|
|
| |||
|
________________________
Cikin iko da hikimar Allah, Imam Sajjad (a.s) ya rayu bayan kisan gillan da Umayyawa suka yi wa zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a) a Karbala, cikin wani irin yanayi mai ta da hankali da Imam Sajjad din da kansa ya bayyana shi lokacin da Manhal
bn Umar ya tambaye shi cewa ya ya ka wuni Ya dan Manzon Allah?, sai yace masa: "Mun wuni kamar yadda Bani Isra'ila suka wuni a hannun mutanen Fir'auna, suna yanka 'ya'yayensu maza suna rayar da matayensu(1)".
Cikin kaddaran Ubangiji Madaukakin Sarki Imam Sajjad (a.s) ya tsira daga wannan kisan gilla alhali a lokacin yana dan shekara ashirin da uku a duniya. Hakan kuwa ya faru ne saboda rashin lafiyan da ya kama shi lokacin yaki,
lamarin da ya sauke masa nauyin yin jihadi da ke kansa.
Gama wannan yaki na al-Dif (Karbala) ke da wuya sai al-Sajjad (a.s) ya dau ragamar harkar kawo canji da gyara wanda mahaifinsa ya fara. Wannan jagoranci na Imam Sajjad (a.s) dai yana da wasu abubuwa guda biyu:
Hakika Umayyawa da 'yan amshin shatansu sun riga da sun san irin matsayi da daukakan da Husaini da Ahlulbaiti (a.s) suke da su a zukatan al'umman musulmi, kuma sun riga da sun fahimci cewa kashe Imam Husain (a.s) da sahabbansa a Karbala zai
janyo fushin al'umma a kansu, don haka ne suka tsara wasu tsare-tsare da kuma ba da dukkan himmarsu wajen ganin sun sanya wani shamaki kan wannan danyen aiki da suka aikata, don su sami damar gamawa da duk wani mayar da martani da za su iya fuskanta, musamman ma a kasar Sham.
Don haka ne sai suka sanya kafafen watsa labaransu da kuma 'yan amshin shatansu suka fara aiki da kuma nuna wa mutane cewa Imam Husain da sahabbansa bijirarru ne.
Ya zuwa wani haddi dai wadannan farfagandoji sun sami nasara a Sham kan kokarin da aka yi na nuna karyan wannan da'awa ta Umayyawa da kuma bayyanar da hakikanin manufofin wannan yunkuri na Husaini (a.s) da kuma matsayin da yake da shi a idanuwan musulmi.
To sai dai Imam Sajjad (a.s) da sauran gwarazan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) irinsu Zainab da Ummu Kulthum da sauransu sun tsaya tsayin daka wajen ganin bayan wannan bakar siyasa ta Umayyawa ta rufe wannan danyen aiki nasu.
A Sham, lokacin da aka shigo da wadannan fursunonin yaki na gidan Manzon Allah (s.a.w.a), sai wani tsoho ya dubi Imam Sajjad (a.s) ya ce masa: 'Godiya ta tabbata ga Ubangiji da Ya hallakaku Ya kuma ba wa Amir (Yazid) nasara a kanku'.
Sai Imam Sajjad (a.s) ya amsa masa da cewa: "Ya Kai dattijo, shin kana karanta Alkur'ani?.
Sai ya ce masa: Na'am.
Sai Imam (a.s) ya ce: "Shin ka taba karanta ayar:
( قل لا اسالكم عليه اجرا الاالمودة في القربي),
Shin ka taba karanta ayar: (واتذ القربي) da kuma fadin Allah (واعْلموا أنَّما غنمتم من شيء فأن للهِ خُمْسهُ و للرَّسول ولذي القربي) sai dattijon ya ce lalle na karanta wadannan ayoyi.
ai Imam (a.s) ya ce: "Wallahi mu ne wadannan makusanta da ake magana cikin wadannan ayoyi".
Sai Imam ya sake tambayarsa: Shin ka taba karanta ayar:
(إنَّما يُريدُ الله لِيُذْهِبَ عنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَيْتِ ويُطهِّرَكُمْ تَطْهيراً )
Sai dattijo ya ce: 'na'am'.
Sai Imam (a.s) ya ce masa: "To mu ne Ahlulbaitin da Allah Ya kebance mu da tsarkakewa".
Sai dattijo ya ce: Don Allah ku ne wadannan mutane?
Imam (a.s) yace masa: "Babu shakka mu ne wadannan mutane".
Nan take sai wannan dattijo yayi nadama kan maganar da ya yi, kuma ya yi Allah wadai da Umayyawa da mabiyansu(2).
Don karya kashin bayan wannan farfaganda ta Umayyawa da kuma bayyanar da munanan ayyukan Yazid, Imam Sajjad (a.s) ya fuskanci Yazid bn Mu'awiyya da dukkan hakimominsa shuwagabannin bata ya gabatar da jawabinsa yana mai nuna irin bakar siyasar Umayyawa ta zalunci da kuma bayyanar da matsayin da wadannan
fursunonin yaki na gidan Manzon Allah (s.a.w.a) suke da shi a wajen Allah da kuma idanuwan muminai. Ga kadan daga cikin abin da wannan jawabi nasa ya kunsa:
"Ya ku mutane! An ba mu wasu abubuwa guda shida an kuma fifitamu da abubuwa bakwai: An ba mu ilmi, hakuri, daukaka, fasaha, jaruntaka da kuma kauna a zukatan muminai. Sannan kuma an fifita mu da cewa: zababben Annabi yana daga cikinmu ne, siddik, dayyar, zakin Allah, zakin ManzonSa, kuma a cikinmu shugaban matayen
duniya Fatima al-Batul take da kuma jikokin wannan al'umma.
