da sahabbansa.

3- Rashid al-Hujari, wanda aka gutsure hannuwa da kafafunsa alhali yana raye.

4- Juwairiyya bn Musahhir al-Abdi.

5- Awfar bn Hussain, shi ne mutum na farko da Ziyad ya kashe saboda muhawarar da ta shiga tsakaninsu, da farko dai Ziyad ya tambaye shi kan Usman da Mu'awiyya sai ya ba shi amsar da ba ta yi wa Ziyad din dadi ba, daga nan kuma ya tambaye shi me zai ce dangane da shi kansa (Ziyad), sai ya ce:

"Na ji an ce ka fadi a garin Basra cewa wallahi za ka azabtar da maras laifi maimakon mai laifi, haka nan mai zuwa maimakon mai tafiya".

Sai ya ce lalle na fadi haka.

Sai Awfar ya ce masa: To kuwa lalle ka cakuda lamurra.

Sai Ziyad ya cea: To ai wannan mai girman kan ba shi ne mafi munin kungiyar ba, daga nan sai ya kashe shi(9).

Ibn Athir ya nakalto mana mummunan yanayi da zaluncin da ya gudana a garin Basra bayan sulhun da aka yi tsakanin Imam Hasan (a.s) da Mu'awiyya, kamar haka:

"Bayan nada Sumrah gwamnan Basra da Ziyad ya yi na dan wani lokaci, sabon gwamnan ya kashe mutane da daman gaske. Ibn Sirrin ya ce: Sumrah ya kashe kimanin mutane dubu takwas a dan wannan lokaci na rikon kwarya. Lokacin da Ziyad ya tambaye shi ko ba ya jin tsoron cewa ya kashe mutumin da ba shi da laifi a yayin hakan, sai ya ce: 'Hakika ko da ninkin hakan na kashe ba zan ji tsoro ba'. Abu Sawari al-Adawi ya ce: 'Cikin kwana guda kawai, Sumrah ya kashe mutane arba'in da bakwai daga cikin sahabbai wadanda dukkansu mahaddata Alkur'ani mai girma ne(10)".

To wannan dai shi ne yanayin da al'umma suke ciki a wancan lokaci, wanda ke nuni da irin da dabi'a da kuma tafarkin da mahukunta suke tafiyar da al'umma da shi, da kuma yadda suke yi da duk masu adawa da su daga cikin mabiya Ahlulbaiti (a.s) ko kuma sauran kungiyoyin 'yan adawa masu zaman kansu wadanda suke son ganin bayan wannan hukuma ta zalunci.

Malaman tarihi sun nakalto mana irin kakkausar mayar da martani da yakin da Umayyawan suka kaddamar a kan kungiyar adawar da Imam Hasan da Husaini (a.s), jikokin Manzon Allah (s.a.w.a), suke jagoranta, da kuma kokarin wulakanta Amirul Muminin Aliyu bn Talib (a.s) da kuma da la'antarsa da masu mulkin suka sa a yi a kan mimbarori, don mutane su kyamace shi tare da 'ya'yansa da kuma mabiyansu.

Al-Mas'udi ya nakalto wata muhawara da ta gudana tsakanin Mu'awiyya da Sa'ad bn Abi Wakkas, wacce take nuni da hannun Mu'awiyya cikin wannan farfaganda na kokarin zubar da mutumcin mafi daukakan sahabbai (Imam Ali), Mas'udi na cewa:

