Ta haka dai Imam Husaini (a.s) ya shirya barin birnin Madina, to sai dai kuma bai bar birnin ba har sai da ya kai ziyarar ban kwana ga kabarin kakansa Manzon Allah (s.a.w.a), yana cike da sanin cewa ba zai dawo ba kuma daga wannan rana ba zai sake samun damar ziyarar kabarin kakan nasa ba. Yana mai sane da cewa ba za su sake ganawa da shi ba har sai a Aljanna, kuma ba zai hadu da kakan nasa ba face yana a matsayin shahidi da kuma isar da kukansa gare shi saboda irin abin da aka masa. Don haka sai Imam Husaini (a.s) ya tsaya a gaban kabarin yayi salla raka'a biyu, sannan ya daga hannu yana munajati da Ubangijinsa:
"Ya Allah! Wannan kabarin AnnabinKa Muhammadu (s.a.w.a) ne, kuma ni din nan dan 'yar AnnabinKa ne. Ka riga da kasan irin halin da nake ciki. Ya Allah! Ina son umarni da alheri da kuma hani da mummuna, don haka ina rokonKa, Ya Ubangijin daukaka da karamci, don darajar wannan kabari da wanda ya ke cikinsa, da Ka zaba min abin da zai kasance cikinsa akwai yardarKa da kuma yarda ManzonKa(1).
Haka wannan azama ta Imam Husaini (a.s) ta kasance, haka wannan Jagora, wanda ba ya mika wuya, ya yi azama. A'a ta ya ya zai mika wuya ba yan ya kasance makomar al'umma kana kuma mai kare sakon Musulunci? Don haka ya nufi Makka, zuwa ga Haramin Aminci, don kaddamar da wanann yunkuri nasa daga wajen.
Daga nan ne sai wannan tawaga ta Imam Husaini (a.s) ta kama hanyar Makka(2), ya kama hanya cikin hamada tare da iyalan gidansa, sahabbi, mataye da 'ya'yansa tare da kuma 'yar'uwarsa Zainab al-Kubra (a.s), yana mai maimaita fadin Allah Madaukakin Sarki cewa:
( ÝóÎóÑóÌó ãäåÇ ÎóÇÆöÝðÇ íóÊóÑÞóÈõ ÞóÇá ÑÈøö äóÌøöäí ãöäó ÇáÞóæúãö ÇáÙøóÇáãíäó ) "Sai ya fita daga gare ta, yana mai jin tsoro yana sauna. Ya ce, "Ya Ubangijina! Ka tseratar da ni daga mutane azzalumai(3)".
A hanyarsa ta tafiya zuwa birnin Makka, Imam Husaini (a.s) ya hadu da Abdullahi bn Muti' wanda ya tausayawa halin da Imam (a.s) din ya ke ciki yana mai tsoron cewa duniya za ta rasa mutum kamar Husaini (a.s), wanda babu wani kamarsa a lokacin wanda zai kare Musulunci da kuma koyarwa ta Manzon Allah (s.a.w.a).
Don kuwa a lokacin dukkan bururrukan al'umma sun koma ne ga Husain (a.s) kamar yadda kuma zukata suka koma gare shi. A lokacin babu wani mutum guda ko kuma wani karfi da al'umma za su iya rikewa da zai iya fuskantar hukumar ja'irzi ta Yazid, don haka Abdullahi bn Muti' din ya ce masa:
"Na rantse da Allah, idan har aka kashe ka to za a mai da mu bayi bayanka".
Babu shakka wannan kalami da ra'ayi na Abdullah shi ne kalami da kuma ra'ayin al'ummar musulmi a wancan lokacin, wannan kalami na sa yana nuni ne da irin halin da al'ummar musulmi suke ciki ne a wancan lokacin. Yana ji a jikinsa irin mulkin kama karya da danniya na Umayyawa, kuma babu wani mutum guda da zai iya 'yantar da al'umma daga wannan hali da suke ciki in ba Husaini (a.s) ba, don haka ne yake fadin wannan kalami nasa:
"Na rantse da Allah, idan har aka kashe ka to za a mai da mu bayi bayanka".
