A BABBAN BIRNIN HALIFANCI

Don nuna farin ciki da kashe dan 'yar Manzon Allah (s.a.w.a) da sauran sahabbansa da kuma isowar kawuka da fursunonin gidan Annabci zuwa Damaskus babban fadar halifanci, sai Yazid ya yi umarni a yi ado wa garin da sanya fitilu a kan tituna da kuma gayyatar mata masu rawa da kida don cashewa(1).

Haka aka wuce da ayarin fursunonin da kuma kawukan tituna-tituna na garin har zuwa fadan Yazid, wanda ya cika da farin ciki saboda kashe Husaini (a.s) da ya yi. A daidai wannan lokaci kuwa Yazid ya ci ado ya sanya wani kambi na yakutu(2) a kansa, ga shi kuma ya kira dukkan manyan kasar Sham ya zaunar da su a gefensa(3).

Daga nan sai aka shigo da kawukan shahidan, kan Husaini (a.s) yana gaba, sai Yazid ya matso kusa yana dukan bakin Husaini (a.s) da wata bulaliya da take hannunsa. Ganin haka sai wani sahabi na Manzon Allah (s.a.w.a) mai suna Abu Barzat al-Aslami ya ce masa: Shin kana dukan bakin Husaini ne da bulaliyarka? Wallahi ka sa bulaliyarka cikin bakin da na ga Manzon Allah (s.a.w.a) yana tsotsansa. Kai Yazid za ka zo Ranar Lahira alhali Ibn Ziyad ne zai kasance mai cetonka, shi kuwa wannan zai zo Ranar Lahira alhali Manzon Allah (s.a.w.a) ne zai kasance mai cetonsa, daga nan sai ya tashi ya fice(4)".

Sanannen abu ne cewa a Yakin Badar an kashe mushirikan Umayyawa da yawa, to daga wannan lokacin bakin cikin wannan abu da ya faru ya ke ci gaba da tafasa cikin zukatan Umayyawan har lokacin da aka zo kan Yazid. Shi ya sa a daidai lokacin da aka zo da kan Husaini (a.s) aka ajiye a gabansa sai ya fara rera wasu baitoci na wakan da daya daga cikin mawakan mushirikan Kuraishawa wato Ibn al-Zab'ari ya rera yana mai nuna juyayinsa da kashe mushirikan da aka yi a Badar:

Kaicon manyana a Badar da ma sun shaida,
             Damuwar kabilar al-Khazraj kan…..
Da sun kasance cikin tsananin farin ciki,
             Kana su ce min barkanka kada ka janye.

Amir al-Sha'abi ya ce: sai Yazid ya kara wasu baitoci guda biyu kan wadannan baitoci, yana mai cewa:

Hashimawa sun yi wasa da mulki alhali babu,
            Wani labari da ya zo kuma babu wahayin da ya sauko.
Lalle ban kasance daga rami ba in ban dau fansa,
             Daga zuriyar Ahmad in ban aikata ba
(5).

Tun kafin isowar wadannan fursunoni na gidan Manzon Allah (s.a.w.a) dai mahukuntan wancan lokacin sun tura 'yan amshin shatansu suna ta yada kararrakin cewa Yazid ya yi nasara a kan masu masa tawaye kuma wadannan fursunoni da aka zo da su mata da 'ya'yayensu ne, kana kuma suka bukace su da su yi ado don nuna farin cikinsu. Wasu dai sun yarda da wannan karya, hatta ma dai wasu malumman tarihi sun ruwaito yadda lamarin ya kasance, kamar haka:

"An shigo da zuriyar Ma'aikin Allah (s.a.w.a) garin Damaskus ne ta wata kofa da ake kira Kofar 'Tuma', daga nan aka wuce da su zuwa masallaci inda ake taruwa. Ko da isowarsu sai wani tsoho ya kalle su cikin wulakanci ya ce: 'Godiya ta tabbata ga Allah da Ya kashe ku da kuma hallaka ku kana kuma Amirul Muminina ya sami nasara a kanku'.