Ya ku Mutane! Wanda ya sanni, to ya sanni, wanda kuwa bai sanni ba, to bari in gaya masa kyakkyawar nasaba ta.
Ya Ku Mutane! Ni ne dan Makka da Mina, Ni ne dan Zam-zam da Safa, ni ne dan Wanda ya dau Bakin Dutse, ni ne dan mafi daukakan wanda ya yi dawafi, sa'ayi (tafiya tsakanin duwatsun Safa da Marwa) da aikin Hajji yana mai fadin Labbaikalla humma labbaik, ni ne dan wanda aka dauke shi akan Buraka kana Jibrilu ya isa da shi zuwa
'Magaryar Tukewa', har ya kasance gwargwadon zira'i biyu, ko kuma abin da ya fi kusa, ni ne dan wanda ya yi salla da Mala'ikun sama, ni ne wanda Ubangiji Madaukaki Ya yi masa wahayi da abin da Ya yi masa wahayi.
Ni ne dan Fatima al-Zahra, shugaban matayen duniya, kuma dan Khadija al-Kubra, ni ne dan wanda aka jefar cikin jini, ne dan wanda aka yanka a Karbala(3)".
Lokacin da ya gama fadin wannan matsayi nasa, sai ya juya, nan take sai mutane suka fashe da kuka mai tsanani yayin da suka ga gaskiya. Wannan lamari dai ya tilasta wa Yazid ya umarci ladaninsa da ya kira salla don ya katse Imam (a.s) daga wannan huduba tasa. Imam dai bai ce komai ba har sai lokacin da ladanin ya iso
ga kalmar "Ashhadu Anna Muhammaduan Rasulullah", sai Imam (a.s) ya juya ga Yazid ya ce masa:
"Wannan Annabi madaukaki, kakanka ne ko kuma kakana?, idan har ka ce kakanka ne to duk mutanen da suke nan sun san cewa karya kake yi, idan kuwa ka ce kakana ne, to me ya sa ka kashe mahaifina cikin zalunci da kiyayya, ka kwashe dukiyansa da kuma kama matayensa? To lalle bone ya tabbata gare ka matukar dai kakana
ya kasance mai jidali da kai ranar lahira".
Su kuwa matayen gidan Manzon Allah (s.a.w.a) sun turbude hancunan Umayyawa cikin turbaya da kuma kunyata su a gaban al'umman. Ana iya ganin hakan cikin hudubar da Sayyida Zainab ta gabatar a fadar Yazid a garin Damaskus da kuma jidalin da ya gudana a can.
Duk wanda yake bin gudummawar Imam Sajjad (a.s) bayan dawowarsa birnin Madina, zai ga cewa Imam (a.s) ya tsara wani tafarki na aiki bayan zurfi dubi kan yanayin al'umma na gaba daya bayan yunkurin Imam Husaini (a.s) bugu da kari kan gano bangarorin rauni na wannan yunkuri da kuma kokarin magance su.
Imam Sajjad (a.s) ya gudanar da nasa gudummawar ne ta hanyar karfafa da kuma gina tafarkin Musulunci na hakika tsakanin al'umma da kuma fadada bangarorin da zasu ba da tasu gudummawar. Imam (a.s) dai ya shirya wajen gabatar da wani sabon yunkuri na ruhi da al'adu a tsakankanin musulmi wajen sanya su kula da Musulunci da
kuma aikata dokokinsa a dukkan bangarori na rayuwarsu. A yayin gudanar da wannan aiki nasa dai, wasu abubuwa guda biyu sun taimaka masa wajen samun nasara, su ne kuwa:
Abu Na Farko: Irin tashin hankali da zaman dar-dar tsakanin al'umma da ya faru a mafi yawa daga biranen duniyar musulmi bayan faruwar waki'ar Karbala.
Abu Na Biyu: Irin karban Ahlulbaiti (a.s) hannu bibbiyu da al'umma suka yi sakamakon irin tausayawar da al'umma din suka nuna dangane da irin zaluncin da aka musu, musamman dai bayan shahadar Imam Husaini (a.s) a Karbala.
Imam Sajjad (a.s) dai ya yi amfani da irin wannan dama da kuma tausayawar da mutane suke nunawa Ahlulbaiti (a.s) wajen wayar musu da kai da kuma fahimtarsu ga Musulunci, kamar yadda kuma ya ba da kokari wajen yin bayani kan matsayin Ahlulbaiti (a.s) tsakanin al'umma. Ya ba da kokarinsa wajen samar da wasu masana wadanda
za su isar da sakon Musulunci na hakika, ba irin Musulunci da mahukuntan Umayyawa suka zo da shi ba.
|
||||