Daga nan sai ya tambayi Imam Husaini (a.s), alhali yana son jin ra'ayinsa da kuma matsayarsa, wacce take matsaya ce ta al'umma gaba daya, sai ya ce masa:
"Ya Shugabana, ina ka nufa ne?"
Sai Husaini (a.s) ya amsa masa: "A halin yanzu garin Makka na nufa, daga baya kuma zan bar wa Allah zabi".
Sai Abdullah ya ce: "Allah Ya shiryar da kai kuma Ya sanya mu fansa gare ka, to sai dai idan har ka isa Makka, to ina horonka da kada ka kusanci Kufa, don kuwa garin shu'umin gari ne, a gurin ne aka kashe Mahaifinka, aka ha'inci Dan'uwanka aka kuma kashe shi. Ka lizimci Haramin Allah, don kuwa kai Shugaban larabawa ne, babu wani mutum da za a iya kwatanta shi da kai daga cikin mutanen Hijaz, kuma mutane ba za su taba amincewa da wani a matsayin shugaba in ba kai ba, za su zo maka ta kowani bangare. Kada ka rabu da Harami, Allah ya sanya baffana da kawuna su kasance maka fansa, wallahi idan har aka kashe ka, to lallai za a cutar da mu a bayanka(4)".
Hanyar zuwa Makka dai tana da nisa(5), kuma a lokacin rairayin hamada ya yi zafi saboda zafin rana, to amma haka dai wannan tawaga ta Imam Husaini (a.s) ta tsaga wannan rairayi da tuddan kasa mai zafin gaske. Haka dai wannan tawaga ta masu sadaukarwa kana kuma taurarin jihadi ta juya fuskarta zuwa Dakin Allah, daga nan kuma ta nufi kasar Karbala, zuwa ga makoma ta dawwama kuma fitilar ma'abuta 'yanci karkashin jagorancin Husaini (a.s), wanda ya bi tafarkin fuskantar ja'irar gwamnatin kama-karya. A daidai wannan lokaci dai, Imam Husaini (a.s) yana tunasar (da mutane) hijiran da mahaifinsa Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya yi ne daga Makka zuwa Madina, a ranar da ya sadaukar da ransa yana tare da Fadimomi, yana mai kalubalantar girman kan Kuraishawa da kuma dagawarsu, sabanin irin al'adar masu hijira a wancan lokacin wadanda suke amfani da duhun dare, amma shi da tsakar rana ya yi nasa hijirar.
Hakika karfin ruhin mahaifinsa (Aliyu) na tare da shi, haka nan kuma zuciyar wannan jarumin bawan Allah tana bugawa kamar wata gagarumar ganga a cikinsa. A lokacin iyalan gidansa da kuma masoyansa suna cikin tsoron kan hatsari da kuma cutarwar da mahukuntan wancan lokacin za su yi masa, kamar yadda suka aikata kwanaki biyu da suka wuce ga Ibn Zubair, sai dai ba su same shi ba saboda ya bi hanyar da ba a saba bi ba. Don haka sai suka shawarce shi da ya dau wata hanya ta daban, don kauce wa idanuwa, amma Husaini (a.s) ya ki amincewa da hakan, yana mai jaddada cewa tafiyar tasa za ta kasance ne a fili kuma bayan ya sanar da jama'a. Hakan kuwa a matsayin kafa hujja da kuma motsa lamirin al'umma ne, kowa da kowa ya san batun hijirar tasa har ma dai su dinga tambayar cewa, 'me yasa Husaini ya bar garin kakansa Manzon Allah (s.a.w.a) alhali kuwa shi ne shugabanta kuma wanda ya fi daukaka cikin mutanensa'?