"Abu Ja'afar Muhammad bn Jarir al-Tabari ya nakalto daga Muhammad bn Hamid al-Razi, daga Abi Mujahid daga Muhammad bn Ishak, daga Ibn Abi Najih yana cewa: 'Lokacin da Mu'awiyya ya tafi hajji, yayi dawafi tare da Sa'ad, bayan gama dawafin sai ya tafi inda zai karbi mutane (Dar al-Nadwa), sai ya zauna tare da Sa'ad. Zamansa ke da wuya sai ya fara zagin Ali (a.s), nan take sai Sa'ad ya matsa yana cewa: 'Ka zaunar da ni a kan shimfidarka, kana ka fara zagin Ali, wallahi, in mallaki sashi guda na falalar Ali, shi ya fi soyuwa a gare ni a kan abin da rana ta fito a kansa (dukkan duniya), wallahi in zamanto sirikin Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma samun da irin wanda Ali ya samu, shi ya fi soyuwa a gare ni a kan in mallaki dukkan abin da rana ta fito a kansa. Wallahi, da Manzon Allah (s.a.w.a) ya fada a kaina abin da ya fadi wa Ali ranar Khaibar ("Gobe zan ba da tuta ga wani mutum da Allah da ManzonSa suke sonsa, shi ma kuma yake son Allah da ManzonSa, tabbatacce ba mai gudu ba, Allah Zai ba da nasara a hannunsa"), shi ya fi soyuwa a gare ni kan in mallaki abin da rana ta fito a kansa. Wallahi, da Manzon Allah (s.a.w.a) ya fadi a kaina abin da ya fadi a kan Ali ranar Tabuka, ("Ashe ba ka yarda ka kasance a gare ni kamar yadda Haruna ya kasance ga Musa ba, sai dai kawai babu Annabi a bayana"), shi ya fi soyuwa a gare ni sama da in mallaki abin da rana ta fito a kansa, lalle ba zan sake shiga gidanka matukar ina raye ba, sai yayi tafiyarsa(11).

Ibn Athir ma ya ce:

"Wata rana Bisr bn Arta'ah ya kasance a gidan Mu'awiyya sai ya fadi mummunar kalma a kan Imam Ali (a.s), nan take sai Zayd bn Umar bn al-Khattab da mahaifiyarsa Ummu Khultoom bint Ali suka buge shi da sanda har suka raunana shi(12)".

Haka nan kuma ya nakalto cewa:

"Lokacin da aka nada Mughira gwamnan Kufa, ya aike da Shihab zuwa garin Rayyu a matsayin mai kula da garin, alhali kuwa ya kasance mai yawaita zagin Ali a kan mimbari, kuma haka ya ci gaba da yi har lokacin da Ziyad ya karbi jagorancin garin Kufa(13)".

"Wata rana Ziyad ya tara mutanen Kufa a fadarsa inda ya tilasta musu la'antar Ali, wanda kuwa ya kiya, sai ya kashe shi".

Wannan yanayi na zagin Aliyu bn Abi Talib (a.s) dai ya ci gaba har lokacin da Umar bn Abdul'Aziz ya dare karagar mulki, inda ya hana hakan da kuma yin kwaskwa-rima ga jami'an gwamnati.

Al-Mas'udi ya ci gaba da cewa:

"Umar dai ya kasance mutum mai tsantsaini da kaskantar da kai. Ya sallami jami'an gwamnatin Umayyawa wacce ta wuce da kuma sanya wasu wadanda suke na kirki, wadanda suke bin tafarkinsa na gudanar da al'amurra. Shi ne wanda ya kawo karshen la'antar Ali (a.s) da ake yi akan mimbarori, da maye gurbin hakan da wannan aya ta Alkur'ani mai girma:

( ربَّنا أغفرلنا ولإخواننا الذين سبقونا بالإيمان ولا تجعل في قلوبنا غلاًّ للذين أمنوا' ربّنا إنَّك غفور رحيم )

"Ya Ubangijinmu! Ka yi mana gafara da kuma 'yan'uwanmu, wadanda suka riga mu yin imani, kada Ka sanya wani kulli a cikin zukatanmu ga wadanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin kai".(Suratul Hashr: 59:10).

Wasu kuma suka ce wannan ayar ce ya sanya maimakon la'antar da ake wa Ali (a.s):

( إنّ الله يأْمر بالعدل والإحسان وايتاء ذي القربى وينهى عن الفحشاء والمنكر والبغي )

"Lalle Allah na yin umurni da adalci da kyautatawa, da bai wa ma'abucin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin da aka ki da rarrabe jama'a...". (Suratun Nahl: 16:90).

Wasu kuma suka ce dukkan biyun ne ya sanya, kuma al'umma suka ci gaba da amfani da su a hudubobi har zuwa yau(14)".

