|
|
| |||
|
________________________
Duk wanda ya karanta tarihin Imam (a.s) zai fahimci cewa ya dauki wani tafarki da ke tabbatar da manufa. Daga cikin abubuwan da wannan tafarki ya kunsa kuwa har da:
1- Aikin Koyarwa:
Imam Sajjad (a.s) dai ya dauki masallacin Manzon Allah (s.a.w.a) mai girma da kuma gidansa mai albarka a matsayin wani waje na watsa ilmin Musulunci na hakika. Cikin shekaru talatin da biyar - wato lokacin imaman-cinsa kenan - duniya ta shaida irin ayyukan da ya gudanar na yada ilmi.
A cikin wadannan shekaru Imam (a.s) ya janyo dalibai masu karatun Musulunci a dukkan bangarori zuwa gare shi, ta yadda har ya samu damar samar da wata makaranta ta ilmi ma'abuciyar haske da ta samu yaye dalibai masana, ma'abuta ra'ayi, maruwaita da kuma malumman fikihu.
A wannan makaranta dai, Imam (a.s) ya kasance ya kan karantar da ingantattun hadisan Ma'aiki (a.s) daga mafi ingancin tushen da babu wani da zai iya yin shakku kansa. Wannan tushe dai ya kan fara ne da shuwagabannin matasan aljanna, Hasan da Husaini (a.s), ya wuce zuwa
ga Amirul Muminina (a.s) kana ta karasa kan Manzon Allah (s.a.w.a).
Babu shakka wannan madaukakin tafarki a kan kansa ya kan shiryar zuwa ga ingantaccen tunani, fikihu, dabi'u da kuma shiryarwa zuwa ga madaidaiciyar hanya bugu da kari kan jan hankalin mutane wajen nesantar gurbata cikin tunani da aiki.
2- Kula da Matsalolin Al'umma:
Imam Sajjad (a.s), kamar sauran Imaman Ahlulbaiti (a.s), ya ba da gagarumin kulawa ga al'umma ta hanyar kyautata alaka da ita da kuma mu'amala mai kyau. Imam dai ya kasance uba mai tausayi, shugaba mai hikima kana kuma likita mai magance cututtukan da suke damun al'umma duk tsawon lokacin imamancinsa.
An ruwaito dansa Imam Muhammadu al-Bakir (a.s), dangane da baban nasa, yana cewa: "Ya kasance ya kan ciyar da gidaje dari na fakiran mutanen Madina, ya kasance ya kan ji dadi idan marayu, fakirai, marasa lafiya da miskinan da ba su da abin hannu suka ziyarce shi yayin cin abinci, ya kasance ya kan ciyar da su, wadanda suke da
iyalai kuma daga cikinsu, ya kan dau abinci ya kai musu(1)".
Har ila yau ya kasance ya kan shayar da makwab-tansa raunana, wadanda ba za su iya shayar da kansu ba, don haka sai ya debo musu ruwa cikin dare da kai musu gidajensu. Kamar yadda kuma ya kan yawaita sayen bayi da kuma 'yantar da su daga bauta.
Saboda yawan zama da kuma mu'amalar da yake yi da sassa daban-daban na al'umma, wata rana daya daga cikinsu ya bayyana masa cewa hakan bai dace da matsayin da yake da shi ba, yana mai ce masa: 'Me ya sa kake zama da dukkan nau'i na mutane, sai Imam (a.s) ya ce masa: "Ni ina zama ne da mutumin da zan amfana a bangaren addinina ta hanyar zama da shi(2)".
3- Raya Juyayin Shahadar Husaini (a.s):
Tun bayan waki'ar Karbala dai, Imam Sajjad (a.s) ya kasance ya kan shirya taron juyayin wannan musiba a gidansa don rayar da hakan a zukatan al'umma da tarihinta. Wadannan tarurruka dai sun kasance tunatarwa ne ga akidojin Musulunci wadanda don su ne Imam Husaini (a.s) ya yi wannan yunkuri nasa, ya sadaukar da iyalai da sahabbansa don su.
4- Addu'a:
Tarihin Imam Sajjad (a.s) na cike da addu'oi da suke cike da hikima da kamala. Wadannan addu'oi dai sun kasu kashi biyu a bangaren kamala da kuma alaka da Ubangiji Madaukakin Sarki. Kashin farko ya kunshi bangare na ibada, dayan kuwa bangare na zamantakewa da ke da alaka da tafarkin gyara da yake jagoranta.
Wadannan addu'oi dai su ne aka tara su cikin littafin nan da ake kira da 'Sahifa al-Sajjadiyya' da a halin yanzu yake yawo a hannun muminai.
|
||||