Sai Aliyu bn Husaini (a.s) ya ce masa: "Ya Kai Dattijo, shin kana karanta Alkur'ani?Sai ya ce masa: 'Na'am', sai ya ce masa: "Shin ka san wannan ayar: "Ba na tambayarku wata lada a kansa face dai soyayya ga makusanta(6)'?.Sai tsohon ya ce: 'Lalle na karanta wannan aya. Sai Aliyu bn Husaini (a.s) ya ce: "To Ya kai wannan Dattijo mu ne wadannan makusantan". Sai ya ci gaba da cewa: "Shin ka karanta cikin Surar Bani Isra'ila: "Kuma ka bai wa ma'abucin zumunta hakkinsa(7)"?, sai Dattijon ya ce: 'Na taba karantawa', sai Aliyu bn Husaini (a.s) ya ce masa: "To mu ne ma'abuta zumuncin Ya Dattijo", har ila yau shin ka taba karanta wannan aya: "Kuma ku sani, abin sani kawai, abin da kuka sami ganima daga wani abu, to, lalle ne Allah Yana da humusinsa (kashi daya cikin biyar) haka Manzo da makusantansa(8)"?,sai Dattijon ya ce: 'Lalle na taba karantawa', sai Aliyu bn Husain (a.s) ya ce masa: "To mu ne makusantan Ya kai Dattijo". Haka nan kuma shin ka taba karanta wannan aya: "Allah kawai na nufin Ya tafiyar da kazanta daga gare ku ne Ya ku Mutanen babban gida Ya kuma tsarkakeku tsarkakewa"?, sai Dattijon ya ce: 'Lalle na taba karantawa', sai ya ce masa: "To mu ne Mutanen babban gidan (Ahlulbaiti) da wannan aya ta kebance mu da tsarkakewar".

Jin haka sai Dattijon nan ya yi shiru yana tunanin kan mummunan maganar da ya gaya musu, daga nan sai ya daga kansa sama yana cewa: "Ya Allah ina neman afuwa daga gare ka saboda wannan zance da na yi da kuma gaba da na yi da wadannan mutane. Ya Allah ina barranta daga dukkan masu gaba da Muhammadu da Alayen Muhammadu daga mutane da aljannu(9)".

Yanzu kuma bari mu koma fadar Yazid don ganin abin da yake faruwa a can a lokacin da aka tsayar da Aliyu bn Husain (a.s) tare da sauran fursunonin gidan Manzo a gaban Yazid. Sai Yazid ya ce masa: "Babanka da Kakanka sun so su kasance shuwagabanni, to amma godiya ta tabbata ga Allah da ya wulakanta su ya kuma zubar da jininsu. Sai Aliyu bn Husaini (a.s) ya amsa masa:

"Ya kai dan Mu'awiyya da Hind da Sakhr, wallahi Iyaye da Kakannina ba su gushe ba suna da matsayi, Kakana Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya kasance dauke da tutan Manzon Allah (s.a.w.a) a Badar, Uhudu da Ahzab, a daidai lokacin da kakanninka kuwa suke dauke ne tutan kafirai", daga nan sai ya ci gaba cikin baitocin wake:

Me za ku ce a lokacin da Annabi ya ce muku,
             Me kuka aikata a matsayinku na karshen al'umma.
Da Zuriya da kuma Iyalaina bayan rasuwata,
             Cikinsu akwai fursunoni wasu kuma sun fadi cikin jini.
Haka bai kasance sakamakona bayan na muku nasiha,
             Da kada ku halifance ni da mummana a kan Zuriyata.

Daga nan sai Aliyu bn Husain (a.s) ya ce: "Kaiconka Ya Yazid, da ace ka san danyen aikin da ka aikata ga Babana da kuma Iyalaina, dan'uwansa da kuma yadukwannina. To lalle da ka gudu ka hau dutse da ka kuma zubar da hayawe saboda kasantuwan kan Husaini dan Fatima a rataye a jikin kofan gari, alhali kuwa shi jinginan Manzon Allah (s.a.w.a) ne a gare ku. Don haka ina maka bushara da sakamako da nadama a Ranar da za a tara dukkan mutane da babu kokwanto cikinta".

