Karbala'….Karbala'….gonar takubba, jini kana kuma ma'abuciyar motsa alkalumma.
Karbala kalmar gaskiya…abin maganar bakunkunan zamani.
Karbala…alamar zafi da sosa rai.
Hakika babu yadda za a iya mancewa da Karbala duk tsawon tarihi, hasken ranarta ba za ta taba faduwa ba cikin tarihi. Haka nan kuma babu yadda za a yi dacin abin da ya faru a Karbala ya gushe daga zuciyar duk wani mutum ma'abucin 'yanci.
Ruwan jini ya zubo a Karbala haka nan kuma an samu kafuwar shahidai da kuma yaduwar kiraye-kirayensu a zukata. Haka nan kuma sautin muryar Imam Husaini (a.s) da take cike da jarunta ta dagu a wannan guri kuma ta shiga ko wane lungu na tarihi. Hakika wannan murya ta kasance tsawa da aradu da ke razana da kuma sanya tsoro cikin zukatan azzalumai. Haka nan kuma ta kasance aman wuta ne da ke jijjiga kujerun azzalumai, wacce kuma take motsa zukatan ma'abuta 'yanci da kuma rura wutar bore da mikewa don fuskantar azzalumai da kuma yin Jihadi. Har ya zuwa yanzu wannan kalami nasa na nan yana yawo a kunnuwan al'umma:
"Na rantse da Allah, ba zan mika maka hannuwana (mubaya'a) kamar wulakantaccen mutun ba, haka nan kuma ba ja da baya kamar baya ba".
Abin tambaya a nan shi ne, wai shin wane ne Imam Husaini ne? Mene ne hakikani da kuma dalilan da suka sa ya banbanta da sauran mutane? To yayin amsa wadannan tambayoyi dai muna iya cewa: shi dai wannan cikakken mutum abin kaunar kowa, shi ne jikan Manzon Allah (s.a.w.a), da ga Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib da kuma Fatimat al-Zahra, 'yar Manzon Allah (s.a.w.a).
An haifi Imam Husaini (a.s) ne a garin Madina al-Munawwara a ranar 5 ga watan Sha'aban shekara ta 4 bayan hijira(1), wasu ruwayoyin kuma sun ce an haife shi ne a ranar 3 ga wannan wata na Sha'aban shekara 4 bayan hijira. Wannan haihuwa ta sa dai ta sanya iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) cikin farin ciki, don haka ranar suna sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya sanya masa suna Husain(2).
Imam Husaini (a.s) dai ya girma ne karkashin kulawan Kakansa Manzon Allah (s.a.w.a) da Mahaifansa, Aliyu bn Abi Talib da Fatima al-Zahra (a.s), inda ya sha daga kasko kyawawan dabi'u na annabci. Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance yana tsananin sonsa, ta yadda har ya kan dauke shi tare da wansa Imam Hasan (a.s) yana mai sanar da sahabbansa cewa:
"Ya Allah! Ina sonsu Ka so masu sonsu(3)".
Har ila yau ya kara tabbatar da soyayyarsa ga Hasan da Husaini (a.s) inda yake cewa:
"Wadannan 'ya'yaye nawa guda biyu su ne furen raina a wannan duniya(4).
"Duk wanda ya so Hasan da Husaini to ya so ni, wanda kuma ya ki su, to ya ki ni(5)".
An ruwaito cewa wata rana Manzon Allah (s.a.w.a) yana salla, sai Hasan da Husaini (a.s) suka hau bayansa, da ganin haka sai wasu daga cikin sahabbansa suka rugo da nufin saukar da su daga bayan, sai ya ce musu:
"Ku bar su, mahaifana biyu su kasance fansa gare su, duk wanda yake so na, dole ne ya so su(6)".
An ruwaito shi kuma yana cewa:
"Duk wanda yake son ya ga wani mutum daga mutanen aljanna, to ya kalli Husaini(7)".
