|
|
|
|
| |||
|
Daga: Muhammad Awwal Bauchi IRIB-Tehran - I.R.of Iran awwalubauchi@yahoo.com ________________________ Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Kasar Iraki dai tana daga cikin kasashen musulmi da suke da wuraren ziyara kana kuma masu tsarki a idanuwan al'ummar musulmin duniya, a takaice ma dai ita ce ta biyu wajen yawan irin wadannan wajaje idan ka cire kasar Saudiyya. A kowace shekara dai miliyoyin al'ummar musulmi ne musamman ma dai mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) suke kai ziyara wadannan wajaje musamman ma bayan kawar da gwamnatin kama-karya ta Saddam Husaini, sabanin kasar Saudiyya inda jikokin Sa'ud da muggan malamansu mabiya tafarkin wahabiyanci suke hana al'umma ziyarta irin dimbin wurare masu tsarki da suke wajen face 'yan kadan din da suka rage su din ma dai cikin sanya ido, don kuwa da dama daga cikinsu 'ya'yan gidan Sa'ud sun ruguza su. Don haka abin da ke biye takaitaccen bayani ne kan irin wadannan wajaje masu tsarki da suke Iraki, gari bayan gari: 1- Najaf al-Ashraf:
1- Haramin (hubbaren) Amirul Muminina Ali A wannan guri akwai kaburbura kamar haka:
2- Makabartar Wadi'us Salam Wannan makabarta ce da aka bisne Manyan Annabawa da bayin Allah daban-daban, daga cikin wadanda suke kwance a wajen har da:
3- Kabarin Kumail bn Ziyad (r.a.) daya daga cikin sahabban Imam Ali (a.s). 4- Kabarin Rashid al-Hijri (r.a.), daya daga cikin sahabban Imam Ali (a.s). 5- Masjid Hannana: Wannan wani masallaci ne da ke tsakanin Kufa da Najaf, dalilin daukakan wannan masallaci kuwa shi ne an ruwaito cewa lokacin da Imam Hasan da Husaini (a.s) suka dauko jikin Imam Ali (a.s) mai tsarki bayan shahadarsa sun tsaya a wannan masallaci. Sannan kuma an ce an bisne wani sashi na fatar kan Imam Husaini (a.s) a wajen. 2- Karbala:
1- Haramin Imam Husaini A cikin wannan harami akwai kabarurruka kamar haka:
2- Haramin Abul Fadhl al-Abbas, dan Imam Ali kana kanin Imam Husaini kuma mai rike da tutarsa (a.s). 3- Kabarin Habib bn Mazahir, daya daga cikin sahabban Imam Husaini (a.s). 4- Kaburburan sauran shahidan Karbala da suka yi shahada tare da Imam Husaini. 5- Kabarin Ibrahim, dan Imam Musa al-Kazim, limami na bakwai (a.s). 6-Lambun Imam Ja'afar al-Sadik, limamin Ahlulbaiti na shida (a.s). 7- Lambun Imam al-Asr (ATFS) 8- Hubbarren Hur bn Yazid al-Riyahi, daya daga cikin sahabban Imam Husaini (a.s), kimanin kilomita uku daga Karbala. 9- Hubbaren Aun, dan Sayyida Zainab, 'yar'uwar Imam Husaini (a.s), kimanin kilomita shida daga Karbala. 3- Kufa:
1- Masallacin Kufa A cikin wannan guri akwai:
2- Gidan Amirul Muminina Ali (a.s). 3- Hubbaren Sayyida Khadija al-Sughra, 'yar Imam Ali (a.s). 4- Hubbaren Annabi Yunusa (a.s), kusa da bakin kogi. 5- Masjid al-Sahla. A wannan wajen akwai:
6- Hubbaren Maytham al-Tammar, sahabin Imam Ali (a.s). 7- Masallacin Zaid, kusa da Masjid al-Sahla. 8- Masallacin Sa'asa'a bn Sauhan, sahabin Imam Ali (a.s). 4- Kadhimayn (Kazimiyya):
1- Hubbaren Imam Musa al-Kazim da Imam Muhammad al-Jawad Baya ga wadannan Imamai (a.s), akwai kuma manyan malamai da aka bisne a wajen irin su Shaikh al-Mufid mawallafin shahararren littafin nan na al-Irshad, da kuma Sayyid Murtadha da kuma Sayyid Radhi. 5- Samarra:
1- Hubbaren Imam Ali al-Naki da Imam Hasan al-Askari Hubbaren dai yana dauke ne da:
6- Bagadaza: 1- Akwai kabarurrukan wakilan Imam al-Mahid (a.s) na musamman lokacin karamar buyarsa (Ghaibat al-Sughra), su ne kuwa:
2- Kabarin Kambar, bawan Amirul Muminina Ali (a.s). 3- Kabarin Shaikh al-Kulayni, wanda ya rubuta littafin al-Kafi. 7- Mada'in: 1- Kabarin Salman al-Farisi, sahabin Manzon Allah (s.a.w.a). 2- Kabarin Hudhaifa bn Yaman, sahabin Manzon Allah (s.a.w.a). 3- Kabarin Jabir bn Abdullah al-Ansari, sahabin Manzon Allah (s.a.w.a). 4- Masjid al-Jum'a, kusa da kabarin Salman al-Farisi. 8- Basra: 1- Masallacin Amirul Muminina Ali (a.s). 9- Hillah: 1- Kabarin Kasim, dan Imam Musa al-Kazim (a.s). 2- Kabarin Annabi Ayyub (a.s). 3- Kabarin Annabi Daniel (a.s). 4- Kabarin Annabi Zulkifl (a.s). 10- Musayyab: Wannan waje yana nan ne tsakanin Karbala da Kazimiyya, kuma a wajen ne hubbaren 'ya'yan Muslim bn Akil guda biyu, wato Muhammad bn Muslim bn Akil da Ibrahim bn Muslim bn Akil suke.
|
||||