Sai daya daga cikin malaman yahudawa da ke wurin ya dubi Yazid ya tambaye shi cewa:

"Wannan wani yaro ne Ya Amiral Muminina"? sai ya ce masa: 'Mai wannan kan shi ne Mahaifinsa', sai ya ce masa: 'Kan wane ne wannan Ya Amiral Muminina"?, sai ya ce masa: 'Husain bn Ali bn Abi Talib', sai ya ce masa: 'Wace ce Mahaifiyarsa'?, sai ya ce masa: 'Fatima 'yar Muhammadu'. Daga nan sai malamin yahudawan ya ce masa: 'Tsarki ya tabbata ga Allah, a'a wannan dan 'yar Annabinku ne amma kuka kashe cikin wannan lokaci'?, lalle abin da kuka aikata da zuriyarsa a bayansa ya munana, wallahi da Musa bn Imrana ya bar mana wani jika daga cikin zuriyarsa da mun bauta masa sabanin Allah. Amma ku kan Annabinku ya bar ku ba da jimawa ba amma haka kuka aikata ga dansa kuka kuma kashe shi". Daga nan sai Yazid ya yi umarni a yi da shi, inda nan take wannan malamin yahudawa ya mike yana cewa: 'Oho dai duk abin da kuke son aikatawa da ni ku aikata, amma dai ni na gani cikin Attaura cewa duk wani wanda ya kashe zuriyar wani Annabi, to lalle ba zai yi nasara ba a duk tsawon rayuwarsa, idan kuwa ya mutu Allah Zai wuce da shi Wutan Jahannama(10)".

Har ila yau dai malaman tarihin sun ruwaito hudubar da Zainab al-Kubra (a.s) ta gabatar a gaban Yazid a lokacin da yake hura hancin kiyayya ga Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) a lokacin da aka shigo da su fadarsa alhali suna daddaure:

"Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata da Manzonsa da dukkanin Alayensa. Allah Ya yi gaskiya a yayin da ya ce: "Sa'an nan karshen wadannan da suka aikata mugun aiki ya kasance mafi muni, saboda sun karyata ayoyin Allah, kuma suka kasance suna izgili da su". (Surar Rum:10).

Ya Yazid, shin kana tsammani ka kwace kasa da sama ne daga gare mu don ana yawo da mu kamar yadda ake yawo da fursunoni, sannan kuma mu wulakantattu ne a wajen Allah kai kuma mai daukaka? Saboda wannan nasara ta zahiri ne da ka samu ya sa kake alfahari da dagawa, kana mai tsammanin ka sami wata kyauta ce ta duniya kuma lamurranka sun daidaita haka nan kuma mulkinka ya dawo hannunka. To amma ka dakata kadan, kada ka yi farin ciki. Shin ka mance da fadin Allah Madaukakin Sarki ne cewa: "Kuma kada wadanda suka kafirta su yi zaton cewa, lalle ne, jinkirin da Muke yi musu alheri ne ga rayukansu. Muna yi musu jinkirin ne domin su kara laifi kawai, kuma suna da azaba mai wulakantarwa". (Surar Al'Imrana: 178).

Ya kai dan sakakku! Shin wannan shi ne adalcinka, ka bar 'ya'yaye da kuyanginka cikin sutura amma ka sanya ana yawo da 'ya'yan Manzon Allah titi-titi cikin mawuyacin hali a matsayin fursunoni. Ka ci mana mutumci ta hanyar bayyanar da fuskokinmu. Sojojinka sun dinga yawo da mu daga gari zuwa gari, dukkan nau'oi na mutane, mazauna duwatsu da bakin teku suna kallonmu. Na kurkusa da na nesa, wulakantattu da madaukaka dukkansu suna kallonmu alhali kuwa muna cikin wani irin hali da babu wani namiji tare da mu da zai taimaka mana ko ba mu wata gudummawa.

