Yanayin Siyasa A Zamanin Imam Sadik (a.s):

________________________

Imam Sadik (a.s) dai ya rayu har na tsawon kimanin shekaru arba'in cikin mulkin Umayyawa, ya shaida irin zalunci da babakeren sarakunan Umayyawa a kan al'umma a yanayi na gaba daya sannan mabiya Ahlulbaiti kuma a yanayi na musamman.

To sai dai kuma a shekara ta 132 hijiriyya mulki ya koma hannun Banil Abbas bayan faduwa gwamnatin zalunci ta Ummayyawa, a nan ma Imam Sadik (a.s) ya rayu tare da halifan Abbasiyawan Abul Abbas al-Saffah da kuma wani lokaci na mulkin Abu Ja'afar al-Mansur, na kimanin shekaru goma.

Cikin wannan lokaci dai Imam Sadik (a.s) ya ga muhimman abubuwa guda uku:

1- Yunkurin Zaid bn Ali bn Husain na kawar da halifan Umayyawa Hisham bn Abdulmalik, wanda mulkinsa ke cike da zalunci da fasadi da ba za a iya kamanta shi ba, kana kuma al'umma sun fuskanci tsanani daga gare shi.

A wancan lokacin dai Umayyawan sun dora haraji mai tsananin gaske a kan dukiyoyin al'umma sannan a daidai lokaci guda kuma a takura musu rayuwa.

Umayyawa dai sun dauki dukkan mutane a matsayin bayinsu, don haka suke kuntata musu rayuwa da hana su jin dadi, alhali kuwa sun tara dukiya wa kawukansu da 'yan koransu suna cin karensu babu babbaka.

Zaid bn Ali dai ya kasance mutum bawan Allah mai tsantsaini da kuma tsoron Allah, jarumi mai yawan karatun Alkur'ani, don haka ne ya mike don fuskantar wannan mummunan yanayi na lalacewa. Mutane daga bangarori daban-daban na duniyar musulmi sun yi masa mubaya'a, to amma wannan yunkuri nasa bai cimma nasara ba don kuwa an kashe shi da kuma tsire gawansa tsirara har na tsawon shekaru hudu, kana daga baya kuma aka kona gawarsa da yin watsi da tokarta.

2- Faduwar gwamnatin Umayyawa da darewa kan karagar mulkin da Abbasiyawa suka yi da takurawa Ahlulbaiti (a.s) da suka yi.

3- Yunkurin Muhammadu bn Abdullah bn Husain (Nafs al-Zakiyya) a shekara ta 145 hijiriyya wajen fuskantar sarkin Abbasiyawa al-Mansur al-Abbasi, wanda ya kasance daga cikin sarakunan da suka fi nuna gaba da kiyayya ga Ahlulbaiti (a.s), kuma daga cikin wadanda suka fi kuntata wa al'umman musulmi.

Muhammadu dai ya yi yunkurinsa ne a garin Madina inda aka kashe shi a garin, sai kuma kaninsa ma ya kaddamar da nasa a garin Basra shi ma aka kashe shi a kusa da garin Kufa, ta haka ne dai wannan yunkuri shi ma ya kawo karshe ba tare da samun nasara ba. Bayan hakan kuwa mahukuntan sun kara matsa kaimi wajen cutar da Ahlulbaiti da mabiyansu wadanda suke adawa da mulkin Abbasiyawan.

Imam Sadik (a.s) dai ya ga dukkan wadannan abubuwa, ya ga irin wahalhalun da Ahlulbaiti (a.s) suka fuskanta haka nan ma sauran al'umman musulmi, to sai dai bai mallaki karfin da zai motsa don fuskantar hakan ba saboda wasu dalilai daban-daban.

Don haka ne Imam (a.s) ya koma yana tarbiyyantar da malamai da sauran al'umma da su kaurace wa azzaluman mahukunta da kuma yakansu amma fa ta hanyar watsa koyarwar Musulunci na hakika da kuma wayar da kan musulmi ta bangarorin akida, siyasa da fikihu. Kamar yadda kuma ya karantar da su duga-dugan shari'ar Musulunci bayyanannu, kamar cikin fadinsa cewa:

"Wanda ya yi uzuri wa wani azzalumi kan zaluncinsa, to Allah zai dora masa wanda zai zalunce shi, idan ya yi addu'a ba za a amsa masa ba….".

