Imam Sadik (a.s) dai bai kasance mujtahidi ko kuma wani mutum mai ra'ayi na fikihu ba, face dai shi mai ci gaba da isar da sako kana kuma magajin ilmin Ahlulbaiti (a.s). Makarantarsa ta kasance tafarkin ci gaban sunnar Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma bayyanar da abin da Alkur'ani mai girma ya kunsa.
Duk dai wanda ya sanya ido kan tafarkin Imam Sadik (a.s) da kuma ayyukansa na ilmi, zai fahimci cewa akwai wasu manufofi da yake son cimmawa, da suka hada da:
Na Farko - Kare Akida:
A wancan lokacin an samu kafuwan wasu kungiyoyi na akida, falsafa da dai sauransu da suka kauce wa hanya, irinsu zindikawa, 'yan gullat da sauran akidu da suka saba wa akidar tauhidi.
A wancan lokacin Imam Sadik (a.s) ya yi hobbasa wajen kare hakikanin akida ta tauhidi da kuma fuskantar wadannan batattun akidu, kamar yadda kuma ya tsaya tsayin daka wajen fuskantar 'yan gullatu wadanda suke kokarin buya karkashin inuwar Ahlulbaiti (a.s) da ba su siffar ubangijintaka
don cimma wasu manufofi.
Imam Sadik (a.s) ya barranta daga masu wannan akida ta bata, kamar yadda iyayensa suka barranta daga gare su kafinsa.
Na Biyu - Yada Musulunci:
Wato fadada da'irar fikihu da shari'a bugu da kari kan kiyaye asalinta. Don kuwa babu wani mutum da aka ruwaito hadisi daga gare shi ko kuma wani Imami da aka karbo fikihu da hukumce-hukumce daga gare shi kamar yadda aka karb daga Imam Ja'afar Sadik (a.s).
____________