Idan muka bar dalilan da suka rurata wutan wannan yunkuri da kuma karfin 'yan adawa, da suke kira ga gudanar da hukumce-hukumcen adalci da daidaitawa tsakanin al'umma da Musulunci ya ke kira zuwa gare shi, da girmama nufin al'umma da kuma riko da koyarwa da kuma akidun Musulunci wajen mu'amala ta siyasa da sauran al'umma.

Haka nan kuma idan muka rufe ido kan hakan, muka kuma yi darasin yanayin tattalin arziki na wancan lokacin da kuma yadda mahukuntan suka yi karen tsaye wa tsarin rabon tattalin arziki na Musulunci wanda yake kira zuwa ga daidaituwa wajen rarraba dukiya, haramcin boye kayayyaki, wajibcin daukan nauyi da biyan bukatun marasa galihu, bugu da kari kan matsaloli na tsaro, to za mu ga cewa duk wadannan abubuwa sun kasance dalilai masu karfi na motsa zukatan al'umma da kuma matsowa kusa ga Imam Husaini (a.s) don jagorantarsu wajen kawar da irin wannan tsari.

Hakika marasa galihu daga cikin al'umma sun fara kosawa da yadda ake take hakkokinsu da kuma irin tsananin talauci da suke fama da shi, a gefe guda kuma wasu 'yan tsiraru suna wasa da dukiyoyinsu, duk kuwa da cewa Allah Madaukakin Sarki Ya yi tsokaci kan hakan:

( والَّذِينَ يَكْنزون الذَّهَبَ والفِضةَ ولا يُنْفِقُونها في سبيلِ اللهِ فَبَشِّرهُمْ بِعَذابٍ أليمٍ )

"Kuma wadanda suke taskacewar zinariya da azurfa, kuma ba su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushara da azaba mai radadi". (Suratul Tauba: 9:34).

ما أفاءَ اللهُ على رسولِهِ من أهْلِ القرى فلِلَّهِ وللرَّسُولِ ولِذي القُربى واليَتامى والمَسَاكِين وابنِ السَّبيلِ كَي لايكونَ دولةً بينَ الأغْنياءِ منْكمْ وما اتَاكُم الرَّسولَُ فخُذوهُ وما نهاكمْ غنهُ فانتَهوا واتَّقُوا اللهَ إنَّ اللهَ شَديدُ الْعِقَابِ

"Abin da Allah Ya sanya shi ganima ga ManzonSa daga mutanen kauyukan nan, to, na, Allah ne, kuma na ManzonSa ne, kuma na masu dangantaka da maraya da miskinai da dan hanya (matafiyi) ne, domin kada ya kasance abin shawagi a tsakanin mawadata daga cikinku, kuma abin da Manzo ya ba ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da takawa. Lalle Allah, Mai tsananin ukuba ne". . (Suratul Hashri: 59:7).

Hakika tarihi ya siffanta mana yadda yanayin tattalin arziki da kuma raba shi tsakanin al'umma ya kasance a wancan lokacin, wasu 'yan tsiraru ne suka mallake dimbin arzikin al'umma.

A matsayin misali, tarihin ya bayyana mana sunayen wasu mutane wadanda suka wawuri dukiyoyin al'umma saboda alakar da suke da ita da gidan sarautar Umayyawa tun daga lokacin 'Shiryayyun Halifofi' har zuwa lokacin mulkin Yazid.

Malaman tarihin sun bayyana cewa: 'Amru bn al-Aas, gwamnan Masar a lokacin Mu'awiyya, ya mallaki kadda-rorin da suka kai kimanin dinare dubu dari uku da ashirin da biyar, dirhami dubu, kayayyakin gona da suka kai dinare dubu dari biyu a Masar da kuma sanannen makeken ginin nan da ake ce al-Waht da aka kiyasta kudinsa kimanin dirhami dubu goma'.

'Haka nan kuma Abdurrahman bn Awf ya kasa gadonsa gida goma sha shida ga matayensa, inda kowace guda ta sami dirhami dubu tamanin(15)'.

