Siyasar Mayar Da Martani:

________________________

Gwamnatin Umayyawa ta wancan lokacin karkashin jagorancin Abdulmalik ta jaddada siyasar nan ta kama-karya da aka san Umayyawan da ita ta hanyar ayyana shahararren dan ta'addan nan mai kishin jinin muminai wato Hajjaj bn Yusuf al-Thakafi a matsayin gwamnan Kufa - helkwatar Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) - da nufin tsoratar da al'umma da kuma cin mutumcin masu adawa da gwamnatin da kuma riko da tafarkin gaskiya.

A wannan lokacin Hajjaj ya haifar da tsoro a cikin zukatan mutanen Kufa ta hanyar kashe muminai daga mujarradin tuhuma ko kuma zato kawai. Ya ishe mu misali na irin kisan gillan da Hajjaj ya aikata fadin Imam Bakir (a.s) yayin da yake siffanta irin ta'addancin da ya yi da cewa: "Daga nan sai Hajjaj ya zo inda ya kashe su - wato mabiya Ahlulbaiti - kisan gilla, yana mai aikata hakan daga dukkan wani zato ko kuma tuhuma, ta yadda har sai da ya kai mutum ya kan gwamnace a ce masa kafiri ko kuma zindiki da a ce masa dan shi'an Ali(1)".

"Hajjaj ya mutu ne a shekara ta hamsin da biyar a tsakiyar kasar Iraki…alhali kuwa kididdiga ta nuna cewa mutanen da ya kashe a cikin kurkukunsa da yakin da ya kaddamar akan al'umma sun kai mutane dubu dari da ashirin, sannan kuma ya mutu ya bar mazaje dubu hamsin da mataye dubu talatin a gidan yarinsa cikinsu kuwa har da budurwaye dubu sha shida marasa aure. Ya kasance ya kan tsare mata da maza a waje guda, don cutarwa kuma ya gina wannan gidan yari nasa ba tare da rufin da zai kare mutanen da yake rike da su daga zafin rana lokacin bazara ko kuma ruwan sama da sanyi lokacin damina(2)", lamarin da ke nuni da irin bala'in da mabiya Ahlulbaiti (a.s) suka fuskanta a wancan lokacin.

Bisa la'akari da ci gaban lalacewar yanayi bayan mutuwar Abdulmalik da kuma darewar mulki da dansa Walid ya yi, duk da haka Imam Sajjad (a.s) ya ci gaba da tafarkinsa na gyaran al'umma da kuma shiryar da su, bugu da kari kan yin umarni da abubuwa masu kyau da hani da munana.

Wannan lamari dai ya kasance abin tsoro da ta da hankulan mahukuntan Umayyawa ma'abuta manufar lalata sakon Ubangiji (Musulunci), don kuwa sun fahimci cewa kawo karshen wannan harka ta Imam ba zai yiyu da ta'addanci akan mabiya Ahlulbaiti (a.s).

Don haka sai suka fara kulla kulleleniya na ganin bayan Imam Sajjad shi kansa, hakan kuwa ya faru lokacin da Sulaiman bn Abdulmalik ya kashe shi ta hanyar sa masa guba cikin abinci.

Ta haka ne rayuwar wannan Imami mai girma ta kawo karshe, to amma fa ra'ayi da kuma manufofinsa sun ci gaba da wanzuwa da haifar da alheri da kuma shiryarwa.

Ta hakan ne kuma Imam Sajjad (a.s) ya koma ga Mahaliccinsa da kuma saduwa da iyaye da kakanninsa, limaman shiriya.

Amincin Allah ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi, ranar da ya yi shahada da kuma ranar da za a tashe shi alhali yana rayayye.




____________
1- Sharh Nahjul Balagah na Ibn Abil Hadid, juzu'i na 11 shafi na 44.

2- Muruj al-Zahab na al-Mas'udi, juzu'i na 3, shafi na 175.