"Azzalumi (mai aikata zalunci) da wanda ya taimaka masa da kuma wanda ya yarda da hakan dukkansu 'yan'uwan juna ne"(1).

Bayan faduwar gwamnatin Umayyawa da darewa mulkin Abbasiyawa, ba a jima ba sai Abbasiyawan suka juya wa Ahlulbaiti (a.s) baya, suka koma suna cutar da su alhali kuwa taken da suka yi amfani da shi wajen kawar da Umayyawa shi ne kare Ahlulbaitin (a.s). Zaluncin Abbasiyawan dai bai tsaya kawai ga Ahlulbaitin ba face har mabiyansu suna fuskanci zalunci.

Mabiyan Ahlulbaiti sun fuskanci mafi girman zalunci daga wajen Abbasiyawa kamar yadda sauran al'umma ma suka fuskanci hakan, ta yadda hatta ma ana kiran halifansu na farko (wato Abul Abbas) da sunan al-Saffah (mashayin jini) saboda yawan zubar da jinin al'umma da ya yi. Wannan sarki dai ya takurawa Imam Sadik (a.s) kwarai da gaske.

Wannan irin mummunan yanayi na zalunci ga Ahlulbaiti da mabiyansu dai ya kara munana bayan da Abu Ja'afar al-Mansur ya dare karagar mulki bayan mutuwar al-Saffah, hakan kuwa ya biyo bayan irin tsoro da yake ciki ne saboda irin matsayin da Imam (a.s) yake da shi cikin al'umma sama da wanda shi (al-Mansur) din yake da shi. Don haka a lokuta da dama ya sha kiran Imam (a.s) zuwa Iraki daga Madina don bincikensa da kuma tabbatar da cewa ba ya jagorantar wata harka ta kawar da shi daga karagar mulki.

A wasu lokutan ma Al-Mansur din ya sha kokarin janyo Imam Sadik (a.s) zuwa ga bangarensa, to sai dai kuma bai ci nasaran hakan ba don kuwa shi da kansa yake kiran mutane (yake wajabta musu) kaurace ma mahukuntan Abbasiyawa. Don kuwa ya san cewa kaurace musu yana nufin matsaya ce ta Musulunci da ya wajaba musulmi su yi riko da ita kana kuma alama ce ta kauce wa hanya da mahukuntan suka yi.

Wata rana Al-Mansur ya rubuta wa Imam Ja'afar Sadik (a.s) wasika yana bukatan da ya matso kusa da shi, yana mai cewa:

"Me yasa ba ka ziyartanmu kamar yadda sauran mutane suke yi akai-akai?" sai Imam Sadik (a.s) ya rubuta masa cewa:

"Babu wani abu tattare da mu da muke jin tsoronka don shi, kuma ba ka da wani al'amari na lahira da za mu yi kwadayi kansa, kuma ba ka cikin wata ni'ima ballantana mu taya ka murna….".

Sai Mansur ya sake rubuto masa yana cewa: "Ka kusato mu don ka yi mana nasiha". Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa:

"Duk wanda yake son duniya ba ya maka nasiha, kamar yadda wanda ya ke son lahira ba ya zama da kai"(2).

Wasu ruwayoyi sun bayyana cewa al-Mansur ya sha kudura aniyar kashe Imam Sadik (a.s), to sai Allah Madaukakin Sarki ya kare shi daga wannan sharri.

Ibn Tawus cikin littafinsa Nahjul Da'awat ya ruwaito cewa Al-Mansur ya kirayi Imam Sadik (a.s) har sau bakwai da nufin ya kashe shi to sai dai Allah Ya kubutar da shi daga makircinsa.

Ta haka dai Imam Ja'afar bn Muhammad Sadik (a.s) ya rayu cikin wannan yanayi na siyasa mai wahalan gaske na zalunci, babakere da ta'addancin mahukunta, to sai duk da haka ya samu damar isar da sakon Musulunci da saukar da nauyin da ya hau kansa ta hanyar amfani da hikima, ilmi da kokarin da Allah Madaukakin Sarki ya arzurta shi da su.




____________
1- Al-Usul min al-Kafi na al-Kulayni, juzu'i na 2, shafi na 333 zuwa 334.

2- Al-Imam Sadiq na Muhammad Abu Zuhra, shafi na 139.