| |
Shahadarsa Imam Sadiq (a.s):
________________________
Bayan dukkan wannan rayuwa ta yada ilmi da aiki da shi, da kuma kokari, jihadi, tsoron Allah da dai sauransu, wannan jika na Manzon Allah (s.a.w.a), wato Imam Sadik (a.s) ya bar wannan duniya a watan Shawwal shekara ta 148 hijiriyya a garin Madina, sakamakon guban da aka sa masa. An bisne shi ne a
Makabartar Baki'a tare da mahaifinsa, kakansa, kakarsa, Fatima al-Zahra (a.s) da baffansa Imam Hasan bn Ali (a.s).
Imam Sadik (a.s) ya koma ga Mahaliccinsa ne alhali ba a ga komai tattare da shi ba in ban da: malami mai gudun duniya, mai kare gaskiya da adalci, mai kira zuwa ga Allah Madaukakin Sarki, mai aikata aikin alheri da kuma shiryar da mutane zuwa gare shi, mai hana sharri da jan kunne
zuwa gare shi, mai neman gafara daga Ubangiji Madaukakin Sarki, mai hakuri kan dukkan wahalhalu da zaluncin da suka same shi, mai haskaka wa al'umma hanyar sa'adar duniya da lahira, mai daga tutar kare shari'a ga al'ummomi masu zuwa da kuma fada da dukkan kauce wa hanya, bidi'a da kuma son rai.
Amincin Allah Ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi, ranar da ya yi shahada da kuma ranar da za a tashe shi yana raye.
____________
|
|