Don mutane su yawaita magana kan wannan tafiya tasa, don tafiyar ta tashi daga boyayyiya zuwa ga wani yunkuri da kuma aiki na fuskantar hukuma, don sanya tabbaci a cikin zukatan al'umma da kuma kawar da lullubin tsoro da kuma tarbiyyantar da ruhin tsayin daka da kuma jarunta. Shi dai ya shirya wa gwagwarmaya da kuma fuskantar ja'irar hukuma, kuma lalle babu tsoro babu kuma komawa da baya, don haka ne ma ya ke dada jaddada wa iyalansa wadanda suka ce masa:
"Ai da ka kauce wa babbar hanya kamar yadda Ibn Zubair ya aikata don kada masu nemanka su same ka, da ya fi". Sai ya ce musu:
"A'a wallahi! Ba zan taba kauce mata ba har sai Allah Ya hukumta abin da Ya ke son hukumtawa(6)".
Haka dai wannan tawaga ta kama hanya da nufin kaddamar da wani gagarumin yunkuri, jagoran wannan yunkuri kuwa shi ne Husaini (a.s), kuma babu wani wanda bai san wannan Shugaba kana Jagora mai girma ba.
Bayan fitarsa da Madinan dai, al'umman garin da suka hada da Muhajirai da Ansar, ciki kuwa har da wasu sahabban Manzon Allah (s.a.w.a) sun kasance su kan taru suna tattaunawa kan wannan lamari: Lalle jikan Manzon Allah (s.a.w.a) ya tafi, ya bar wannan gari na kakansa (s.a.w.a), yana mai nufin wani al'amari mai girman gaske. Ya ki yin mubaya'a da kuma mika wuya ga gwamnatin Yazid, shin me al'umma take jira?.
A halin da ake ciki ga wani shamaki na bakunta da nisa nan ya shiga tsakanin gidajen Ali, Husaini da kuma Zahra (a.s). Garin Madina na cikin damuwa da kuka saboda barinsa da Husaini ya yi, kamar yadda kuma zukatan al'ummar garin ke cike da bakin ciki da tsoro da kuma damuwa, suna tsoron abin da zai faru nan gaba. Suna cikin tsoron cewa mabiya Husaini (a.s) za su ha'ince shi da kuma barinsa ya fada hannun makiya, kuma ta haka wannan tauraro mai haske zai bace daga sararin samaniyyar garin wanda kuma sama ba zata iya samar da wani kamarsa ba.
Ga gidansa nan cike da duhu, gidan da a jiya yake cike amma a yau ga shi an kaurace masa. Wannan gida da a jiya ake raya shi da salla, kana kuma sautukan masu sallar dare suke daukakuwa daga bangarorinsa, kuma mutane suke ganin abin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya bari, tsokar Zahra da kuma sauran Mutanen Mayafi (Ashab al-Kisa'), to amma a yau ba abin da ake ji in ban da kukan masu tausayawa masu hijiran.
A nan ne fa Husaini (a.s) ya kasance, a kuma wannan gidan ne Ahlulbaiti (a.s) suke taruwa, a nan ne dai Imam Husaini (a.s) ya ke nuna kauna da soyayyarsa ga Sukaina, 'yarsa, da kuma al-Rabab, matarsa, yana cewa:
Na rantse da raina ni ina son gidan da,
Sukaina da al-Rabab suke ciki.
Ina sonsu kuma zan ba da dukkan abin da na mallaka,
Kuma ba zan damu da duk wata suka kan hakan ba(7).
Wannan gida dai shi da kansa ya kasance waje ne na nuna rashin amincewa, kuma matattara na gwagwarmaya; kana kuma sauti dake bayyanar da labarin mutane, tun daga farko har zuwa wannan karshe mai cike da bala'i.
A daidai wannan lokaci dai Imam Husaini (a.s) yana cikin tafiyarsa cikin hamada mai kuna da kuma ban tsoro. Ya isa garin Makka ne kuwa a daren Juma'a, rana ta uku cikin watan Sha'aban, yana mai karanta wannan aya:
( æáóãøóÇ ÊóæóÌøóåó ÊöáúÞóÇÁó ãóÏúíóäó ÞóÇáó ÚóÓóì ÑóÈøöí Ãäú íåúÏíäí ÇáÓøóÈöíáö )
"Kuma a lokacin da ya fuskanci wajen Madyana, sai ya ce: "Ina fatan Ubangijina Ya shiryar da ni a kan madaidaiciyar hanya(8)".