Ta haka ne dai Manzon Allah (s.a.w.a) ya bayyanar da matsayin Imam Husaini (a.s) tun yana karami ga al'umma don kada wata rana ma su yi karen tsaye wa hakkokinsa.
To amma abin bakin ciki, bayan dan wani lokaci sai al'umma ta mance da wadannan wasiyyoyi na Ma'aiki (s.a.w.a), inda suka halalta jinin wannan jika na Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma keta huruminsa. Ibn Umar ya tuna wa al'umma wannan lamari, yayin da aka tambaye shi:
An ruwaito Ibn Umar yayin da aka tambaye shi hukumcin kashe kuda ga mutumin da ke cikin haramin (aikin hajji), sai ya ce: "Mutanen Kufa suna tambayata kan kashe kuda, alhali kuwa sun kashe dan 'yar Manzon Allah (s.a.w.a), duk kuwa da cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Su (hasan da Husaini) ne furen zuciyata a nan duniya(8)".
Har ila yau tarihi ya ba mu labarin yadda Anas bn Malik ya kwatanta wasu matsaya guda biyu, ta farko ta Manzon Allah (s.a.w.a), lokacin da yake sumbantan bakin Imam Husaini yana mai rungume shi, dayar kuwa ta Ibn Ziyad, gwamnan Umayyawa na garin Kufa, bayan shahadar Imam Husaini, lokacin da ya ga Ibn Ziyad yana wasa da kan Imam Husaini (a.s) yana dukansa da bulaliyar da take hannunsa, yana mai cewa: "Lokacin da aka kashe Husaini bn Ali (a.s), sai aka zo da kansa wa Ibn Ziyad, sai ya sanya bulalarsa yana dukan hakwaransa yana cewa:
"Lalle yana da kyau", sai na ce bari in dame ka, lalle na ga bakin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) yana sumbantan wannan guri da bulaliyarka take bugu". Ibn al-Dhahhak ne ya fitar da wannan labarin(9).
Amma Halifa Abubakar al-Siddik kuwa cewa ya yi:
"Na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Hasan da Husaini su ne shuwagabannin matasan Aljanna(10)".
To haka dai Imam Husaini (a.s) ya kasance a zuciyar Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma dabi'unsa. Ya tashi ne a mafi girma da daukakan gidajen Musulunci, shi ne kuwa gidan Ma'aiki (s.a.w.a), ta haka ne ya zamanto mai kyawawan dabi'u, tsoron Allah, tsantsaini, ikhlasi, gudun duniya, ibada, karfin ruhi, jaruntaka, mai damuwa da Musulunci da kuma al'amurran al'umma, ma'abucin siffofin shugabanci, marikin gaskiya, mai karfin iko(11), ba ya tsoron zargin mai zargi cikin al'amurran Ubangiji da dai sauran siffofi abin yabo. Saboda irin wadannan siffofi da suka zama tilo cikin al'umma, ya sa Imam Husaini (a.s) ya zamanto wani karfi abin girmamawa cikin tarihin Musulunci, kana kuma rayayyen iko mai tasiri cikin dukkan al'ummomi. Haka nan kuma Imam Husaini (a.s) ya kasance abin koyi cikin zuciyar duk wani mutum ma'abucin neman 'yanci wanda ya san hakki da kuma girman dan'Adamtaka.
Hakika dukkan musulmi sun yi amanna da son Ahlulbaiti (a.s), haka nan kuma sun so Imam Husaini (a.s) a matsayinsa na daya da cikin Limaman Ahlulbaiti (a.s), don haka ne al'umma suka dauki rashinsa a matsayin wata babbar azaba da bala'i da ya same su. Saboda haka Imam Husaini (a.s) ya kasance ma'abucin matsayi mai girma da kuma kauna da soyayya a zukatan al'umma. Irin wannan kauna da soyayya ce ta sa mawaka daban-daban cikin karnoni suka tsara wakoki na yabo da jinjinawa gare shi da kuma nuna bacin ransu da abin da ya same shi.