"Marwan bn Hakam ya kwashi kimanin dinare dubu dari biyar na kudaden shigan da aka kawo daga Afirka(16)".

"Ibn al-Aas ya karbi kyautar da ta kai kimanin dirhami dubu dari(17)".

"Kamar yadda Abdullah bn Khalid bn Asid ya karbi wata kyauta da ta kai kimanin dirhami dubu dari hudu(18)".

"An kiyasta dukiyar Ya'ali bn Umayyah ta kai dinare dubu dari biyar, ban da basussukan da ya ke bin mutane da kuma sauran kaddarori da suka kai dinare dubu dari uku(19)".

"Sa'ad bn Abi Wakkas, a lokacin mutuwarsa, ya bar kimanin dirhami dubu dari biyu da hamsin(20)".

"Sa'id bn al-Musayyab ya nakalto cewa Zaid bn Thabit ya bar zinare da arzurfan da sai da gatari ake saransu da kuma dukiya da kaddarar da ta kai kimanin dinare dubu dari lokacin a lokacin mutuwarsa(21)".

Wannan kadan kenan daga cikin abin da tarihi ya nakalto mana kan abubuwan da suka faru, ko da yake lamarin ba wai kawai ya takaita ba ne ga wadannan mutane da aka ambata, face dai kawai misali ne na irin mummunan yanayi na tattalin arziki da wasa da kudaden al'umma da aka yi. Wannan yanayi da ya kasa al'ummar musulmi zuwa kashi biyu, kashin fakirai marasa galihu da kuma kashin masu abin hannu wadanda suke ci da gumin al'umma, lamarin da ya saba wa tsarin Musulunci da ya yi kira zuwa ga daidaituwa tsakanin al'umma da kuma haramta satan kudaden al'umma da mallaka su ga wadansu kashi na al'ummar.

Don haka irin wannan mummunan yanayi na tattalin arziki da al'umma suka shiga na daga cikin dalilan da suka motsa wutar wannan yunkuri, ta yadda kashin marasa galihu wadanda ake zalunta da kuma masu kira zuwa ga daidaito suka koma bangaren Imam Husaini (a.s), a matsayinsa na mutum guda wanda kawai zai iya gudanar da shari'a da kuma dokokin Musulunci kamar yadda ake yi a lokacin rayuwar Ma'aikin Allah (s.a.w.a).




____________
(1)- Maktal al-Husaini na al-Khawarizmi, juzu'i na 1, shafi na 88.
(2)- Maktal al-Husaini na Ibn Dawus, shafi na 11.
(3)- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 204.
(4)- Maktal al-Husain na Abdurrazak al-Mukarram, shafi na 141 da kuma na 142.
(5)- Sulhu al-Hasan na Shaikh Radhi Al' Yasin, shafi na 320 da Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Tabari, juzu'i na 7, shafi na 104.
(6)- Sulhu al-Hasan na Shaikh Radhi Al' Yasin, shafi na 328.
(7)- Sulhu al-Hasan na Shaikh Radhi Al' Yasin, shafi na 338, ya nakalto daga Bihar al-Anwar na Allamah Majlisi, juzu'i na 10, shafi na 149.
(8)- Sulhu al-Hasan na Shaikh Radhi Al' Yasin, shafi 328.
(9)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 3, shafi na 462.
(10)- Kamar na sama.
(11)- Muruj al-Zahab na al-Mas'udi, juzu'i na 3, shafi na 14.
(12)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 12.
(13)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 3, shafi na 413.
(14)- Muruj al-Zahab na al-Mas'udi, juzu'i na 3, shafi na 183 da 184.
(15)- Kamar na sama, shafi na 23.
(16)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 3, shafi na 91.
(17)- Al-Ma'arif na Ibn Kutaibah al-Dinuri, shafi na 84.
(18)- Kamar na sama.
(19)- Muruj al-Zahab na al-Mas'udi, juzu'i na 2, shafi na 333.
(20)- Dabakat na Ibn Sa'ad, juzu' i na 3, shafi na 105.
(21)- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 2, shafi na 333.