Ya Yazid, duk wani abin da ka aikata yana nuni ne da tawayenka ga Mahalicci da kuma rashin imaninka da Manzo (s.a.w.a), Littafin Allah da kuna Sunnar da Annabi ya zo da ita. Lalle ayyukanka ba za su kasance abin mamaki ba, don kuwa duk mutumin da kakanninsa suka ci hantar tsarkakakkun bayi, wanda namansa ya ginu daga jinin shahidai, wadanda suka yaki shugaban dukkan Annabawa, ba abin mamaki ba ne in ya wuce dukkan larabawa wajen kafirci, aikata sabo da kuma kiyayya da Allah da ManzonSa (s.a.w.a).

Ka tuna fa wadannan munanan ayyuka da ka aikata sun samo asali ne daga kafirci da kuma kullin da kake da shi saboda kakanninka da aka kashe a Badar.

Hakika duk mutumin da ya sanya idanuwan kiyayya da gabansa a kanmu ba zai yi kasa a gwuiwa wajen aiwatar da wannan kiyayya a kanmu ba. Lalle ya tabbatar da rashin imaninsa da kuma bayyanar da shi da harshensa lokacin da ya ce cikin farin ciki: "Na kashe 'ya'yan Manzon Allah da kuma mayar da iyalansa fursunoni" da kuma fatan da kakanninsa sun rayu su ga wannan nasara da ya cimma don su ce 'Ya Yazid, kada hannayenka su rasa wannan karfi, lalle ka dau mana fansa a madadinmu'.

Ya Yazid, shin kana dukan lebban Imam Husain ne da sandanka a gaban jama'a bayan kuwa Manzon Allah (s.a.w.a) ya sha sumbantan wadannan lebba, amma duk da hakan kana cikin farin ciki da annashuwa.

Na rantse da Allah, lalle ka kara mana zafin ciwonmu da kuma cutar da mu gaba daya ta hanyar kashe Shugaban matasan Aljanna, dan shugaban larabawa (Ali) kana kuma tauraron iyalan Abdul-Mutallib mai haske. Ta hanyar kashe Husain bn Ali (a.s), lalle ka kusa isa ga makoman kakanninka marasa imani da Allah. Kana bayyanar da wannan aika-aika da ka aikata cikin alfahari da kuma fatan cewa idan kakannin naka suka ga aikin naka za su yarda da shi da kuma yi maka addu'an kada hannunka ya raunana.

Ya Allah, Ka karbo mana hakkinmu, Ka dau mana fansa akan wanda ya zaluncemu, Ka nuna fushinKa ga wanda ya zubar da jininmu.

Ya Yazid! Ka aikata duk abin da kake so, amma ka kwana da sanin cewa ka yanka jiki da namanka ne da kanka gunduwa-gunduwa. Nan gaba kadan za a gabatar da kai gaban Manzon Allah (s.a.w.a), lalle nauyin mummunan aikinka na zubar da jinin iyalansa da kuma wulakantasu zai gagare ka dauka. Za a kaika inda za a kaika ne a idanuwan iyalan gidansa, inda za a dau fansa kan azzalumai da kuma azabtar da makiya, "Kada ka yi zaton wadanda aka kashe a tafarkin Allah matattu ne. A'a rayayyu ne su a wajen Ubangijinsu, ana ciyar da su. Suna masu farin ciki saboda abin da Allah Ya ba su na daga falalarSa..", (Surar Al'Imrana: 169-170).

Hakika Allah ya isa ya hukumtaka, Manzon Allah kuma ya kasance mai husuma da kai kana Jibrilu kuma shi ne mai taimakonmu. Lalle da sannu wadanda suka dora ka akan musulmi da kuma wahalar da su za su ga abin da ke jiransu, kuma lallai makomar azzalumai ta munana ta zama makoma.