Alkalumma sun yi rubutu a kansa, sai dai kuma alkaluma ba su bushe ba haka nan kuma bayanai ba su kare ba dangane da matsayinsa.
Hakika an samu yunkure-yunkure duk da sunansa, haka nan kuma jini bai daina zuba ba kamar yadda kuma azama ba ta kare ba.
Haka nan an daga take da sunansa wanda ya kasance sauti da ba ya gushewa.
Hakika, jin shu'urin gazawa wajen kare hurumin Ahlulbaiti da ya yi katutu a zukatan al'umma bayan shahadar Imam Husaini (a.s) ya sa wasu al'umma suka tashi suna masu neman daukan fansa jininsa, lamarin da ya haifar da yunkure-yunkure irin na su al-Mukhtar da kuma na Tawwabun, haka nan kuma lamarin ya ci gaba har zuwa wannan zamani namu.
Har ya zuwa yanzu al'umman musulmi sukan zauna don tunawa da wannan babban bala'i na Ashura, tun daga ranar shahadar Imam Husaini (a.s) har zuwa yau din nan, ba su yi kasa a gwuiwa ba haka nan kuma hawayensu ba su bushe ba. Lalle wannan bala'i ya kasance rayayye wanda yake tare da zuciyar dan'Adam, kuma yana tare da shi da kuma yin tasiri cikin al'amurransa.
Hakika wannan makaranta ta mawaka da kuma mimbarorin tunawa da Imam Husaini (a.s) sun kasance rayayyu masu raya wannan bala'i da ya same shi da kuma isar da shi ga al'ummomi masu zuwa.
Ta haka ne Karbala ta kasance mafifici mai ruruta wutan yunkure-yunkure da kuma taken ma'abuta yunkuri, kana shi kuma Imam Husaini (a.s) ya kasance abin kauna da so a zukatan dukkan ma'abuta 'yanci.
Shi ya kasance misali na na ma'abutan 'yantaccen ruhi…misali na mutum ma'abucin yunkuri mai taimakon marasa galihu da wadanda ake zalunta, kuma daya daga cikin makusantan (Annabi) da Allah Madaukakin Sarki Ya yi umarni da a so su:
( قل لا اسالكم عليه اجراً إلا الموَدَّةَ في القُربى ومن يقْتَرِف حَسَنةً نزِدْ لَهُ فيها حسْنَا ) "Ba na tambayarku wata lada a kansa face dai soyayya ga makusanta, kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, za Mu kara masa kyau a cikinsa...". (Suratush Shura: 42: 23).
Kuma yana daga cikin Ahlulbaitin da Allah Ya tafiyar da kazamta daga gare su, yayin da Yake cewa:
( إِنَّمَا يُريدُ اللهُ لِيُذهِبَ عنكُمُ الرِّجْسَ أهلَ البيتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطهيراً ) "Allah kawai Ya na nufin Ya tafiyar da kazamta ne a gare ku, Ya Mutanen babban gida, kuma Ya tsarkake ku tsarkakewa". (Suratul Ahzab: 33:33).
Haka nan kuma yana daga cikin wanda Manzon Allahya yi mubahala da su tare Kiristocin Najran:
( فَمن حَاجَّكَ فِيهِ مِن بَعدِ ما جَاءَكَ مِنَ العِلمِ فَقُلْ تَعَالوا نَدعُ أبناءَنَا وأبناءَكُم ونِساءَنا ونِسَاءَكُم وأنفُسَنا وأنفُسَكَم ثُم نَبتَهِلْ فَنَجعَلْ لَّعنةَ اللهِ عَلى الكَاذِبينَ )
"To wanda yayi musu da kai a cikinsa, bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to kace: Ku zo mu kirayi 'ya'ya-yanmu da 'ya'yayanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa'annan kuma mu kankantar da kai, sannan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata". (Suratu Al'Imrana: 3: 61).