Zamanin Imam Sadik (a.s) dai ya bambanta da sauran zamunna saboda shi zamani ne na ci gaban ilmi da wayewa tsakanin wayewa da tunanin ma'abuta addinin Musulunci a bangare guda, da kuma wayewa irin ta sauran al'ummomi da kabilu daban-daban a bangare guda.
A wancan zamanin dai duniyar musulmi ta ga wani yunkuri na yada ilmi da wayewa tsakanin al'umma da suka hada da ilmummuka irin na addini, kimiyya, lissafi da dai sauran ilmummuka. Kamar yadda kuma an samar da yanayi mai kyau na fassara
ilmummuka daban-daban da suke cikin harsuna daban-daban zuwa ga harshen larabci. Daga cikin irin ilmummukan da aka fassara din kuwa sun hada da ilmin mandiku da falsafa, lamarin da ya haifar da gagarumin canji na ilmi a tsakankanin al'umma.
Kamar yadda kuma a lokacin an samu bayyanar wasu akidoji da yunkure-yunkure na akida da suke kalubalan-tar akida da matsayar Musulunci kan abubuwa da dama, to sai dai kuma saboda irin wannan yaduwa na ilmi da aka samu, ya sa an samu nasarar
gamawa da irin wadannan kungiyoyi da kuma cin galaba a kansu.
A bangare guda kuma, bisa ga irin wannan ci gaba na ilmi da aka samu ya haifar da faruwar wasu abubuwa daban-daban a bangarorin siyasa, tattalin arziki da zamantakewar al'umma, wanda hakan ya janyo aka samu bukatuwa da sanin matsayar shari'a kan wadannan batutuwa. Wannan dai shi
ne ya janyo bayyanar mazhabobi na fikihu da yunkure-yunkure na ijtihadi (fitar da hukumce-hukumce da masdarorin shari'a).
____________