Ya Yazid! Ba wai ina maka wadannan maganganu da kuma nusar da kai irin azabar da ke jiranka don ko ka yi nadama kan abin da ka aikata ba ne, a'a, don kuwa kai kana daga cikin mutanen da zukatansu suka kekashe, wadanda rayukansu da jikkunansu suka tarbiyyantu da sabon Allah, wadanda kuma suke karkashin la'anar Manzon Allah (s.a.w.a). Lalle kai kana daga cikin mutanen da Shaidan ya yi musu tambari a kan zukatansu, ba abin da suke haifarwa in ban da sharri.

Babban abin mamakin shi ne kisan gillan da 'ya'yan sakakkun masu sabo suka yi wa bayin Allah, 'ya'yan Annabawa da wasiyyai. Hannayensu sun zubar da jininmu kana kuma namanmu ya kasance musu kalace. Lalle muna jin zafi ga wadanda aka bar gawawwakinsu a yashe a fagen daga ba tare da an bisne su ba. Kai Yazid, idan har kana tunanin cewa wannan abin da ya same mu a matsayin wata nasara gare ka, to lallai za ka dandana kudanka kan hakan a lokacin da ba abin da za ka gani face abin da ka aikata, don kuwa Ubangijinka ba ya zaluntar bayinSa. Allah Shi ne abin dogaronmu kuma Shi ne kawai muka mika burinmu gare Shi.

Ka yi dukkan makircin da ka ke iyawa, sannan ka yi dukkan kokarin da za ka iya, amma dai wallahi ba za ka iya shafe ambatonmu ba da kuma dushe haskenmu, haka nan kuma ba za ka kawar da wannan wulakancin da kake ciki ba. Shin akwai wani abin da ya rage wa kalamanka in ba rauni ba, haka nan kuma ranakunka face 'yan kididdigaggu ba. Lalle ka kiyaye ranar da mai sanarwa zai sanar da la'anar Allah a kan azzalumai.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, Wanda ya cika wa na farkonmu da sa'ada da kuma gafara, kana na karshenmu kuma da shahada da rahama, muna rokon Allah da ya cika musu da lada Ya kuma kara musu Ya kuma kyautata mana halifanci, don kuwa Shi Mai rahama ne, kuma lalle Allah Ya isar mana kuma madalla da wakilcinSa(11)".

Wasu malaman tarihin dai, saboda wasu dalilai da suka hada da kwadayin abin da ke hannun azzaluman masu mulki ko kuma saboda tsoron fadin gaskiya, sun ruwaito wasu ruwayoyi inda suke kokarin wanke wannan mummunan aikin da Yazid ya aikata na kashe abin kaunar Manzon Allah (s.a.w.a) wato Husain bn Ali (a.s) tare da iyalai da kuma sahabbansa, suna masu cewa wai Yazid ya la'anci Ubaidullah bn Ziyad kan abin da ya aikata da kuma cewa wai Yazid bai so a kashe Husaini (a.s) ba da dai sauran zantuttuka irin wadannan marasa tushe, wadanda abubuwan da Yazidun ya aikata bayan wannan danyen aiki ya ke karyata su. Don idan da a ce Yazid ya damu ko kuma ya ji zafin kashe Husainin da aka yi, to me ya sa ya aika da wasika zuwa ga Ibn Ziyad yana umurtansa da ya turo mataye da yaran Husaini (a.s) daga Kufa zuwa Sham a daure cikin sarka? Kana kuma me ya sa ya shirya bukukuwa da kuma sanya fitilu cikin garin Sham da gayyatar masu kide-kide da raye-raye don taya shi murna? Haka nan kuma me ya sa ya ajiye kan Husainin (a.s) a gabansa yana dukan bakinsa da bulaliyar da ke hannunsa, kana kuma me yasa ya ke rera wakar Abdullah bn al-Zab'ari da kuma nuna jin dadinsa da daukan fansa a kan Manzon Allah (s.a.w.a) ta hanyar kashe Zuriyarsa tsarkaka?, kamar dai yadda muka ambata a baya daga tabbatattun masdarori(12).

Ala kulli halin dai Imam Sajjad (a.s) tare da sauran iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) sun zauna na wasu kwanaki a Sham, kafin suka kama hanyar komawa Madina da kuma wucewa da kawukan shahidan Karbala zuwa can Karbalan don bisne su kusa da jikkunansu.

Imam Sajjad (a.s) dai da sauran wadanda suke tare da shi sun iso Madina alhali daman labarin abin da ya faru ya riga da ya iso, don haka tuni garin ya rude da koke-koke don nuna bakin ciki da damuwa da abin da ya same su. A daidai lokacin kuwa ana iya jin sautin Bishr bn Hathlam yana cewa:

Ya mutanen Yathrib! Ba ku ci ta zama ba,
             An kashe Husain, hawayena na zuba ba kyakkyaftawa.
Jikinsa yana nan cikin jini a Karbala
             Kansa kuwa yana nan a jikin mashi an tsire shi.

Haka dai garin Madina ya ci gaba da zama cikin juyayi da bakin ciki har lokacin da al'umman garin karkashin jagorancin Abdullah bn Handhalah suka yi bore wa hukumar Umayyawa suna ba da rayuwarsu don kaunar Husaini da kuma Ahlulbaiti (a.s).




____________
(1)- Khawarizmi al-Hanafi ya yi karin bayani kan wannan batu cikin littafinsa Maktal al-Husaini juzu'i na 2, shafi na 60 da 61 da ruwaya daga sahabin nan mai girma Sahl bn Sa'ad wanda a daidai lokacin ya zo wucewa kasar Sham, don haka ya ruwaito abin da ya gani.
(2)- Maktal Husain na Khawarizmi, juzu'i na 2, shafi na 61.
(3)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 352 da Al-Futuh na A'atham al-Kufi, juzu'i na 3, shafi na 152.
(4)- Tarikh al-Umam wa al-Muluk na Dabari, juzu'i na 4, shafi na 356, Ibn Athir cikin Al-Kamil fi al-Tarikh, juzu'i na 4, shafi na 85, Maktal al-Husain na Khawarizmi, juzu'i na 2, shafi na 58 da kuma Ibn Kathir, juzu'i na 8, shafi na 192.
(5)- Maktal al-Husain na Kharizmi, juzu'i na 2, shafi na 58, Ibn Kathir cikin Tarikh Ibn Kathir juzu'i na 8, shafi na 192 da 204, Al-Futuh na A'atha al-Kufi, juzu'i na 3, shafi na 150. Yazid ya canza baiti na biyu inda ya sanya sunansa, yana cewa:
Da sun kasance cikin tsananin farin ciki,
               Kana su ce Ya Yazid kada ka zama shanyayye.

Kamar yadda za mu gani nan gaba cikin hudubar Zainab da ta yi a gaban wadannan azzalumai.
(6)- Surat al-Shura', aya ta 23.
(7) - Suratul Isra', aya ta 26.
(8)- Suratul Anfal, aya ta 41.
(9)- Al-Futuh na A'atham al-Kufi, juzu'i na 3, shafi na 151 da 152, Maktal al-Husain na Khawarizmi.
(10)- Al-Futuh na A'atham al-Kufi, juzu'i na 3, shafi na 153 da 154 da kuma Maktal al-Husain na Khawarizmi, juzu'i na 3, shafi na 71.
(11)- Maktal al-Husain na Abdurrazak al-Musawi al-Mukarram, shafi na 358 da 359.
(12)- Karin abin mamakin ma dai shi ne cewa su wadannan malaman tarihi su ne dai suka ruwaito ruwayoyin da suka yi nuni da zaluncin da Yazid ya yi wa Iyalan gidan Annabi (s.a.w.a), kame su a matsayin fursunonin yaki da kuma bugun bakin Imam Husain (a.s) da yake yi da bulaliyar da take hannunsa.